Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 53 of 227
“Yarinyar nan bata son na daga da zarar na motsa sai ta tashi ta rike min hannu, wata kila tsoro take ji har yanzu ko kuma tana kewar mahaifiyarta ne”
“Ummi sai ki biye mata, ki zauna tare da ita har tsawon wannan lokacin”
Ta sakw fada yayin da ta karasa kusa da ita ta duka. Sai Ummi ta kai hannu ta shafa fuskar Nimra.
“Zan tashi, nima na jidadin zaman ne, ina ta jin kewarku kuma lokacin da kuke da kurciya kamar ita haka kuke yawan rabar jikina”
“Har yanzu ma ai ba mu daina ba, kuma ba za mu taba girma da hakan ba”
Ummi ta yi murmushi sannan ta cire hannun Waira a hankali ta aje kasa ta mike tsaye, da sanda suka fice daga dakin ita da Nimra saboda kar ta farka. A bakin kofar dakin Nimra ta fara yi Ummi tambayoyi.
“Ummi an bincike motar kuwa?”
“Ina tunanin police din sun yi bincike ai, ba su koma ba ma sai gobe za su kama hanya tun da sassafe”
“Kuma ba su ga komai a motar ba?”
“Da sun gani da sun fada ai, mi yasa kika tambaya?”
Ta dan hade yawu tana tunanin irin amsar da zata bawa Ummi.
“Akwai a motar wanda na siya few days before abun ya faru kuma akwai ATM dina da waya a motar ina tunanin ko Ameer ya bar su a ciki”
“Sarewa kuma? Ki yi me da sarewa ke ba namiji ba? Zan tambaya Abieyun ku na ji idan akwai a motar”
“Idan kuma babu Ummi ki karba min key din na duba da kaina”
“Okay”
Ya juya ta nufi hanyar dakinta, Ummi ta bita da ido tana karantarta, domin ta ninka a kiriniya lokacin da take da kurciya, tunanin Ummi dole sai dara nata saboda ita uwa ce kuma ta bata shekaru masu yawa, a take zuciyarta ta raya mata sarewar ba ta ta ba ce, sai dai bata nuna mata hakan ba kuma bata ce mata komai ba har ta shige dakinta. Ajiyar zuciya ta sauke ta taka zuwa kofar dakin Maleek ta tura ta shiga, hango shi kwance saman gado ya daga mata hankali cikin kulawa ta shiga dakin ta karasa har gurin gadonsa ta kai hannu ta bude blanket din da ya rufa da shi ta taba jikinsa ta jishi da zafi sosai kamar an kara a wuta.
“Subhanallahi”
Ya bude ido da sauri ya kalleta, sai yayi hanzarin tashi zaune yana kallon agogon bangon dake dakin, tun da ya kwanta bayan gama Sallah Magariba be sake farkawa sai a yanzu da hannu Ummi ta taba jikinsa.
“Baka da lafiya ne?”
Ummi ta tambaya, sai ya kai hannu ya taba jikinsa.
“Ba sosai ba”
Ya mike tsaye ya nufi bathroom, Ummi na zaune har yayi alwala ya fito ya nufi inda carpet yake shimfide ya tada ikama ya fara Sallah.
HUMAIRA POV.
Sai da ta taso daga makaranta sannan ta wuce gurin aikinta, daman ta kan yi hakan shiyasa ta fi kaunar duty dare, idan kuma har tana da duty rana kuma ga karatu wani lokacin suka yin canjen aiki ita da abokan aikinta, wani yayi amfani da lokacinta ita kuma idan ta dawo sai ta dauki lokacinsa, a haka dai take ta kai da kawo na ganin sun yi survive ita da iyayenta, ba abu ne mai sauki a gareta ta hada abu biyu a lokaci daya ba, kamar aikin Restaurant da kuma karatu da yake bukatar lokaci sosai, sai dai rashi da neman abun dogaro da kai ya saka a dole ta sabawa kanta da wannan wahalar har ya kan zama idan bata je aikin ba bata jindadi, kuma bata isa ta jefar da karatun da makomarta da na iyayenta yake ciki ba. Washe garin data dawo kowa sai tambayar ya fuskarta yake, wadanda suka samu labarin abun da ya faru daga baya kuma suka jajanta mata, ba sosai suke ake baki suna zaginsa ba, saboda akwai Security Camera tsoron suke kar su zure da yawa a duba Camera a gani su ja kansu matsala. Ita kanta da fargaba ta yi aikin na yau tana ta tsammanin ganin takardar kora daga mai gurin ko kuma ďansa dan gadara bata ga ko daya ba har ta gama duty ta direban gurin ya kaita gida.
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: *W_G -it's not free, pay 500 to 2451879008 Hadiza Abubakar Zenith Bank, then send the evidence to 08036126660*
23
Washe gari bayan gama Sallah Asuba Ummi ta shiga dakin Waira ta same ta zaune ta kasa ta takure guri daya.
“Kin farka? Ni ban san sunanki ba, ban kuma taba jin maganar ki ba, balle na fahimci yarenki ma”
Waira dai kallonta kawai har ta karaso kusa da ita ta zauna saman gado ta kama hannunta a hankali ta duba. Sannan ta rika ta ta mikar tsaye tana mata alama da ta tashi su shiga bandaki, bata yi musu ba, domin ita ma kanta fitsari ya cika mata mara kuma bata son shiga bandakin da take masa kallon ya fi dakinta ma ta yi fitsari, yadda kofar za ta yi kara idan aka tura ko rufe take tunani, Ummi ce ta bude mata ta shiga kamin Ummi ta yi mata alamar komai ta risina kasa ta juya baya ta saki fitsari a nan, ganin hakan ya saka Ummi ta yi saurin juyawa ta fice daga bandakin. Ba ta saba yin tsarki bayan fitsari ba hakan ya saka bata yi tsarki ba ta mike tsaye taja wandonta sama ta juyo ta fito. Duk yadda Ummi ta yi juyim duniya ta nuna mata yadda zata wanke baki sai ta ki idan ta mika mata brush ai ta yi irin yadda ta yi a gidansu Shuraim wato ta lashe man ta aje brush din, sai da Ummi ta kama fuskarta ta wanke a fanfo ta nuna mata ta yi alwala a nan kam ta girgiza kai domin ta fahimci ibada ce suke wacce ba irin tata ba, ta ga hakan tun a gurin Ameer da kuma Dr Shuraim.
Ummi bata cilasta ta yin alwala ba, daman tana kallonta ta san ba addininsu daya ba, sai ta janyo hannunta ta fito da ita, bata tsaya da ita a dakin ba, ta fito da ita har waje saboda ta sha iska kuma ta dan sake jiki da su. Sakin baki ta yi ta daga kai tana kallon sama dakin tun da take a rayuwarta bata taba ganin gidan da ana gina aka kawata ginin da kyalen kyalen duniya ba irin wannan, bin Ummi kawai take a baya suna saukowa idonta na akan falon, ba ma kamar da idon nan nata ya sauka akan plasma dake kashe, bata san me ake da ashi ba, amman zata iya tuna ta ga irinsa a gidansu Dr Shuraim sai dai na su be kai wannan girma ba, gurin saka plasma da aka yi har wata wuta ke fita a gurin ga an dora kananan fulawoyi an masa decoration. Saman cushion Ummi ta zauna da ita sai ta ji kamar ta zauna a saman ruwa saboda sanyin ac da ya sauka akan kujerun ga laushin da suke da shi kamar kaďa, da sauri ta sauka ta zauna kasa.
“Zan je na shirya abun karyawa”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.