Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 216 of 227

“I thought rumgume ni zaki yi duk matsuwar nan da kika yi na dawo”

“Ba kyau ni ba muharramankar ba ce kuma akwai mutane sosai a nan”

Ya juya ya kalli gurin.

“Kowa sha'aninsa yake indai har da gaske kike yi kin yi missing dina hug me”

“Akwai mutane Ameer”

“I don't care hug me Humairah show me that you miss me”

“Ameer... Ba kyau fa”

“This will be the last one till we get married....!”

Wani dummnn ta ji maganar a kunnenta sai ta ji kamar ba daga bakinsa ta fito ba, tsaye tayi kamar hoto tana kallonsa ko motsi bata yi. Murmushi yayi irin murmushin da ya kara masa kyau ya warware jacket dinsa dake hannunsa ya dora mata saman abayar da ke jikinta ya rumgume ta.

“I miss you so much Humairah i never thought mun sabu haka ba sai a yanzu da na ganki”

Hawaye ya sauko idonta sai ya saketa ya dube ta, ganin hawayen ya saka hannunsa biyu ya share mata hawayen.

“Mu tafi”

Ya fara tafiya ita kuma ta kasa juyowa ta kasa tafiyar ta kasa komai har lokacin, baya baya yayi ya riko hannunta ya juyo da ita.

“Wasa nake miki kar ke ma ki yi breaking heart dina kamar Nuwaira i can see that you don't love me...”

Yana rufe baki sai ya rumgume shi ba tare da ta sani ba ta fashe da kuka. Murmushi yayi ya daga hannayensa ya daga ta jikinsa ya sumbanci goshinta sannan ya rika hannunta suka nufi gurin motar. Kamin ya isa direban ya bude masa baya, sai da ya fara sakata sannan ya shiga driver yaja motar.

“Ina zamu je?”

“Gidan Hajiya”

Ta fada cikin wata murya mai ban tausayi, kallonta yayi yana murmushi sai ya ga shi take kallo hawaye na sauko mata, a hankali ya kai hannunsa ya rika yatsunta ya murza a hankali yana kara yarda da maganar Hajiyar.

“Me kika shirya min?”

Ta kasa cewa komai shi kuma be fasa tambayarta ba har suka isa gidan, ita ta fara fita motar sannan ya fito yana fadin.

“Ya kamata a samu mai gadi, ko dan ku samu mai kula muku da gidan”

Ya fadi hakan ne kasancewar da za su shiga sai da direban ya fita ya bude gate ya shigo da motar, ita dai har lokacin ta kasa cewa komai gaba daya jikinta a mace yake, bata jin sautin komai sai maganar da Ameer yayi mata a airport, domin ya furta mata ita a lokacin da bata yi zato ba, ba ta ma yi tsammanin ya fahimci yaren soyayyarta ba. Wata tambaya ce ta zo mata a rai a lokacin da yake ta hira da Hajiya yana cin abinci, da gaske yana jin wani abu a zuciyarsa gema da ita ko kuma dai saboda zai cika burin Ummi ne? Har ya ci ya sude beta tofa komai a maganarsa da Hajiya ba. Sai da zai tashi ya shiga dakinsa yayi mata alama da abincinta yayi dadi. Bata hakaro ba ta ji shi a kusa da ita yana mata magana.

“Are you okay?”

Wani irin faduwa gabanta yayi kwarjinsa ya cikata bata taba jin wani abu kunyarsa ba sai a lokacin, ta sauke ido kasa tana lekawa ta gani idan Hajiya bata gurin domin sosai ya matse har tana kusan jin numfashinsa.

“Hajiya bata nan”

Bata yarda da sai da ta duba da kanta bata ma san Hajiya ta bar falon ba sai lokacin.

“Zata iya fitowa ta ganmu a haka”

Ya kama hannunta ya rike yana murzawa a hankali.

“Humairah ina da banbanci da mutane yawanci abun da yake saka wasu kunya ko tsoron ni baya saka ni, nan ai gidanmu ne, dan anganmu a haka miye a ciki?”

Murmushi yayi mai sauti ya ce.

“Zaki iya tuna lokacin da kika fada min cewar idan na taba ki ko na rumgume ki sai ki min fadan hauka kin nuna min ke ba yar iska ba ce”

Ta fisge hannunta da sauri, sai kawai ya rumgume ta yana dariya sosai kamar ba shi ba.

“Go ahead idan na sake ki yanzu ki mare ni”

Ya fada sannan ya sake ta, abun mamaki duk masifarta sai ta daga ido ma ta kalleshi balle ta yi yunkurin aikata abun da ta furta.

“Ashe ni da ke duk marasa jin magana ne”

Ta kasa cewa komai har lokacin, da murmushi ya zagaye ya shige dakinsa kiran Daddy na shigowa wayarsa, sai da ya shige sannan ta juyo ya kalli bayansa tana murmushi ta kai hannunta ta dafe zuciyarta ta nufi dakinta da gudu tana shiga ta maida kofar ta rufe ta fada kan gadonta ta lumashe ido...

Daga lokacin ne wata sabuwar alaka da shakuwa ta fara shiga tsakanin Humaira da Ameer, ita dai daman kaunar Ameer ta dade ginuwa a zuciyarta, a yanzu kuma sai ta tarairayi barta tana gina masa kaunarta a zuciyarsa. A month later suka shirya har Hajiya da Bahijja suka tafi Kano gurin dangin mahaifin Deen da kuma Hajiya daman ta labarta musu komai a waya, tun a lokacin da abubuwan suka faru, su suka sauka a family house dinsu shi kuma ya sauka gidan Ammynsa wato Hajiya Jamila ba karamin murna ta yi ba ganin Ameer domin Allah ya saka mata kaunarsa ba kadan ba, satinsa biyu a sokoto babu inda be zaga ba gurin yan'uwa da suke kusa kowa mamakin ganinsa suke a nan ma sai da aka samu masu zagin Ummi akan abun da ta aikata, wasu kuma suka ce gobarar titi a jos, domin a familynsu babu mai rufin asiri da arziki da Ameer yake da shi a yanzu wadda har Hajiya da Bahijja suka samu, suna ganin da ace Ummi bata aikata hakan ba da yanzu babu wannan shataletalen arzikin, daman fahimtar kowa dabam wasu na ganin bata kyauta ba, kuma ta dauki alkali wasu kuma na ganin bata yi laifi ba domin bata bar shi a wahala ba. Har gurin dangin mahaifin Humairah sai da Ameer ya je ya gaishesu a matsayin dan'uwanta kuma mai kudirin aurenta, kusan duk inda ya tafi sai ya karar da aljihunsa domin dangin nasa ba wasu masu arziki ba ne, su ma nema suke yi, a nan ya gane Ummi ba karamin taimakon ta yi masa ba na bada shi gurin Mr Bashir ko da be tashi cikin wahala a gurin dangin Deen ba, saboda tana raye ya san ba zai samu kalar gatan da ya samu a yanzu ba, domin Abiey ba zai rike shi ya sakar masa dukiyarsa kamar yadda Mr Bashir yayi ba, ya saka tufafin da yake so idan zai yi tafiya a gari ma sai dai idan ya isa garin ya siye wasu tufafin amman baya tafiya da kaya duk inda zai ji saboda yana jin sun zame masa aiki, idan zai dawo ma ba zai dauko su ba, motar sai wadda ya ga dama yake shiga tsabar gatan da Mr Bashir yayi masa shi taba sanin akwai talauci mai tsanani ba sai da ya hadu da Humairah a yanzu kuma zuwansu gurin dangin mahaifinsa ya fahimci komai. Ta waya Ummi ta hada shi da Yayarta Maryam dake shirin barin kano zuwa duba Ummi, ba karamin sanyi da dadi ya ji ganinta domin tana kama da Ummi sosai ta hada shi da duka yayanta da suka manyata har da iyalansu suka yi exchanging number junan, bata yarda ya bar gidan ba sai da yayi kwana biyu, nasiha sosai ta yi masa ta labarta masa irin soyayyar da Zahra ta yi da Deen kamin rai yayi halinsa, ya nan ya fahimci ita ta bada gudumawa gurin samun lafiyar mahaifinsa a lokacin da ba a haife shi ba, domin ta siyar da kayan dakinta kuma ta yardar a siyar da gidansu na gado a hada da kasonta a nema masa lafiya. Sosai suka yi hira ya saki jikinsa yana jinta kamar Ummi, domin ta yi masa maraba yayanta ma sun nuna masa kauna haka ma Mijinta. A nan ita ma ta kai shi gurin wasu dangin mahaifinsu da kuma na Mahaifiya ya gaisa da mutane da yawa kowa sai mamaki yake idan ya ji cewar dan Zahra ne.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.