Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 17 of 227

“No karku zo yanzu, Ummi fada take zan kira ka later”

Be jira cewar Dawood ba ya sauke wayar ya nufo kofar dakin ya bude ya fito, tsaye yayi a stairs din yana kallon mahaifiyarsa dake zaune Namra na rumgume da ita tana kuka.

“Matsalata da ku karamin abu sai ku mayar da shi babba, miye abun kuka a nan kuma?”

Nimra dake tsaye rike da keys din da alamar shigowarta kenan ta watsa masa harara kamar wani sa'anta.

“Ba komai ba ne? A saka maka abun da zai iya zama sanadiyar lalacewar rayuwarka ko ma rasa ran gaba daya? Sannan ka ce ba komai ba ne? Ba laifinka ba ne mu muka da mu da kai”

Ta risina kusa da Ummi ta rika hannunta.

“Ummi dan Allah ki daina zubar da hawayenki a banza, ki daina damuwa da Maleek dan girman Allah, ta so mu je ciki”

Ummi ta mike tsaye Nimra na rike da hannunta ta juyo a hankali ta fara takawa, Maleek kuma ya fara saukowa tare da kawarda fuskarsa daga barin kallon kukan da mahaifiyarsa take yi. Hajiya ta lumshe ido ta hade yawu wannan karon ba kuka take na abun da aka yi ma Maleek ba, kukan marmarin danta Ameer take, ko a wane hali yake ciki a yanzu? Waya yake kula da shi a yanzu? Su waye abokansa? Wacece uwar rikonsa? Tana bashi kulawa kamar yadda danta yake samu? Har yanzu Mr Bashir yana kaunarsa kamar da ko kuma ya sauya? Yana ma raye ko ya mutu?

“Ummi...”

Kamar wacce ta farko daga dogon bachi haka ta bude ido da sauri ta kalli Nimra dake rike da ita, sai ta sake fashewa da kuka ta kwantar da kanta jikin Nimra.

“Ba zan taba zama lafiya ba Nimra, ba zan sake samun farinciki domin na siyar da shi da dadewa, shiyasa kullum da kalar kalubalen dake fuskantar yayana ko kuma ni”

“Ummi me kike fada haka ne? This too shall pass, ki daina saka kanki a damuwa please, idan kina saka damuwa a ranki muma sai ki saka mu shiga wani hali, muna bukatar rayuwarki Ummi”

Ta kalleta sai ta yi murmushi cikin hawaye, daf da zata kai hannu ta share hawayen Abiey ya shigo falon yana fada kamar zai tashin falon.

“Sai ga waye uban yaron nan a Abuja, sai na ga abun da yake takama da shi a garin nan, sai an daure min shi a ceil”

Ummi ta kara hanzarin kai hannu ta share hawayenta, karaso kusa da shi tana tambayar abun da ya faru, Maleek ma kallonsa yake kamar yadda Nimra ma take yi.

“Miya faru?”

“CP ne ya kira ni, wai yaron baya garin nan, amman mahaifin yaron ya bada hakuri, daga shi har yaron babu wanda ya je gurin, ni za a nuna isa? A taba min yaro kuma ace za a taka ni?”

Maleek yayi tabe baki abun mamaki ba ne idan aka ce Ameer yaki zuwa gurin, kadan daga cikin halinsa ne, kuma mahaifinsa zai goya masa baya akan haka.

“Indai wanda nake tunani ne, ba zai je ba daman, kuma baka bukatar yin komai akai Abiey mahaifinsa yana da kudi sosai, zai iya yin komai ya kare dansa, wannan wasan a tsakaninmu ne, dan Allah ka hakuri ka kyale ni da shi kawai”

“A tsakaninku? Wannan ya wuce a tsakaninku, komai Ubansa ya Mallaka sai na hukunta yaron nan, kuma kar na sake ganinka da abokan nan naka”

Ummi ta kalleshi kamar ta yi magana sai kuma ta yi shiru ta sauke ajiyar zuciya. Namra ta yi kwafa tace

“Wannan abun ya zama rainin hankali, danka ya aikata abu kuma ka kasa zuwa balle har ka tura shi ya bada hakuri, ta ina za ayi musu iyaka kenan? Kuma hakan ai zai bashi damar sake aikata wani abun a nan gaba”

“Na fadawa CP shi idan ba zai yi ba, zan saka DSS su kama shi, kuma sai na hukunta shi ko dan ya zama izina ga wasu”

Sam ran Maleek baya son abun da mahaifinsa Abiey yake kokarin aikatawa, sai dai be isa ya hana shi ba, ya san idan ya nuna mahaifinsa hakan zai bude wani sabon shafin fadan ne a tsakaninsu, domin Abiey baya wasa da abun da ya shafi iyalinsa, musamman yayansa a yanzu.

AMEER POV.

Rabuwarsu da Nimra da uku ya bude motarsa ya shiga, ba mutum ne ma'abocin yawo ba, duk kuwa da kasancewarsa tantari gurin zuwansa uku ne idan baya gida yana tare da abokansa idan baya can yana tare da falkarsa sai kuma a yanzu da ya samu wannan gurin zuwa da yake haduwa da Nimra. Gurin da suka saba zama da abokansa ya nufa sai ya samu gurin a rufe, abun da ba a taba ba.

“Miya faru?”

Ya tambayi kansa, kamin wani gefe na kwalkwalwarsa ya tuna masa da abun da ya faru..

“Oh...”

Ta tabe baki, ya juya motarsa ya ciro wayarsa number Tarig ya fara kira ta yi ringing har ta yanke be daga ba, a ka'ida baya kiran mutum sau biyu amman haka ya daure ya sake kiransa nan ma be daga ba, ya kira Dawood shi ma be daga ba, then Abdull ma yaki dagawa.

“Me yake faruwa?”

Ya tambayi kansa gabansa na faduwa, zuciyarsa na raya masa ba lafiya ba, domin be saba kiransu gaba daya ace kowa be daga ba, juya akalar motarsa yayi zuwa dayan gurin da suke hutawa, maybe zai samu wani a can, if not sai dai ya wuce gida domin a tsakaninsu babu mai iya zuwa gidan wasu neman wani. Ya isa a sa'a after faka motarsa da minti biyu ya fito ya shiga VIP din dake gurin, part din da suke zama ya nufa tun kamin ya karasa ya hango Abdull da Dawood zaune a gurin with serious face da alama wani abun suke tattaunawa. Kujera yaja ya zauna kamin ya ce komai Dawood ya fara mikewa tsaye Abdull ya bi masa baya suka fice daga gurin suka bar shi zaune da mamaki.

“What this mean?”

Ya tambaye kansa domin ransa be kawo masa komai ba, sai yanzu fushi suke da shi akan abun da ya faru? Or Maleek yayi masa wani sharin a gurinsu?

“It's because of....”

Sai kuma yayi shiru, a ganinsa ko da saboda abun da yayi ma Maleek ne be kamata su shigar da kansu ba, domin a tsakaninsa da Maleek ne, idan ba haka ba miyasa ba su yi ma Maleek haka ba a lokacin da ya watsa masa yawu a fuska? Be tabbatar abun da friends dinsa suka masa ya masa zafi ba sai da ya shiga motarsa yayi mata key, da wani irin karfi ya daki sitiyarin motar yana jin kamar ba a taba bata masa rai irin haka ba, domin be taba samun matsala da friends dinsa da ta kai ya zauna su tashi ba sai a wannan karon and all because of Maleek, bayan fadan da Daddy yayi masa.
  Wayarsa ce ta yi ringing da gangan yaki kallon gefen da wayar take ma balle har ya duba ya ga mai kiran balle kuma ya amsa, har ya isa bakin gate din gidansu be bi ta kan wayar ba, kamar zai tashi gidan haka ya danne horn har sai da Masu gadin gidan suka bude masa gate. Har gaban kofar Momy ya faka motarsa ya fito va tare da ya dauki wayar ba ya karasa gurin kofar falon, yana ganin yadda kanwarsa ta bude masa kofar falon tana jiran shigowarsa ya san wani yakin zai tarar a gidansu. Kallo daya yayi mata ya dauke kai ya shiga ciki, sai ya samu mahaifinsa a tsaye yana jiran shigowarsa. Kamar ya san nemansa Daddy yake sai ya karasa gurinsa ya tsaya ya kasa ce masa komai kamar yadda be yi sallama a farkon shigowarsa falon ba, daman can kuma ba al'adarsa ba ce sai dai ya kan gwada yi wani lokacin idan Daddy na gurin saboda ganin fuskarsa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.