Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 69 of 227

“Ba zan hana a fadawa police ba, amman dai zuwa garinsu ai kamar tona mata asirine idan ma yan garin ba su san inda take ba, ka ga mun bude musu hanya sai su aikata mata abun da suke so, kuma fa ta fada ma Jabir iyayenta sun rasu bata san iyayenta”

Ya kai hannunsa ya dafa kafadar matarsa a kokarinta na saitata a hanyar da yake ganin za au bulle musu.

“Madam, ki zauna da ita ki yi hira da ita cikin hikima ki yi mata tambayoyi ki saurari labarinta ko iya ta nan zamu gane gaskiyarta kuma mu fahimci halin data fito, sannan na sha miki magan akan nunawa yarinyar addini amman baki kula da wannan”

Ya aje cup din dake hannunsa.

“Na kan nuna mata tallar addini ne kawai ban fara mata ba, kuma ka san ba ayi ma mutum dole a addinin musulunci”

“Na sani, amman yanayin mu'amalarki da ita da kuma yadda kika nuna kyaun addinin shi zai saka ta ji tana sha'awar shiga, ya kamata ki rika nuna mata wasu abubuwan”

“Zan yi kokarin yin haka”

“Toh Allah yayi miki albarka, ya bada iko Hajiyata”

“Ameen”

Ta amsa da murmushi, sannan ta mike tsaye tare da daukar cup din tana fadin.

“Bari naje na duba Aunty Zainab”

“Duk ke kadai wai aikin gidan nan be miki yawa ba? Ya kamata dai a kawo miki mai taya ki gaskiya”

Domin kawai ya tsokane ta yayi maganar, sai ya yi sara akan gaɓa ya sosa mata inda yake mata kaikayi.

“Kamar kasan abun da yake raina kenan Wallahi, kawai na rasa ta ina zan fara maka maganar ne”

Dariya yayi

“Kamar gaske, mata ai basa son abokiyar zama balle ke da na san ki da kishi”

“Kishi ai na yara ne ranka ya dade, yanzu mun wuce wannan kuma har ga Allah ina son ka karo wata saboda ka samu mai maka wasu abubuwan ko da bana nan, kara ka saba tun yanzu abun zai fi maka sauki”

Ba fahimci yarenta, hakan ya saka shi nitsawa a duniyar zoyalarta da yake.

“Kuma idan na tashi kawarki zan auro”

“Ai ba ni kawar da bata da aure a yanzu, a dai duba mai mutunci wacce zata son yayanka”

“Hauka kenan ban yi aure da kurciya ba zan yi shi yanzu da furfurata a gemu, yayanki ma ai ba za su bari ta zauna lafiya ba, ke din dai ke ce Allah ya bar min abata har mutuwa ya sa ke za ki min wanka”

Ummi ta yi murmushin da ita kadai ta san abun da take sakawa a ranta sai kuma Allah.

After like 30 minutes da barin Ummi da Abiey bangaren, Mahmood ya dawo gidan tare da Jabir da Umar, ba su shiga bangaren Ummi ba sai suka tsaya a dayan side din da mostly idan aka yi baki a nan suke sauka saboda wadatar gurun kuma an samar da komai a ko wanw ďaki. A waje suka ci na su abincin na dare dan haka ba su damu da leka bangare ba Ummi ba. Maleek kuma be fito daga dakinsa ba sai karfe ďaya saura, ya sauko sanye da nasa pajamas din, Plasma dake kunne ya fara nufa ya kashe, yana juyowa Waira na farkawa sai ta tashi zaune tana kallonsa da idonta masu kamar na mage. Tashi tayi ta dauki wayar Ummi dake kusa da ita ta haura sama, bata dade ba ta sauko har lokacin yana tsaye gurin Plasma doing nothing thinking nothing, zuwa ta yi ta boya bayan cushion din da ta kwanta. Sai da ya fara kallon gurin for like 15 to 20 seconds sannan ta taka a hankali ya leka, sai ya same ta ta kwanta a kasa ta takure guri daya take rike da wayar Ummi, ba tabawa take ba ta dai rike wayar kawai. Upstarts ya nufa yana hawa ya tura kofar ďakinta a hankali sai ya hango Yesmin kwance a kan gadonta, slowly ya rufe kofar ya nufo downstairs, saukowa tai daidai ta fitowar Ummi daga bangaren Abiey rike da cup a hannunta.

“Aljanin dare baka kwanta ba?”

Ya ďan yi murmushi kaďan kamar na amsa mugun dole.

“Abinci nake son ci”

“Okay”

“Yarinyar nan bata kwanta ba”

Ummi ta juyo tana kallonsa domin ta yi rabin falon, jin muryar Ummi ya saka Waira ta fito daga inda take ta nufo Ummi.

“Waira Baby kin tashi?”

Ta daga mata kai.

“Kina jin yunwa”

Ta daga kai.

“Zaki sha tea? Ko madara?”

“Tea”

Ta amsa, sai Ummi ta kama hannunta.

“To zo muje mu hada tea”

A tare suka shiga kitchen din Ummi ta hada tea a cup biyu ta bata ďaya ďayan kuma ta ce ta dauka ta kaiwa Maleek, sai ta girgiza mata kai.

“Aa”

“Dauki ki kai masa ba ni na saka ki”

Ta aje nata cup din ta dauki na Maleek ta fito kitchen din tana tafiya a hankali ta nufi inda yake zaune a dinning yana cin nasa abincin daren, kusa da plate din da yake cin abinci ta aje masa tea a hankali. Sai ya dago ya kalleta.

“Tea Ummi ta ce Waira ta kawo Tea..”

Ta fada sannan ta juya ta nufi hanyar komawa Ktchen din yana binta da kallo.

©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[6/17, 10:49 PM] My S Line: 29

“Kin kai masa Tea”

Ta daga sai Ummi. Ta girgiza mata kai.

“Bude baki yi min magana”

“Waira ta kai ma Ya Maleek Tea”

Ta saka Yaya ne saboda haka Nimra ke kiransa.

“Ba haka ake cewa ba, cewa zaki yi Na kai ma Ya Maleek Tea din”

“Na kai ma Ya Maleek tea din”

Ta maimaita kamar yadda Ummi ta bukata, sai Ummi ta yi murmushi.

“Good daga yanzu idan na yi miki magana ki rika bude baki kina amsa min, kin ga dazun na ji haushi duk zamana da ke a gidan nan baki taba bani labarinki ba, amman wani yana zuwa kin fada masa komai har dariya kike masa sosai ana jin muryarki ko'ina”

Ummi ta yi sad face tana bayyana damuwarta a fili, sai Waira ta kama kunnenta ta ce.

“I'm sorry Ummin”

A karo na biyu Ummi ta sake yin murmushi.

“Good na yi hakuri amman karki sake kin ji ko?”

Har ta daga kai sai ta tuna da Ummi tace ta rika bude baki tana mata magana, a take ta ce.

“Tohm”

“Minene Good ma?”

Ta mata thumps up tana dariya.

“Yayi kyau”

Ummi ma dariyar ta yi ta dauki tea ta mika mata, muje falo ki zauna ki sha idan kika gama sai ki kwanta. Kamar mai jiran umarni sai ta karba ta juyo ta fito kitchen, gurin da set din kujerun falon suke zata nufa sai Ummi ta dakatar da ita.

“Zo ki zauna a dinning”

Ta juyo sai ta kalli Maleek dake zaune yana ci abinci ta kalli Ummi, Ummi taja mata kujerar dinning dake kusa da Maleek, ta mata haka ne saboda ta sake jiki da shi, domin shi ne kadai mutumen da bata shan inuwarsu sai kuma Namra. Bata son musu hakan ya saka ta taka a hankali ta isa gurin ta zauna a kujerar da Ummi taja mata, ta rike tea da hannu biyu marikin cup din ta yi sama da shi, haka take idan tana shan tea ko a abu a cup sai ta rike da hannu biyu. Bayan ta zauna Ummi ta bar dinning din zuwa duba bakinta, jikinta ya bata Maleek kallonta yake hakan ya saka ta juyo ta kalleshi sai ta ga idonsa yana kan zoben dake wuyanta, ta kalli zoben sannan ta dago sai suka hada ido.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.