Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 162 of 227
“Me yasa kika fadawa Ameer za a kaiki wani gurin karatu? Idan ina bukatar ya sani ni zan fada masa ba ke ba”
Waira dake zaune kasa ta dago ta kalli Ummi tana jan numfashi kamar zata shide.
“Shi ya tambaya me yasa nake kuka? Ummi bana son na bar gidan nan please”
“Ya zama dole kuma, domin Ameer da Maleek fada suke a kanki, ni kuma hadin kan yayana nake bukata ba watsewarsu ba, saboda ke yau Maleek yayi ma Ameer gori, saboda ke Ameer ya fadi maganar da bata dace ba akan Abiey, saboda ke Waira hadin kan yaya zai tarwatse, fada suke akanki”
“Saboda me?”
Ummi ta kasa bata amsa sai ma mikewa da ta yi tsaye ta nufi gurin da take aje uniform ta dauko mata.
“Tashi ki saka uniform kin yi wanka?”
“Eh na yi wanka”
“Okay ki saka uniform dinki lunch box dinki yana dinning zan yi ma driver magana ya kai”
“Ameer fa?”
“Ya fita daga rayuwarki daga yanzu, ki manta da shafin rayuwarsa, ki goge shi a zuciyarki”
Waira kallon rashin fahimta kawai take yi ma Ummi har ta fice daga dakin. Da tunanin Waira ta saka uniform din bata damu da yadda fuskarta take da jurwayen hawaye ba ta sauko ta dauki lunch box dinta.
“Waira zaki iya gane garinku?”
Ta juyo da sauri ta kalli Ummi dake saukowa.
“Aa ba zan iya ganewa ba, a ka'ida sarki yace idan na gudu ba zan iya gane hanyar gida?”
Ummi ta zauna a one of dinning chairs tana kallonta.
“Me yasa kika gudu?”
Waira ta sauke kanta kasa wasu hawayen na cika ramen idonta, bata tunanin ta taba fada musu dalilinta na guduwa idan na ta fadawa wani a cikinsu Ameer ko Jabir da ta sakewa da yawa.
“Wani aka kashe aka ce ni na kasheshi kuma ban aikata ba, kuma idan na kai wasu shekaru za a bani sarautar tsafin garin ni kuma bana so saboda zasu kashe ni ne idan na mutu”
Ta aje lunch box din ta bude hannun uniform dinta ta nunawa Ummi wani tabo dake hannunta.
“Gadon mu ne, idan an haihu ake mutuwa, a cikin wannan tabon ina ganin abun da ya faru da mutum a baya, ina iya kashe wani idan ina so, ta ciki na iya gane ciwonki da damuwar da kike boyewa ta Ameer, tun kamin ki fada, ta ciki dazun na ga abun da Abiey yayi magana da ke, da zarar na rumgume mutum zan iya ganin komai ko na san komai”
Ummi ta mike tsaye tana kallon Waira da mugun mamaki.
“Kina tsafi kenan? Ban taba yi ba, sun ce sai na girma zan iya saffara komai yadda nake so, a garin mu kowa matsafi ne sai dai wani ya fi wani karfin tsafi, wanda ba dan garin ba baya shiga, rayuwarmu da ta ku akwai banbanci addininmu dabam da na ku, a yanzu na saba da nan dan Allah karki ce zaki maida ni gida Ummi”
Ummi taja dogon numfashi ta sauke tana
“Ya sunan garinku?”
“Garuk... A lokacin da na gudu daga garinmu na boya a gurin duwatsu a nan na fara haduwa da Ameer”
“Okay ki je waje na yi magana da direba zai sauke ki school”
Waira ta durkusa kasa ta kama kafar Ummi.
“Ba tsafi na yi ma yayanki suke so na ba, ni ma ina sonsu duka, ina kaunarsu dan Allah kar hakan ya saka ki maida ni Garinmu ko ki koreni daga gidanki, kashe ni zasu yi, na san za su bibiyeni a duk lokacin da suka tashi kasheni, amman for now ina son zama da ku please, tsafina ba zai muku komai ba, ba zan cutar da ku ba, idan kuma baki yarda ba, toh ki kira min Sulem zan zauna a gurinsa”
“Tashi Waira tafi direba na jiranki karki yi latti”
Ta mike tsaye ta share hawayenta ta gyara hannun rigarta ta dauki lunch box dinta ta fice daga falon still tana hawaye. Tana fitowa Maleek ne farkon wanda ta fara cin karo da shi, tsaye a balcony din kamar mai jiranta bata yarda ta kalleshi ba, ta fara sauko a staircase din dake gurin shi kuma ya bita da kallo kamar zai kamota ya cinye. Ta isa gurin motar da direba ya saka ma key ya bude gidan baya yana jiran isowar Waira. Ta shiga gidan baya ta rufe motar, sai ga Maleek ya iso yayi ma direban alama da ya fito daga cikin motar ba musu ya fito Maleek ya shiga yaja motar aka bude musu gate. Suna kama hanya ta gyara madubin gaban motar ta saita fuskar Waira, ita kuma ta ki dagowa sai kuka ke cinta.
“Waira.. Idan baki ra'ayi ba za a kai ki ko'ina gurin karatu ba, zaki zauna a tare da mu”
Ta dago ta kalleshi ta cikin madubin yadda idonta ya kumbura yayi ja abun har tsoro ya bashi.
“Ya Maleek can you do me a favor?”
“Uhm-Hmm”
“Dan Allah ka daina fada da Ameer, shi ma zan masa magana, Ummi ta fada min a yanzu kun yi fada saboda ni, kuma ita tana ganin kamar laifina ne, har na fada mata abun da be kamata ta ji ba, kuma na ga tsoronta da fargabar zama da ni a cikin idonta, ta fara tambaya ina ne garinmu, tace zamana a gidanta ba zai yiyu ba, Ya Maleek bana son komawa garinmu kashe ni za su yi....”
Ta shimfida masa irin labarin da ta fada ma Ummi, kuma ta nuna masa hannunta sai hawaye take kamar ba gobe. Tsayar da motar yayi ya faka gefen titi ya dauki tissue ta bude motar ta fito ya zagaya back seat ya bude ya shiga ya zauna ita dai sai kallonsa take. Cikin tausayinta ta kai hannunsa dake rike da tissue ya fara goge mata hawayenta.
“Dan Allah ku daina fada da juna, Ummi bata jindadi kuma ni abun zai shafa, ni burina kowa ya so ni na zauna da kowa lafiya, amman ba irin son da zai saka ku fada da juna ba, a yadda na saba da rayuwa a nan ko na koma can ba za su karbe ni ba, kuma zamana a nan ba zai saka su kyale ni ba”
“Babu inda za a kaiki, mune familynki a yanzu, I'm sorry zamu gyara ni da Ameer ba zamu sake fada ba, Ummi kuma ba zata sake miki maganar garinku ba ki daina kuka”
Ta daga masa kai sannan ta mika hannu ta karbi tissue din ta kwanta jikin kujera, shi kuma ya bude motar ya fita zuciyarsa na sosuwa da hawayen da ya gani a idon Waira, ba taba jin damuwa da matsalarta irin yau ba. Kuma bata taba bashi tausayi irin yau ba. Har ya isa makarantar kallon fuskarta yake a madubi kamar zai yago naman fuskar ya cinye, damuwarta ta haifar masa da damuwa fiye wanda ya taba kasancewa a baya. Yana fakawa bakin gate din makarantar ta bude motar ta fita ba tare data sake kallonsa ba tun bayan da ta gama magana da shi a dazun, kasa tafiya yayi sai kallonta yake har ta shige cikin school ya daina hangota sannan ya sauke ajiyar zuciya.
Kusan a takure ta wuni a makarantar duk wani darasi da ya kamata ta maida hankali ta rubuta ko ta fahimta sai ta kasa yin ko daya, gaba daya rayuwarta ta baya sai ta dawo mata, sai tunanin yadda ta rasa abubuwa take, farko garinsu da Eid, daga baya Shuraim ta sabu da Nimra ta rasata ta sabu da Ummi da Ameer gashi shakuwa na shiga tsakaninta da Maleek a yanzu, sai kuma ace Ummi ta maida ita garinsu? Garin da suke neman kasheta? Idan kuma ta cigaba da zama a gidan ta san zata cigaba da haifarwa da Ummi damuwa, bayan kuma bata cancanci haka daga gareta ba bayan duk abubuwan da ta yi mata na kyautatawa, kana a yanzu ta san Ummi ba zata aminta da ita ta zauna da ita kamar da ba, bayan ta gama bude mata sirrinta. A lokacin da aka kada karaurauwar break kowa ya fita gurin cin abincinsa masu kudi suka nufi gurin siyen abun da za su saka a cikinsu ita kuma sai ta kebe kanta can bayan karshen kujerar dake class dinsu ta zauna a gurin tana ta kuka, ta kasa fita daga ajin ma balle har ta ci wani abu, gashu bata ci komai da suka fito daga gida. Haka dai ta wuni cikin kuka da tunani da takura har aka tashi, ta yi zaman da yayi awa daya sannan direba ya zo daukarta ta shiga motar cikin wani irin yanayi na damuwa da bak'inciki, a can idan aka tashi daga makaranta tana daukin zuwa gida saboda tana jin kamar karatun da yan makarantar takura ne a gurinta a yau kuma sai ta samu kanta ta fargaba da tsoron komawa gida. Direban na fakawa ta bude ta fita ta tura kofar falon ta shiga, babu kowa a falon sai Ummi Hanne na zaune kasa tana matsa mata kafafuwanta. Ummi ta lura da damuwar sa Waira take ciki domin ta ga hakan a idonta da fuskarta, hancinta har yayi ja tsabar kukan da ta sha a yau. Dinning ta nufa ta aje lunch box dinta ta nufi stairs ba tare da ta yi ma Ummi abun da ta saba ba, wato hug da murnar dawowa daga makaranta. Ummi ta bita da ido har ta haye sama, sannan ta dauke kafafuwanta ta mike tsaye lunch box din ta nufa ta bude sai ta tararda abinci a yadda ta zuba mata shi. Ummi bata jidadin ganin Waira bata ci komai ba domin ta san kamin ta fita ban da kuka bata karya da komai ba, dan haka ta yi hanzarin nufar kitchen ta dauko cake din dake cikin fridge ta saka a oven ta dumama mata ta hada mata tea mai kauri ta dauki plate ta bude gurin da take ajiyar biscuits da chocolate ta zuba mata ta dauko dayan plate din ta zuba mata shimkafa da miyar da aka girka domin ta san zuwan Ameer tana kan gwada cin abincin da suke ci saboda ya koya mata, sai dai ba kasafai take ci ba. Karamin bowl ta dauko ta saka mata boiling eggs uku ta dauko babban tray ta jera komai a kai, sannan ta dauko ruwa ta dora sama ta dauki tray da kanta ta fito daga kitchen din, Hanne na ganinta ta yi saurin ta shi zata rika mata.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.