Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 160 of 227

Ummi bata da karfin cewa komai a yanzu, ta san Abiey ba zai fahimce ta, haka ma Ameer ba fahimtar da zai yi ba.

“Allah ya zaba mana abun da ya fi zama alheri, bari na shiga kitchen”

Ta wuce ta nufi kitchen, yana ganin haka ya san akwai abu a kasan zuciyarta daman shi ma juyawa yayi ya fice daga falon ya koma bangarensa. Sai da ya wuce sannan Waira ta sauko daman tun dazun tana labe a saman ba dan tana ji abun da suke tattaunawa ba kuma ba dan tana son ta ji din ba, sai dan bata son Abiey ya ganta, domin zuciyarta na yawan raya mata Abiey baya sonta. Ta sauko ta shiga Kitchen sai ta Ummi ta rike fridge sai kuka take a hankali, ta saba ganin Ummi a kitchen da asubar fari irin haka, amman sai idan akwai dalili kamar tana son shirya abun karyawa da wuri saboda wani ko ita, amman a ka'ida Ummi bata shiga kitchen sai 6:30am ko 7 ma.

“Ummi...”

Ummi ta juyo ta kalli Waira da ta kira sunanta, sai ta ji kamar ace tana da wani iko da zata cewa Waira ki cire sonki a cikin zuciyar kowa.

“Are you okay, ko Abiey ya miki fada ne na ganshi ya zo”

Ummi ta share hawayenta.

“Labe kike mana?”

“Aa na zo zan shiga dakinki na dauko abun sallah ne sai na hango kin fito na zo saukowa sai na ganshi shiyasa na koma na boya na san ai baya so na”

“Abiey be tsane ki ba Waira ki daina saka wannan a zuciyarki”

Ta daga mata kai son sanin damuwar Ummi da abun da ya saka ta kuka ya saka Waira tambayar Ummi.

“Ummi can I hug you?”

Ummi ta daga mata kai, sai ta rumgume Ummi ya rufe ido, babu abun da bata gani ba, tun daga kan maganar da Ameer ya fadawa Ummi har zuwa wanda Abiey ya fadawa Ummi akan Maleek da kuma na yau da Abiey yayi magana da ita. A cikin duk abubuwan bata ga na damuwa ba, da zai saka Ummi kuka ba, domin duk cewa suke suna sonta ita kuma a gurinta haka abun ne mai kyau sai dai kalmar aure da ta yi ji a ciki shi ne abun da ya fi daga mata hankali. Ta dago daga jikin Ummi ta kalleta sai Ummi ta sakar mata murmushi.

“Mun yi magana da Abiey ne akan yana son ya fitar dake wata kasar ki yi karatu”

“A nan fa?”

“Ba wai na aminta ba ne, zan yi shawara na ga idan hakan ya dace kuma idan kina ra'ayi”

“Bana so, bana son wani gurin da ba nan karatun da nake a nan ma ya isa ai, ba kullum ina zuwa school ba, Mai Lesson ne ya daina zuwa ai amman ni ban fasa yin darasi ba”

Tana fadar haka ta saki Ummi ta fice daga kitchen tana shirin yin kuka.

AMEER POV.

“Abun is na ma rasa me zan ce”

Ameer ya hade yawu yana marairaice fuska kamar gaske.

“I know shiyasa tun farko ban fada ba, amman yanzu ina kokarin ganin na gyara abubuwan da na bata ne, dan Allah karka min mummunar fahimta ne”

“Nonono ka yi tunani mai kyau, amman aure ba abu ne da za ayi wasa da shi ba, kuma a yanzu da kake kokarin gyara abubuwa hakan yana da kyau, sai dai dole ne ka nemi afuwar yarinyar”

“Zan yi haka Daddy, na gode sosai da fahimta, me kake son mu tattauna?”

“No karka damu wata rana zamu yi magana akai ci abincinka”

Daddy ya fada da murmushi a fuskarsa, Ameer ya fara cin abincin yana jin wani iri, domin be tsaya ya saurari shakuwar Daddy ba, kuma be kamata yace masa no a duk wani abu da zai gabatar masa ba, shi dai be masa wannan karyar dan kawai ya hana shi fadar abun da zai fada ba, sai dan ya samu mafitar gabatar masa da Waira kamin shi ya gabatar masa da wata a matsayin matar aure.

“Daddy ba zan jidadi ba idan baka fada min abun da kake son mu tattauna ba, please ka fada min ko gankali zai kwanta”

“Zan fada maka amman ba yanzu”

Cewar yana murmushi sai dai zuciyarsa ta kasa yarda abun da Ameer ya fada masa a yanzu, kuma ya kasa natsuwa wata kila saboda ya ji abun ne wani irin kamar ba abun da kai zai kama ba. Ameer yayi bachi a daren mai dadi da saka nishadi, saboda tunanin Waira. Washe gari da 6:30am ya fita daga gidan zuwa gidan Ummi saboda ya samu kai Waira School da wuri, domin ya daukarwa kansa nauyin kaita makaranta kullum kuma ya daukota. Bakwai da yan mintuna ya iso gidan ya shigo falon yana ta zuba kamshi. Sai dai yana shigowa ya tararda Mahmood da Maleek da Namra a dinning sai ya saka jin babu dadi, kara ma Mahmood suna dan good time da shi, amman Maleek da Namra makiyansa ne kamar yadda shi ma suke kallonsa a makiyansu, Sai dai ganin Ummi da yayi ya dan saka shi jin sanyi, ya karasa gurin cikin gadara ya dafa kujera ya gaishe ta.

“Ummi ina kwana”

Ta dago ta kalleshi yanayi fuskarta da idonta sun fada masa ba lafiya ba.

“Lafiya Kalau how was your night?”

“Alhamdulillah”

“Ga breakfast din nan”

“Let me drop Waira makaranta first”

Yana fadar haka ya juya ya nufi upstairs, Maleek ya ji kamar ya juya ya ce masa wani abu, sai kuma wata zuciyar ta hana shi sai dai be jindadin yadda yake kai Waira makaranta a kullum.

“Ya iso nan baku gaisa ba? Anya rayuwa zata yiyu a haka? Kuna abu kamar ba yan'uwa juna ba, sai k”

“No Wallahi mantawa na yi mun saba gaisawa da shi ai”

Mahmood ya fada yana wanke kansa Namra da Maleek ne dai ba su ce komai ba. Hakan kuma be yi ma Ummi dadi ba. Ameer ya haura sama ya tura kofar dakin Waira ya shiga, sai ya same ta zaune saman gadon tana ta kuka shabe shabe har muryata ta shake. Da sauri ya karasa kusa da ita ya risina gabanta ya kai hannunsa ya dago fuskarta tashin hankali ganin hawayen sahibarsa karara a fuskarsa.

“Lafiya waya taba ki?”

“Bana so Ummi tace Abiey zai kai ni wata kasa karatu, ni kuma bana so”

Cikin tsananin kuka take fada masa iyakar gaskiyarta bata son barin gidan nan, domin ta sha wahala kamin ta sabu da su, taya za a kaita wani gurin kuma inda bata san kowa ba? Kukan da take na kiyayyar tafiyar ne Ummi bata ma san tana kukan ba, gaba daya tunaninsu tana ciki tana shiryawa.

“Abiey baya so na na sani shiyasa zai min haka”

Ta sake fada cikin muryar kuka. Ameer ta mike tsaye rai a bace ya fice daga dakin tun kamin ya sauko kasa ya fara aiko da tambaya rai a bace yana nuna upstairs.

“It's because of na ce ina son Waira shi ne Abiey zai dauke ta ya kaita waje karatun?”

Gaba dayansu suka dago suna kallonsa, Mahmood da Waira da ba su san abun da yake faruwa ba suka ji abun kamar daga sama. Ummi ta nufeshi da sauri tana girgiza kai.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.