Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 201 of 227

Skylines Hospital aka kwantar da ita shi da abokin aikinsa Dr George suka dubata duk wani abun da ya kamata ayi mata suka mata sannan ya fito daga asibitin ya nufo gida. Yana fakawa harabar gidan ya ji wata mahaukaciyar yunwa ta sako shi gaba, kusan haka ya wuni kamar mai azumi sai da ya shigo falon Ummi ya nufi kitchen dinta ruwan zafi ya fara zubawa ya sirka da na sanyi zafin ya ragu ya dauka ya sha be ko iya jira ya hada tea ba.

“Waye a kitchen?”

Namra ta fada a lokacin da take saukowa stairs domin ga ga wulgawar mutum amman bata tantance ko waye ba, kai tsaye ta nufi kitchen din ta leka sai ta yi arba da Maleek with surprised ta ce.

“You...? Yanzu ka shigo?”

Ya daga mata kai kawai ya dauki plate ya fito daga kitchen din ya aje plate din a dinning.

“Zuba min abinci kamin na sauko”

Ya nufi upstairs, dakinsa ya shiga ya tsabtacen jikinsa ya canja tufafi ya fito ba tare da ya shafa komai a jikinsa ba, domin yunwar cikinsa ta kusan firgitashi. Spoon ya dauka da sauri ya fara cin abincin hannu baka hannu kwarya.

“Baka ci abinci ba since?”

“Gaba daya yau banci komai ba, sai yanzu ma nake jin yunwar Ina Ummi?”

“Tana asibiti?”

Ya kalleta da sauri.

“Nonono ba ciwonta ba ne, Ameer ne?”

Har yanzu ma kallonta Maleek yake domin jin ba'asin. Namra bata yi kasa a guiwa ba ta karanta masa komai a take ya tsayar da cin abinci yana yawo da idonsa a falon.

“Abiey fa?”

“Yana cikin gida, ina ita Nuwaira?”

“Tana asibiti bata da lafiya, shiyasa na fara aje ta can”

Ya zuba ruwa ya sha ya tashi ta dauki wani cup din ya hada tea ya dauki cup din ya nufi bangaren Abiey rike da cup din tea. Abiey na yi arba da dansa farinciki ya lullube shi ganin dansa lafiya kalau babu rauni a tare da shi sai gajiya da yunwar da ya kwaso har ta saukar masa da rama na wuni daya. Maleek ya zauna cikin jindadin abubuwan da suka faru ya fadawa Abiey komai, take dadi ya lullube Abiey jin yadda dansa ya zama Jarumi cikin birnin matsafa ya rinjayesu da karfin ayar Allah da tsaronsa, kamar wanda ya samu tv haka Abiey ya rika kallon Maleek yana alfahari da shi. After ya gama bashi labarin ya dauko maganar Ameer Abiey ya girgiza kai.

“Namra ta fada maka ko? Umminku ma tana can asibiti ance bachi yake amman tace ba zata dawo ba sai ya farka”

“Daman na yi tunanin haka, shiyasa da yayi ta kirana na ki na daga, saboda ba zan iya masa karya ba, kuma na san gaskiyar zata yi effecting dinsa, and i san Ameer irin mutanen nan da idan rai ya bace basa iya controlling kansu, and zai iya facing komai ba”

“Na dai fada masa, ya kamata ya kiyaye ko dan mahaifiyarsa”

“Yes”

Maleek ya amsa sannan ya mike tsaye ya aje cup din.

“Bari na leka asibitin daga sai an fada mata halin da Nuwaira take ciki, saboda a samu wanda zai kwana a tare da ita asibitin”

“Okay ka cigaba da rike addu'a fiye da da Maleek”

“Dole ai Abiey, ni na ga tasirin addu'a a zahirinta kuma hakan ya kara min kwarin guiwar rike ta da hannu biyu”

“Good Allah ya kara tsarewa, bana shakkar ka shiga ko'ina Maleek I'm proud of you”

“Thank you”

“Idan ta farka Cp yace min za su dauki statement dinka da nata saboda gaba, kuma tsarin haka yake dole san komai ya faru”

Daf da zai fice Abiey ya fada masa haka, sai ya amsa da.

“Okay”

Sai da ya sake komawa bangaren Ummi ya shiga dakinsa ya dauko keys da waya sannan ya dauko ya fice daga falon. Wata motar ya dauka ta dabam ba wadda ya dawo da ita ba, sai da yayi warming dinta sannan yayi reverse masu gadim suka bude masa gate. Tun da ya kama hanyar asibitin yake tunani daya har ya isa, a harabar asibitin ya faka ya fito ya nufi masallacin yayi alwalar Magariba ya shiga ya gabatar da sallah tare da mamu sannan ya fito ya kira wayar Ummi tana ganin kiransa ta daga da sauri.

“Maleek I'm sorry na manta ban kira ba how are you?”

“I'm fine Ummi kuna ina? Na shigo asibitin”

Yana tafiya tana fada masa har ya isa. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya tura kofar dakin ya shiga sai ya samu Ummi da Fiyya zaune akan carpet din dake shimfide kasa Ameer kuma yana kan gadon goshinsa da kasa, da alama taimama yayi kamin Sallah Magariba a madadin alwala. Tun da ya dago ya kalli Maleek sau daya ya sauke kai be sake kallonsa ba har Maleek ya iso kusa da shi.

“Ya jikin?”

Maleek ya tambaya.

“Alhamdulillah, ya hanya? Hope kun iso lafiya”

“Lafiya kalau nake ni, ita dai Nuwaira tana asibiti amman ita ma da sauki ina tunanin ciwon da ta ji ne sai gajiya da tsoro”

Ummi ta mike tsaye cikin karfin hali ta nufi inda yake tsaye tana taba jikinsa ta duba wai ko ya ji ciwo sai kawai ya saka dariya.

“Lafiya ta kalau fa Ummi sai da muka gama magana da Abiey sannan na iso nan I'm fine”

“Zaka iya boye min ai”

“Amman kin san idam ba lafiya nake ba Abiey ba zai bari na zo nan ba”

Sai ta sake shi.

“Ita kuma fa?”

“Tana asibitin da nake aiki, amman da sauki Abiey ya fada min tun da rana kike nan, ya kamata ki tafi ki duba Nuwaira daga nan sai ki wuce gida Hanne ko Namra su je su kwana da ita, karki ce min zaki kwana a nan please”

Ameer ya ce.

“Ni ma ba zan bari ba, ta ga jikin nawa ai da sauki maybe ma su sallame ni soon”

“Toh wa zai kwana da kai, Mommy ka tafi fa, Humairah kuma na ce Mahmood ya aje su gida ita da mahaifiyarta da Hajiya, kuma mun yi da su gobe yaje ya dauko ta tare da Hajiya ta sake dubaka saboda na fada musu zan kwana a nan”

“Ga Fiyya zata kwana a nan”

Maleek ya kalleta. Sai ta ce

“Yes I'm his sister zan iya kwana a nan, ina wuni”

“Shut up mace da ke? Duka zaku iya tafiya zan kwana a nan”

Da mamakin Ummi da Ameer suka kalleshi sannan suka kalli junansu. Fiyya ta dan turo baki daman tana yaba masa a rashin mutumci gashi yau ma ya gwatsaleta.

“Ni ba gida zan kwana ba yau ai na fadawa Daddyna”

“Toh sai ki bi Ummi idan kun duba Nuwaira sai ki kwana a can, because ba zan kai ki gidanku yau ba, sai dai ki kira a zo a dauke ki”

Ta lake kafada ita ala dole gata autar gidansu. Ummi tace.

“Karki damu zan saka ya kaiki gida”

“Ba zan fa kaita ba, duk rigimar yarinyar nan bata kai Nuwaira ba tun da kuwa har na iya da Nuwaira ke ma zan iya dake Ummi mu je na kai ki ki dubata sai na sauke ku gida”

“Be ci abinci ba, abinci zan ba shi”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.