Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 227 of 227

Shi dai be ce komai ba saboda Ummi take kusa.

“Ka cire mata shi Maleek yanzu nan?”

“Toh Ummi abun cirewa yana mota ai ta zo muje a cire”

“Ummi wayo yake miki Allah kuwa”

Ta fada a shagwabe kamin ta dago ta kalli gurin da Kanenen Ameer suke zaune wato yayayun Fiyya da aka yi aurensu a tare ta daga musu hannu, suma suka dago mata.

“Ba wasa nake ba key din yana mota”

“Bishi ku tafi ya dauko ya cire miki, haka kawai zai takurawa yata a cikin mutane”

“Ni ma ai shi na gani”

Nuwaira ta fada, Maleek ya girgiza kai yana murmushi ya ja suka fita daga gurin, yana tafe tana masa mita har suka isa gurin motar, jinginar da ita yayi jikin motar ya fara mata chakulkuli a wuya.

“Ni zaki yi kara gurin Ummi”

Ta saka dariya da kuka a lokaci daya.

“Give me a kiss”

Ta mika masa bakinta ya sumbanta sannan ya bude mata motar ta shiga ya zagaya ya shiga dayan side din ya rufe ya saka motar a lock.

“Kin ga yanzu sai mu zauna ni da ke a nan har a gama, idan kika gaji sai mu tafi gida”

Sai kawai ta fashe masa da kuka, dariya yayi ya kwanto dakanta jikinsa inda rigimarta ce ya saba da ita, tun da suka yi aure ta zame masa kamar wata yarinyar goye, indai tana kusa da shi shagwaba babu kalar wadda bata masa, rigima ma babu kalar wadda be sani ba tata, har ta kai yanzu idan be ga ta masa ba baya jin dadi. Fir Maleek ya murje ido ya hanata fita motar har aka tashi bikin, aikuwa suna komawa gida ta ce babu shi babu zaman lafiya, abinci ma sai yayi da gaske sannan ta ci ta kwanta kuma ba dan bata jin yunwa ba sai dan ta wahalar da shi. Tun da ta samu cikin ba zama lafiya kullum da kalar fitinar da take masa, daman can da take ita kadai ta yi masa haka balle kuma yanzu da ta suka zama su biyu. Haka dai yayi ta juriya tana biyewa hallayarta har Allah ya sa ta sauka. Ranar da ta haihu kamar ya hadeta murna kamar ya zuba ruwa kasa ya sha, ita kuma rarrashinta yake ta yi kamar ya lashe. Ranar sunan Baby ta ci sunan Ummi aka saka mata sunan Ummi wato Fadimatul Zahra, aka yi mata alkunya da Teema, duk wanda ya kalli yarinyar ya san yar Nuwaira domin fuskarta ta dauko gaba daya kadan ta tsakuro a fuskar Maleek. Idan aka yi magana sai Maleek yace saboda tana mace ne idan suka sake haihuwa shi zata biyo.

*** *** *** *** *** ***

Rayuwa ta zamewa Ummi a yadda kowa be zata ba, girma ya kama ita da Abiey jikoki sai kewayesu suke iyalai ta ko'ina sai hamdala. Abubuwa da yawa sun zowa iyalin ta inda ba su zata ba, a. Rayuwata koma cikin jindadi da farinciki, idan wannan ya sauke wannan ya dauka ranar da aka so week gida ko aka yi hutu Ummi bata da zaman lafiya saboda yawan magana da bari bari, hakan ya saka kullum gidanta baya rabo da sweet da kayan kwalama. Domin bayan Abiey yanzu tana da wasu mazajen kuma sojiji ciki har da masu sunan Abiey da ake kira da Aliyu Haydar wato dan Namra yarta ta biyu kuma ana kiranta da Little Nimra. Rayuwa cike take da kalubale wani lokacin dadi wani lokacin wahala, wani lokacin kuma a hada maka duka, wani sa'in kuma sai wahalar ta wuce dadi ya zo wani dadin kuma baya zuwa sai bayan wahala. So many blessings sun sauka ga iyalan wadda ya wanke duk wani kalubale da kunci da aka shiga, komai ya zama labari sai idan ya tuna.

Alhamdulillah Thumma Alhamdulillah

Yabo da godiya su tabbata ga Allah tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Annabi Muhammad Rasulullahi Sallalahu Alaihi Wassalam. Alhamdulillah na gode Allah da ya bani ikon rubuta wannan labarin ina addu'ar Allah ya sa mu amfana da shi.

Kuma ina son na yi amfani da wannan damar na bawa wadanda na batawa rai akan rashin sani, kuskuren ko ganganci, a gafarce ni a yafe min 🥺🙏

Haka kuma ina sanar da wadanda suka karanta ba su biya ba, cewa ba free ba ne domin sauki nauyin hakkin karatu pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank.

Littafin sadaukarwa ce ga Asma'u Badamasi (Asmee yar gagara) Safiyya Dan jumma (Ummul Falsak mai kan kwakwa) Salma Gidado (Salwees ƴar yarinya) Allah ya shiryaku.

Godiya ga duk wadanda suka siya littafin nan suka karanta shi ta hanyar halak, Allah ya bar kauna duka Fan's dina ina gaisheku a duk inda kuke, sai mun hadu a littafina na gaba mai suna HURIYYA labari mai ban tausayi da taba zuba, kuma mai dauke da rikita rikita.

Best Regards 🥰🙌
Khadeeja Candy ❤
080361266660

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.