Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 111 of 227
Ameer ya tako cikin dakin ya iso gurin Daddy ya rumgume ya fashe da kuka, Daddy ma kuka yake ya kasa juyowa kuma ya kasa barin kukan nasa ya fitarda sauti.
“A kowane dare ina bachi da bakincikin rashin haihu, sai dai saboda son kwanciyar hankalin Jamila a wacan lokacin na kan boye abun na barwa raina, daga lokacin da ta gabatar min da kai a matsayin ďa sai na ji kamar ba ni da sauran kunci a duniyar nan, bayan bayyanar gaskiya sai sonka ya karu, a lokacin ba ni da mafitar da ta wuce na mallaka ka ga mahaifiyarka, duk kuwa da irin kaunar da nake maka saboda na san ta fini bukatarka, domin ita dole ce ta saka ta rabuwa da kai, sai dai bana tunanin dole ce ta saka ta kyautar da kai a gareni, domin ban cilasta mata ba, ban kuma san wani ya cilasta mata ba, sai dai ina kallon abin a matsayin kyautar daban zata ba daga Allah, rahma Allah ce yayi min kyautarka, kuma tun daga lokacin da Zahra ta tabbatar min da kai a matsayin ďa, sai bakincikina ya yaye farinciki ya ninku, musamnan da na sake aure na haifi yaya mata, sai an fahimci hikimar Allah na bani kai kyauta da yayi. A yanzu ma ban san manufar sa, wata kila akwai abun da yake shirya mana, sai dai ina jin kamar ba zan iya jure kallonka a wannan halin ba, saboda ina matukar kaunarka, taso da wannan maganar da Zahra ta yi zata haifar min da damuwar da bata da magani”
Ameer ya sake shi ya fadi kasa ya fashe da kuka, gaskiyar da yake son sani ya santa amman ta haifar masa da karin bakinciki, damuwa da kunci suka bude masa sabon shafi, gaba daya komai ya zame masa ka rubutun littafi, wani abun kuma kamar mafarki. A cikin wuni daya duniyarsa ta juye, rayuwarsa ta sauya, mutanen da yake kallo a matsayin iyayen sun tashi daga iyayensa, wadanda be sani ba be taba mafarkin rayuwa da su ba, su ne iyayensa ta ina zai fara? Kiran wasu da suna da iyayensa? Da girmansa?e yasa wannan abun be same shi a lokacin da yake da kurciya ba? Sai yanzu da girmansa? Har ya mike tsaye ya juya ya fice daga dakin Daddy be juyo ba, Stairs ya sauko be kula da wadanda suke falon ba ya fice zuwa gurin motarsa. Ya shiga yayi mata key yayi reverse, kamin ya isa gate masu aikin kula da gate din sun bude masa. Sai da ya hau titi tunanin ina zai je ya zo masa? Wa zai fuskanta ya fadawa damuwarsa? Damuwace da ba a magani balle a magance masa this is reality. Tafiya mai nisa yayi sannan ya isa unguwar su Humaira, domin zuciyarsa bata raya masa ya je ko'ina ba sai can. Yana shiga unguwar ana kiran sallah Isha'i immediately yayi parking daidai inda Masallacin yake ya fito rike da ruwa ya wanke fuskarsa ya kuskure bakinsa sannan ya rufe motar ya nufi Mallasacin. Second time kenan da yayi sallah a cikin jam'i kafadarsa na taba ta wasu mutanen da be san inda suka fito ba. After gama Sallah ya sake daga hannunsa sai kuma ya rasa addu'ar da zai yi. Sai mikewa yayi tsaye ya fito daga Masallacin ya dawo ta saitin inda gidansu Humairah yake ya tsaya yana ta kallon corner.
Ya dade a haka sannan ya samu wanda ya aika ya fada masa sunanta kuma yayi masa kwatancen gidansu da taba shiga da shi, matashin saurayin ya ce ya gane ta. Takowa yayi ya dawo gurin motarsa ya jingina. Almost 30min sannan ya hango Humaira ta fito, kallonta yake har ta iso inda yake, hakan nan kawai ya ji kamar ya rumgume ta domin yana a cikin damuwar da yake bukatar hug, sai dai ya san Humaira bata cikin irin matan da zai yi ma wannan matukar yana son su kwashe lafiya.
“I thought na ce na aje aiki a gurinku? Miye na sallamo min kuma? Da na san kai ne Wallahi da ba zan fito ba”
Ya dauke idonsa daga barin kallonta ya kalli wani gurin dabam tare da rumgume hannayensa.
“Damuwata ta wuce ta kamfani ko wani gurin aiki, Humaira ban san inda zan je ba, na bata da yawa daga abokaina, some of them ma idan ma fada musu kallon marar hankali zasu min, bana ma son su sani, ban san me zan yi ba, na rufe kaina a daki na yi kuka kamar jariri ko na fito waje na yi ta ihu? Ko kuma na je gurin mutanen da ban sani ba, wadanda suka kira kansu a matsayin iyayena na yi fada da su? Or should I just died?”
Kalamsa sun sanya jikinta sanyi, domin a cikin lafazi mai rauni da neman mafita yake maganar. A wani yanayi na tsoron hantararsa da fadansa ta dago wayarta ta haska fuskarsa. Hawayen da ta gani a fuskarsa ya matukar daga mata hankali, domin duk wani abun da zai iya saka Ameer din data sani kuka to ita zai iya ma kasheta wata kila.
“Me ya faru Ameer?”
“I just need someone to talk to kuma na zo nan na ji kamar bana son magana akan damuwar anymore, I'm sorry for bothering you”
“No... No... No please don't, you need me just tell me me ke damunka?”
Ya sauke kai kasa.
“I'm so weak”
Ya juya ta bude masa motar.
“Shiga ka zauna”
Ya taka ya zauna cikin motar sai ta kwantar masa da seat din, ta rufe motar ta zagaya dayan side din ta shiga ta zauna ta bar nata bangaren a bude saboda idon mutane.
“Do you want water?”
Ya girgiza mata kai, sai ta kalli ruwan dake cikin motar.
“I'm sorry akwai ma ruwa a motar, to zaka ci wani abu?”
Ya girgirza mata kai.
“Ko kana son wani abu? Kana son zuwa wani gurin? Ko kana son shan magani?”
Murmushi ne ya zo masa a lokacin da be yi zato ba, domin ya fahimci so take ta dauke masa damuwa kuma bata san ta inda zata fara ba. Ya juyo yana kallonta sai ta wayarsa ta yi ringing, ya dago wayar yana dubawa sai number Ummi ya gani be hadace number ba amman ya fahimci number ta ne tun a lokacin da ya saka number daga wayar Nimra zuwa wayarsa. Rejected call din yayi a take mood dinsa ya canja.
“Na san bama shiri da juna, and ka tsane ni na sani, amman ganinka a cikin halin ya haifar min da damuwa a yanzu, please fada min meke damunka?”
“Humairah how would you feel idan wata uwar ta fito a matsayin mahaifiyarki, ta ce matar da kike kallon a yanzu ba mahaifiyarki ba ce ita ce mahaifiyarki, and mahaifinki da a kullum kike masa addu'a saboda ya rasu sai wani ya fito yace miki yana raye, yana can wata duniyar yana rayuwa da wasu iyalan da ya fi kauna fiye da ke, ke kuma ya barki duk da yasan shi mahaifinki ne be damu ya baki kulawa da kaunar da kike bukata, and abun da ya fi komai ciwo ya ce kyautar da ke yayi, kuma ya san kina raye amman ya ki baki kulawa saboda baya kaunarki, sai daga wasu kike samu kulawa da kauna, kuma saboda ya rusa farincikinki sai ya fito da rana tsaka ya rusa mafarkinki...”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.