Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 177 of 227

“Ameer ya ba ni mamaki Ummi, kamar ba shi ba”

“Ciwon So kenan Namra, mai haukatar da mutum mai tsutsuta bawa ya firgita kwakwalwarsa, mai rufe idon mai yinsa ya saka yin abubuwan da ba su dace ba, i was in his shoes before shi ya saka na aikata duk abun da na aikata a yanzu, Abiey ma hauka ne kawai be yi ba a lokacin da ya rasa ni, amman Ciwon So ciwo ne mai wahalar magani”

Ummi was talking from experience tana kallon kofar dakin har lokacin. Wani bangare na yarenta kawai Namra ke iya ganewa domin ita ma ta ga zahiri a abun da ya faru da yar'uwarta, kuma ita tana cikin dakin so.

AMEER POV.

“Zaki yi ta yin kuka ne har hawayenki su kare Nuwaira?”

Ta dago ta kalleshi.

“Baka san yadda nake ji ba, bana son rabuwa da kowa”

Yayi murmushi domin shi kan ya fita sani da jin duk wani abu da take ji na kewa da zata yi da mutane.

“Duk yadda kike ji, na fiki jin haka ke kewa ce kawai kike ji a ranki, ni kuma wata kalar azaba da radadi nake ji, saboda zaki tafi ne da ruhina na zuciyata, ban san ya zan kasance ba idan kika tafi, hauka zan yi? Ko kuma zan iya jurewa na yi hakuri na cigaba da rayuwa da tabon da kika min a zuciya, duk yadda zan misalta ba zaki taba ganewa ba, amman dai Daddy ya dora ni akan shawara, ta addu'a da neman zabin Allah kuma na dage da haka, wata kila babu alheri a tarayya ta dake shiyasa ma kika dage sai kin tafi, sannu sannu komai zai yaye har na manta da ke”

Yana maganar tana kallonsa har ya gama be kalleta ba, ita kuma bata fasa kallonsa ba har suka isa gidan, sai a sannan ya cire tissue ya mika mata. Ta karba ta share hawayenta ya fita motar ya zagaya ya bude mata ta fito ya rufe motar suka jekara suna tafiya har suka shiga cikin falon Mummy ta fara yi musu lale marbabun fuska a sake baki har kunne.

“Sannu da zuwa Marhabun lale”

Mummy da yayanta suka tarbi Nuwaira da farinciki da jindadi, Ameer da kansa ya shiga ya sanar da Daddy zuwan Nuwaira suka jero a tare suka fito daga bangaren, Daddy kamar ya hade Nuwaira ba saboda Ameer yana sonta kawai ba, sai dan addinin musulunci da ta shiga ya kara mata kwarjini da farinciki a gurin kowa. Liyafa Mummy ta shirya mata, sai dai ita kasa cin komai ta yi saboda tunanin gaba da take. Bayan sun gama cin abincin Daddy ya aika yarsa ta dauko masa ajiyar da yayi a dakinsa, ya gabatarwa da Nuwaira, sarka zinari ce mai matukar ktau da tsada irin mai cika wuya wadda ke hade da abun hannu da agogo.

“Wannan duka na ki ne, ina fatar idan kin tafi ba zaki manta da mu ba, musamman ma ďana Ameer, yana yawan maganarki kusan ya zama kamar wani soko akanki, ki rika tunawa da shi kina masa addu'a ko dan silar shigar da yayi miki a addinin Allah mai tsabta da natsuwa”

Ta saka hannu biyu ta karba, ba lallai ta fahimci minene ba saboda a garensu ba haka ake sarrafa zinariya a yi ado da shi a garinsu ba. Amman ta san abu ne mai kyau da tsada ganin yadda yake daukar ido.

“Zinari ne wannan, yana da kyau sosai”

Ta girgiza kai da sauri.

“Ba zan iya karbar wannan ba yayi yawa”

“No ba a maida kyauta karki ce haka ki karba mana”

Mummy ta fada tana kallonsu da murmushi. Godiya sosai Nuwaira ta yi ma Daddy har ta rasa kalaman hadawa ta nuna masa farincikinta. Mummy ma ta yi mata kyautar turaruka da earring masu kyau na GL da lace mai kyau. Suka rakota har gurin mota ta shiga suna daga mata hannu.
[8/6, 7:07 PM] 𝐊𝐡𝐚𝐝𝐞𝐞𝐣𝐚 𝐂𝐚𝐧𝐝𝐲: 72

A tunaninta gida Ameer zai nufa da ita kai tsaye bayan ya bar gidan Daddy. Sai ganin ganin ya faka a gaban wani gate ya fita ta bude gate din ya shiga da motar ya sauya tuninaninta.

“Ina ne?”

Ta tambaya a lokacin da ya bude mata motar take kokarin fitowa.

“Kakata yau suka tare, na fada mata zan kawo ki, ki musu bankwana”

Kamin ya rufe motar Humaira ta fito rike da waya a kunnenta amman hakan be hanata yin welcoming din Nuwaira ba, cikin kyakkyawar tarba fuska a sake. Ameer ya wuce gaba Nuwaira ta bi bayansa har suka shiga cikin falon da ba a gama sakawa kaya ba, shi ya fara yi mata nuni da inda zata zauna sannan ya shiga dakin farko dake cikin falon. Humaira ta shigo after minutes da zaman Nuwaira a falon tana sake mata maraba da zuwa.

“Sannu da zuwa, Ameer yana yawan ba mu labarinki, kusan kowa ya san ki tun farko fara haduwarku ya fada kin yadda ya rikice akanki, bari na baki abun sha kar na cika ci da surutu”

Ta tashi ta shiga dakin da ke nuna madafa ce ta dauko mata ruwa da taliyar da ta girka, domin su ne kadai abubuwan da zata iya samu for now a gidan, kasancewar tarewar ta wuri ce kuma hankali Ameer ba kwance ba, be gabatar musu da komai ba, arzikinsu daya Daddy be manta da su ba, shi yayi musu komai a gidan. Nuwaira ta kai hannu ta dauki ruwan ta rike kamar wadda bata san abun da zata yi da shi ba. Can kuma ta daga kai tana kallon Ameer davya fito dakin Hajiya na bayansa tana takawa a hankali da sandar guragu, Bahijja na bayanta sai leken Nuwaira take kamar ba zata karaso kusa da ita ta kalleta ba.

“Sannu da zuwa yau bakuwar Ameer ce a gidan mu”

Nuwaira ta mike tsaye tana kallonsu, sai wani irin take ji, ta bakuncin mutanen da suka san da labarinta ita kuma bata san su ba. Hajiya ta karaso ta zauna tana kallon Nuwaira ita dai zuciyarta bata gamsu da yarinyar ba, ba dan tarbiyarta ko wani abun ba, sai dan ganin take ta fito daga bangaren Ummi ne, ganin take idan ya aureta Ummi zata sake dauke mata shi ne bayan duk abun da ta yi da farko, hakan na nufin ta ci nasara kenan. Cikin rashin natsuwa da sakin jiki Nuwaira ta gaisa da su, sannan ta yi musu sallama suka fito ita da Humaira ganin kamar Ameer ba zai fito yanzu ba.

“Da alama kin matsu ki bar gidan nan”

Ta kalli Humairah bata san me zata ce mata ba, domin ta san gaskiyar Hunairah ta fada, tabbas ta matsu ta fita saboda rashin sabon da bata yi da su ba.

“Karki damu, zamu taba da juna babu jimawa, domin na san Ameer yana sonki sosai irin son da ya wuce kwatance balle a kwatanta, ya wuce zane haka ma ya fi karfi fada, balle kuma ace alkalami ya rubuta, fatana dai ki share masa hawayensa ko san wahalar da ya sha”

Kallon Humaira kawai Nuwaira take kamar wadda bata fahimci abun da take fada ba. Fitowar Ameer ne ya saka Humairah ta dan matsa baya domin ba shi guri.

“How kika ji sabon gidan na ku?”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.