Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 109 of 227
Iyakar kokarin da ta yi na danne abun da ta ji ne a lokacin da ya ambaci cewar zai so zuwa ko dan Waira.
“Ban gane ba, me ka gani a gurin iyayena kuma?”
“Sai na ga kamar ba jindadin zuwa na ba, bayan na gama bayyana musu ko ni waye, especially your Dad yanayin yadda yake amsa min ya nuna cewar ya san mahaifina, kuma kamar be yi maraba da ni ba”
Alamar mamaki ne ya cika fuskarta domin bata jin wannan ba, saboda ba a gabanta ya gaisa da su ba, kuma tashin hankalin da suka samu kansu a ciki na ciwon Nimra ya saka ba ta yi maganarsa da kowa ba.
“Ka fada masa wanin abun da be dace ba ne? Ko kuma akwai wani abu a nasabarka da be dace kowa ya sani ba?”
“To ban sani ba a halin yanzu, har sai na samu mahaifin mun yi magana da shi, amman ni ma san babu wata illa a nasabata sai dai kamin na tafi ina bukatar sake ganin ki gaskiya, kuma ina son ganin yarinyar nan please”
“Kana dai son ganinta, ba da ni ba”
“Both ke da ina ina mamarin ganinku, ita saboda na kwantar mata da hankali ta natsu, ke kuma saboda nawa hankalin ya kwanta, so please ki saka mana meeting point kuma ki zo min da ita”
“When?”
“Yau if possible, idan kuma ba zai samu ba zan hakura har zuwa gobe, ba dan haka ba babu abun da zai saka na sake kwana garin Abuja”
“Zan kiraka idan abun da kake bukata zai samu”
“Ganinki mai samuwa ne na sani, sai dai fitowa da Waira ne ba ni da tabbaci, amman dai ki min kokari please”
“Okay”
“That's my Babe Girl i love you ”
Ta samu kansa ta kasa amsa masa da i love you too kamar yadda ta saba sai sakon godiya data aika masa ta kashe wayar, ta juyo yana kallon Nimra dake bachi. Me yasa Abiey yayi masa haka shi ne abun da ya fara zuwa a ranta kamin ta fara jin kamar ta tsani Waira saboda yawan maganarta da Shuraim yake dan zuwan nan da ya yi. Daf da zata zauna aka turo kofar dakin sai ta fasa zaman ta kalli Maleek da ya shigo fuska babu walwala ba kuma zata ce ransa ne a bace ba, domin ba ta ga alamun haka ba, ya kusa cin karfin damuwarsa dan haka bata bayyana a fuskarsa ba, yana a wani yanayi da abu ne mai wahala ka bayyana halin da yake ciki, damuwa ce ko bakinciki ko rashin lafiya da jindadi ba kuma zaka ce yana cikin farinciki ba, haka kuma baka isa ka ce yana nishadi ba.
“Sannu da zuwa”
Da kai ya amsa mata ya zauna a kujerar dake fuskantar Nimra, yana kallon kanwarsa ta rame sosai kamar ba ita ba, har yanzu oxygen ne a bakinta da hancinta numfashinta na tafiya wahala kamar dai wanda yake daf da bankwana da duniya.
“Ya jikinta?”
“Da sauki, gashi har ta samu bachi, da bata iya bachi kuma likitan yana tsoron yayi mata allurar bachi saboda yanayinta, amman ga dukan alamu yanzu sauki ya fara zuwa”
Hannu ya kai ya shafa kanta da babu dankwali yana jin tausayinta, domin ta fada tarkon mutumen da ya tabbatar ko sama da kasa za su hade ba zai aureta ba, gashi tana ta wahala akansa. Namra ma kallonta take har sai da wayar Maleek tayi ringing sannan hankalinta ya koma gurinsa.
“Ina asibiti gurin Nimra”
“Akwai maganar da nake son mu yi mai muhimmanci Maleek, akwai abun da ya kamata ka sani”
Mahmood ya fada a dayan bangaren.
“Akan ciwon Ummi?”
“No akan Ameer”
“Me ya kuma ya faru?”
“I can't tell you on the phone, sai dai fada min inda kake ko kuma ka same ni”
“Kana ina?”
“King and his Kingdom”
“Okay gani nan zuwa”
Ya sauke wayar, gabansa na faduwa zuciyarsa na raya masa ko Ameer ya sake shirya wani abun ne, domin King and his Kingdom ba gurin zuwan Mahmood ba ne, it's a very right or appropriate place for rich kids like them amman ba gurin zuwansu ba ne, kara shi ma yana dan taba fita da abokansa sometimes amman Mahmood ya zama Mommy's boy, idan ya dade ya be dawo gida ba har kira take ta ji yana ina, not like Maleek da ta san baya son zaman gida saboda halinsa a can ba, duk da haka kuma ba zata yi bachi ba sai duka yaranta sun dawo gida. Waceaganar ce da ba zai iya fada masa ta waya ba? Shi ne dalilin karin kuzarin Maleek na fice daga asibitin ba tare da jiran kanwarsa ta farka ba...
©Khadeeja Candy
©®Copyright
2023
[7/1, 9:32 PM] My S Line: 45
Ya shiga falon Daddy a wani yanayi da be taba shiga ba, wannan ne karon farko da yake jin wani abu mai kamar kunya da bakinciki saboda zai tunkari Daddy yayi magana da shi, tafiyarsa ma ta banbanta da yadda ya saba yinta. A kofar dakin Daddy ya tsaya ya share hawayen da suke masa zuba sannan ya kai hannu ya kwankwasa kofar ďakin sai kuma ya fasa ya duka a gurin ya dafe kansa hawayen da tsaya suka dawo suna masa zuba. Ganin yake kamar ba gane ba ne ace Daddy ba mahaifinsa ba ne, ya kuma kasa karbar karyar da zuciyarsa take masa. Sai da yayi da gaske sannan ya iya controlling kansa ya share hawayensa ya mike tsaye ya kwankwasa kofar dakin.
“Yes come in”
Gabansa na mugun faduwa ya tura kofar dakin ya shiga, kunyar da bata san ta ina ta fito ba ta lullube ya kasa kallon Daddy har ya zauna a couch, Daddy ya aje wayar hannunsa yana kallon Ameer cikin wani yanayi na tsoron da gargabar rasa ďansa.
“Baka saba kwankwasa min kofa idan zaka shigo dakina ba, kana shigowa ne kai tsaye idan kana so ko da kuwa bana cikin dakin nan, ka dauki abun da kake so, ko kuma ka fadi abun kake so, miyasa yau zaka shigo min tare da kwankwansa”
Ya daga kai ya kalli Daddy sai ya kasa, a take kallon da yake masa a matsayin uwa ya sauya zuwa na maigida da yaronsa. Daddy ya nufi kujerar da Ameer yake zaune ya zauna yana kallonsa.
“Ameer fada min damuwarka me kake so? Fada ka yi da wani? Wani ya taba ka? Ko ka sake kade wani? Mommy ce ta taba ka? Or...”
Daddy na tambaya Ameer na hawaye kuma ya kasa dagowa ya kalli Daddy har lokacin.
“Me ya same ka Ameer? Waya taba ka? Fada min komai kake so a duniyar nan zan maka”
Sauka yayi daga kan kujerar da yake zaune ya zauna a kasa ya kama kafar Daddy ya rike ya dora kansa a cinyar Daddy sai ya fashe da wani irin kuka mai taba zuciya. Daddy ya danne abun da yake ji a zuciyarsa ya cikawa bakinsa iska yana tunanin yadda zai bullowa Ameer domin bayan son ya nuna masa ya yi magana da Hajiya Jamila.
“Babban tashin hankalina a duniyar nan na ga tashin hankalin ďana, ina jure komai a duniyar nan ban da damuwarka, ka fi kowa sanin yadda nake gudun rigimar da kake shiga ko dauko magana, amman ni ne mutum daya da zaka gudu ka boya a bayana kuma na yi maka rumfa, na hana kowa taba ka, fada min Ameer me ka aikata? Wallahi ko rai ka kashe wannan karon na shirya baka kariya”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.