Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 199 of 227
“Are you okay?”
“I don't know ina jin dai kamar ba ni da lafiya”
“Akan Waira ne?”
Yayi kamar be jita ba ya cigaba da tafiyarsa har ya shiga cikin falon, sai da ya zauna sannan ya gaishesu. Hajiya da kanwar mahaifinsa suka amsa suna karantar yanayinsa da ya canja.
“Allah yasa ba Ummi ce ta bato maka rai ba kuma Ameer”
Ya dago ya kalli Hajiya cikin yanayin damuwa.
“Hajiya idan kina son na so ki kuma na kaunace ki na girmamaki ki daina maganar Ummi marar dadi a gabana, duk wani abun da ta yi min ko zata yi min ita din uwata ce babu wanda ya isa ya canja wannan, kuma wannan damuwar tawa ba akanta ba ne akanta ba ne akan yarinyar da nake so ne”
Humairah ta zauna tana kallonsa.
“Wani abun ya same ta?”
“Ina fatar dai tana cikin aminci, domin Maleek ya bita sun shiga garin kuma police din sun ce mutanen sun fara dauka da zafi tun kamin su shiga da ita ma, ina ta kiran wayarsa kiran be shiga ba Abiey ma ya kira wayar bata shiga, and jiki na bani wani iri like kamar ba kalau ba akwai dai abun da yake faruwa”
“Da alama dai kana son yarinyar sosai Ameer”
Ameer ya kalli Bahijja ya daga mata kai yana kiranta da sunan da Humairah take kiranta.
“Sosai Mama ina son fiye da tunanin duk wani mai tunani”
“Allah ya zaba maka abun da ya fi zama alheri”
“Ameen thank you”
Ya kalli Humairah
“Ina list din?”
“Ko mu bari sai next time na ga kamar baka cikin yanayi mai dadi”
Sai ya mike tsaye ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi mai kauri ya duka gaban Hajiya ya aje mata.
“Ga wannan ko da zaku yi hidimar gida, zamu je da Humairah mu siyo wasu abubuwa sauran kuma ina tunanin sai dai na bada kudi a siyo dabam”
Hajiya ta mika hannu ta dauki kudin tana dubawa, farincikin ganin kudin ya kawar da damuwar maganar da ya fada mata akan Ummi a take ta washe da kau har ta fara hade fuska, ganin kamar baya son ana ganin laifin Ummi bayan kuma ita din a gurinsu babbar mai laifi ce.
“Ameer wannan duk hidimar gida? Maa Shaa Allah, Allah dai ya saka maka da alheri, ina ma ace mahaifinka yana raye ya ga wannan hidimar ace dansa ne yayi, Allah dai yayi masa rahma”
Ta karasa tana fashewa da kuka domin har ga Allah tana jin kewar danta, abubuwa da yawa tana yawan fata ina ma yana raye yayi mata, yau gashi kuma daga jininsa anyi mata amman bashi a raye balle ya gani. Maganar mahaifinsa da ta yi da kuma kukan ya saka Ameer kara shiga damuwa, sai ya ji abun ya ninka masa. Ajiyar zuciya kawai ya sauke ya fice daga falon. A mota Humairah ta same shi bayan ta saka hijabinta ta dauko takardar da suka yi list din. Be ce mata komai ba ya fara tuka motar, ita ma bata ce masa komai ba, kuma ta yi iya kokarinta ta dauke idonta daga gareshi har suka isa super market din. Ya faka ya ciro wayarsa yana gwada dialing number Maleek yana fadin
“Me zamu fara siya?”
A lokacin da ya kira wayar Maleek kiran ya shiga sai ya ji wani irin sanyi a ransa, har wani gyara zama yake yana kallon Humaira murmushi na bayyana a fuskarsa.
“Wayar Maleek ta shiga”
“Allah yasa ya daga”
Humairah ta masa addu'ar tana masa fatan samun jin muryar Waira domin bata son ganin damuwa a tare da shi, hakan ya saka take masa fatan samun Waira a yanzu domin ta gama fahimta yana sonta sosai. Rashin amsa kiran da Maleek yayi ya sake daga masa hankali hakan ya saka yayi ta kiran wayar ba adadi har da fita motar yayi yana yawo kamar wani tababben, a yanzu hankalinsa ya fi tashi fiye da farko da be san halin da take ciki. Da sauri ya dawo cikin motar yaja motar da sauri kai kace shi kadai ne a hanya haka ya rika tuki ba tare da ya fadawa Humairah inda za su je ba, ita ma tsoron yadda yake tukin ya hanata tambaya domin tuki yake bana arziki ba. Sai da ta ga sun fara ratso unguwarsu Ummi sannan hankalinta ya kwanta.
“Gurin Ummi zamu tafi?”
Ya kalleta a firgice domin ya manta ma tana cikin motar.
“Oh my God kina nan still”
Bata sake cewa komai ba har ya faka harabar gidan, yana bude mota ya fito Mahmood ma ya bude tasa ya fito.
“Ina Abiey?”
“Yana falom Ummi”
Mahmood ya amsa masa yana kallon Humairah da ta fito a front seat din. Ameer ya nufi kofar falon Ummi da gudunsa, Humairah ta rufa masa baya tana tafiya a hankali ganin Mahmood na kallonta ya saka ta gabata masa da kanta.
“I'm Humairah ni Cousin dinsa ce ta bangaren mahaifinsa”
“Oh... Oh.. O... Nice Sannu Humairah”
Ya fada yana jin kamar ya santa, ita da shi a tare suka shiga falon, sai suka samu Ameer a zaune yana kallon Ummi dake kuka. Ameer ma be san dalilin kukanta ba and he don't want to ask shiyasa ya samu guri ya zauna kamar yan'uwansa Namra da Mahmood sai kuma Abiey dake zaune kujera daya da ita.
“I'm sure Maleek yana lafiya Ummi dan Allah ki kwantar da hankalinki”
Namra na fadar haka ya fahimci saboda Maleek ne hankalin Ummi ya tashi. Abiey ya ce.
“Na yi magana da police din yau za su kuma sun tabbatar min ba za su dawo ba sai da ďana”
“Na kira shi yanzu wayar ta shiga yana ringing amman be daga ba”
Ameer na fada hakan Abiey ya dauko wayarsa da sauri ya gwada kiran Maleek and suka yi sa'a yayi picking sai Abiey ya saka a speaker saboda hankalin Ummi ya kwanta. Kamar wanda aka daga sama aka buga da kasa aka mikar tsaye haka Ameer ya ji bayan ya gama sauraren wayar Maleek da Abiey, kasa cewa komai yayi ya mike tsaye yana hade wani abu mai daci a makoshinsa ya nufi kofar fita, duk binsa suka yi da kallo har ya fice. Ummi ta share hawayenta ta kalli Abiey ta ce.
“Me yasa Maleek zai fadi magana irin wannan a gaban Ameer?”
“Be fada dan ya san Ameer yana nan ba, please don't blame him bari dai ya zo mu ji whole story”
Abiey ya fada a kokarinsa na kare dansa. Humairah ta mike tsaye
“Bari na duba shi”
Ta fice daga falon daman jin take kamar tana kan kaya, tana fita ta ga babu Ameer babu alamarsa. Sai ta juyo ya dawo cikin falon ta tsaya daga bakin kofa
“ban ganshi ba ina ganin ya tafi”
“Zo ki zauna zan kira shi ya zo ya dauke ki”
Ba musu ta dawo ta zauna kamar yadda Ummi ta bukata, Ummi ta dauki wayarta ta yi ta kiran wayar Ameer be daga ba.
“Maybe yayi fushi, ki jira zuwa anjima na san zai dawo ko dan ya duba Nuwaira”
Bata son musawa Ummi haka ya saka ta amsa ta toh. Ta zauna a falon ta maida hankalinta gurin tv dake kunne Namra kuma ta tashi ta rika Ummi suka nufi Upstairs Abiey ma ya fice daga falon zuwa bangarensa aka barta ita kadai sai Mahmood dake zaune yana buga game da wayarsa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.