Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 68 of 227

Time to time Maleek yake jefar Waira da kallo a sace, yana mamakin me Ummi ta fada mata take ta mata wannan kallon a yau, ya san ta saba da kallon mutane har sai mutum ya sargu, ba ma kamar Ummi sai dai wannan karon kallon da take yi mata ya so yayi yawa ko ma yayi. Suna a wannan halin ne Dr ta dauko labarin rayuwar waje wacce ta sha banban da Nigeria kasancewar gidan jaridar suna tattauna abun da ya shafi Africa ne, yadda ake bin doka da order da kuma yadda komai yake a tsare can take ta ba su labari, can jefi Maleek yake sako bakinsa yana fadar wani abun da ya sani a lokacin da Karatu ya kai shi kasar. Shigowa Abiey ne ya tsinke musu hirar waje da suke, annashuwar dake fuskarsa na farincikin ganin yar'uwarsa kuma macen da yake mata kallon uwa abokiyar shawara wacce ke share kukansa tun a wacan lokaci ya saka Ummi jindadi, domin bata da farinciki a yanzu sai an mijinta Abiey. Tsokanarta ya fara yi yana dariya sosai kamar ba shi ba, har buga kafa yake kasa tsabar nishadin da yake ji a yau. Sai da suka yi rabin hira sannan Juwairiyyya da Yesmin suka sauko suka gaishe shi domin ba su san shigowarsa har sai da Ummi ta kwalawa Namra kira. A bangaren ya cire babbar rigarsa ya aje domin yau ko marmarin part dinsa haya yi tsabar murna da farincikin ganin yar'uwarsa, Ummi ta daga kan Waira da ta yi bachi ta aje a kan kujerar a hankali sannan ta tashi ta dauko masa abincinsa ta jera masa komai a inda yake zaune. Abun ka da ďan'uwa cin abincin da Dr Zainab ta yi a dazun be hanata karawa a yanzu da ďan'uwanta yake cin nasa ba, hira suka sha sosai har kusan sha ďaya na dare Ummi tun tana saka baki ana yi da ita har ta fara jin bachi, sai hamma take tana murza ido.

“Toh Sarkin bachi ya fara kawo ziyara ko? Har yanzu baki daina bachi da wuri ba, na dauka duk kin watsar da ragancin nan ai”

Karaf Abiey yayi tare numfashin yar'uwarsa yana shigarwa matarsa.

“Doctor yadda Zahra take da juriya ko ke zaki iya ba a yanzu, duk fa yawancin aikin gidan nan ita take yi, ko bata ti girkin kowa ba sai ta yi nawa saboda ban son abincin kowa sai na matata da uwata kin kuma sani, ai tana kokari ma, da ke ce da yanzu kin yi bachi, ko kin dauka na manta yadda kike ne?”

Dariya ta saka ta girgiza kai, yadda yake tsokanarta sai ka rantse ita ce kanwa shi ne yaya, ko kuma ka yi zaton yan yaya da kanwa ne ba yaya uwa ďaya ba. Maleek ya tashi ya fice daga falon yana murmushi daman ya san halin Abbansa idan yar'uwarsa na kusa baya raga mata kamar yadda ita ma take masa idan ta tashi ramawa. Ummi bata bar falon ba sai da ta kira Mahmood ganin shiru shiru be dawo ba gashi har dare ya fara lulawa.

“Ga mu a hanya, Jabir ne ya debe mu nesa kin san ya kwana biyu be shigo garin ba, amman dai mun kusa isowa gida”

“Toh Allah ya kawo ku lafiya”

Ya ake wayar kusa da inda Waira take kwance ta dauki babbar rigar da Abiey ya cire tare da jakarsa ta nufi bangarensa, ko minti uku bata yi da shiga ba, ya shigo yana cire agogon hannunsa tare da kiranta da sunan da ya saba kiranta tun kurciya har yanzu da girma ya zo, soyayya bata canja ba balle ya sake mata sunan da har gaban yayansa idan ya kama yana kiranta da shi.

“Hiayatee ya gidan?”

Ya aje komai a muhallinsa sannan ta juyo tana taya shi cire rigar dake jikinsa ta dauko masa bathrobe ya saka, sannan ta shiga ta hada masa ruwan wanka.

“Yau ka yi latti dawowa, na yi zaton zaka dawo da rana ma saboda zuwan Aunty Zainab”

“Na so na dawo, amman aiki ya rike ni Wallahi”

“Ya dai kamata ka huta Abiey, yaranka sun kawo yanzu wani abun za su iya maka shi, by the time ka kawo tsufa hutu ya kamata ka samu, muma iyalinka mu samu time dinka”

“Wani abun dole ne sai ka yi da kanka, ko da na so na cire hannuna abokam kasuwancin ba za su bari ba, amman dai komai lokaci ne”

“Kullum haka kake fada, kuma lokacin tafiya yake yi baya jiran kowa Abiey, lokuta da yawa ina jin son kasancewa da kai amman baka da time sai dare ko kuma da safe kamin ka fita, akwai abubuwan da ya kamata ace kana saka ido akansu a gidan amman rashin zamanka baya bari, nima kuma ba kullum nake son kasancewa da yara ba”

“To zamu duba, abun da Hajiya take so shi za'ayi dole, zamu aje abun da zai aju wanda ya kamata a rage kuma za mu rage, har ma da wanda za a bari In Shaa Allah”

“Toh Allah ya bada iko”

“Ameen Allah ya miki albarka”

Ta yi murmushi ta bude wardrobe ta fara ciro masa pajamas, shi kuma ya shiga bathroom din, kamin ya fito ta feshe su da turare ta dauko masa maganinsa na ciwon kafafuwa da yake sha ta aje masa tare da ruwa. Sai da ya shirya ya sha maganin sannan ta fita ta koma bangarenta ta hado masa coffee, a lokacin babu kowa falon sai Waira dake bachi da kuma Plasma dake kunne. Bangaren mijinta ta dawo ta kawo masa coffee da ya saba sha tun can baya ta mika masa kana ta zauna kusa da shi tana labarta masa labarin Waira. Tunanin namijj ba ďaya da na mace ba, haka zuciya ma ta mace ta fi tausayi da saurin yarda. Hakan ya saka Abiey be yi saurin amincewa da labarin da Ummi ta ba shi ba, ba Ummi yake karyatawa ba, Waira ce lamarinta ya ďan daure masa kai.

“Amman ta ya aka yi kika tabbatar gaskiya ta fada miki?”

“Kasan ba tun yau ba, na sha yi mata magana akan garinsu da abun da ya shafi rayuwarta bata fada min komai, idan ka lura bata da sakewa irin yadda ya kamata, kusan kullum a tsorace take bata da walwala, kuma yanayinta sai ya rika min kamar mai tunanin wani abu, wata kila tana tsoron fadar garinsu ne, kar ace za a maida ita”

“Maida ta kam dole ne”

“Tace kasheta fa za'ayi”

“To ya kike son ayi mata?”

“A barta ta zauna a nan tare da mu kawai, gudun kar mu maida ita mu jefata a matsala”

“Hajjaju ai ko zata zauna tare da mu, dole ne sai mun san inda yan'uwanta suke, dole ne mu san garinta da kuma dalilin da ya saka suke son kasheta, ko kuma kina tunanin haka nan kawai za su kasheta ba tare da wani abun ba,? Ko da tana da gaskiya ya kamata mu ji gaskiyarta, kuma idan har zata yarda ta fada mana garinsu ai ba mu kadai ko kuma ita kadai zata tafi ba sai tare da jami'an tsaro, bayan haka kuma za mu sake kafa shaida a gurin jami'an tsaron saboda su san duk abun da yake faruwa ko da wani abun ya taso”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.