Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 172 of 227
“Amman ita bata so na Daddy”
“Karamar yarinyar ce fa, ina tunanin kamar Safiyya ma zata girma ta, to miye abun mamaki idan tace bata son namiji kamar kai, ita ai bata san so ba, kuma irin sun fi dadin zama domin kai zaka koya mata sonka da kaunarka hankali kwance”
“How Daddy how? Ita bata fahimta tana so na amman na so na aure ba, kuma barin garin zata yi ta fada min, yanzu ma zuwan da na yi na zo ne saboda tace tana son ta musulumta ta hannunna domin ni na koya mata addinin musulumci har ta fahimceshi”
“Wow ka yi abu mai kyau, wannan ma ai first step ne na jefa kaunarka a zuciyarta, baka bukatar fada da wani dan ka burge mace, baka bukatar mace ta tare maka fada dan kasan tana sonka, Saboda ita mace ba a iya mata, zaka iya abun burgewa kuma ita ta ji be mata ba, wata kila ma shi ne silar batawarku, idan tana sonka tana sonka ne ko da kuwa kai kafi kowa zama rago a cikin garinku, idan kuma bata sonka bata sonka ko da ka fi kowa zama gwarzo a garin. Sai dai ta wani bangaren kana bukatar ka yi Gwarjanta saboda ka nunawa duniya kai gwarzo ne, kuma zaka iya a kowane fanni, karka da bata sonka ko tana sonka. Kai da ka maida hankali gurin bi da ita a yadda take so, ka cigaba da dagewa gurin koya mata addinin. Zan yi magana da Imam na Masjid din mu, sai ya fada mana yadda ya kamata mu yi zuwa gobe zamu gabatar da komai”
Ameer ya mike tsaye
“Okay Daddy”
Har ya fara takawa Daddy ya kirashi.
“Ameer”
Sai ya juyo ya kalli Daddy.
“Kai yanzu mai bukata ne a gurin Allah, bachin dare, ba naka ba ne, aikata sabo da duk wani abun da addinin ya haramta ba na mutumen dake nema a gurin Allah ba ne, ka hana kanka bachi ka yi ta fadawa Allah bukatarka ka kai kukanka a gareshi ka fada masa damuwarka, kuma ban ce ka roki Allah ya baka yarinyar ba, aa ka roki Allah ya baka ita idan ita din alheri ce a gareka ka karkarto da hankalinta izuwa gareka, idan kuma babu alheri a zamanku ya yaye maka damuwarta ya musanya maka da wanda ta fita, kuma ya saka maka natsuwar rashinta da kwanciyar hankali, saboda ta fadi bata sonka ko ta nuna karka ya karya maka guiwa, ita mace kamar hawainiya ce mai canja kala, ka ga tsufan Mommy nan ta ku? Da ace ba ni nake aurenta ba zaka iya zuwa da kalamai da hayyala da dake so a gurin namiji kuma ka kwace min ita ta manta da ni idonta ya rufe ta ce sai karamin yaro irinka, saboda haka karka dauki soyayyar mace a banza tun da har ta nuna tana sonka son aurene kawai bata maka, zata fara maka na haihuwa ma soon”
Ameer ya dawo da sauri yana murmushi ya rumgume Daddy.
“I love you Daddy idan ka raye ban san ya rayuwata zata kasance ba”
“Allah ya maka albarka, je ka samu abun da ka ci ka kwanta da wuri saboda ka samu tashi da dare nima zan taya ka, farincikinka shi ne nawa Ameer”
Tun da Ameer yake a duniya be taba jin kaunar Daddy irin na yau ba, domin shi ne ya fahimci damuwarsa kuma ya dauko hanyar magance masa ita. Be samu cin komai ba Before ya kwanta domin tunanin Waira ba ya barin shi jin yunwa haka ma bachi ko kadan kasa yi yayi, shi dai gani yake kamar idan ya runtse zai farka ne ya ga babu kaunar yar kyakkyawar matashiyar budurwa nan a ransa. Kamin lokacin da zai yi tsayuwar daren yayi duk ya kagu, domin ya san Allah ma ji rokon bawansa ne, kuma matukar ya dage kamar yadda Daddy ya fada masa zai samu biya bukata, walau Waira ta kaunace shi fiye da yadda yake sonta, ko kuma Allah ya musayya masa da wanda ta fita alheri a gareshi.
Haka ya saka shi dagewa yayi ta nafila har sai da ya ji ya yi iya yadda zai iya, sannan ya zauna ya bude al'qur'ane yayi ta karatu, daman dai sani da iya karatun Allah akwai shi a tare da shi, sai dai shashanci da bin hanyar shaida ne ya saka a gaba ya saka ya watsar da wadanda kyakkyawa halayyar da Daddy ya dade yana son gani a tare da shi. Kamin ya gabatar da bukatarsa sai da yayi tuba ga Allah ya daukarwa kansa alkawarin ba zai sake komawa a cikin wacan kazantar da ya taba kasancewa ba, ko da kuwa ya rasa Waira, a yanzu ya kai munzalin da zai san daidai da akasin haka. Lokaci yayi da ya kamata ya natsu ya fuskanci rayuwa domin akwai rayuwa akwai mutuwa at least ya kamata ya zama mutumen kirki kamar yadda Daddy da Umminsa da duk wani masoyinsa na gaske yake son gani.
[8/3, 9:50 PM] My S Line: 70
Ya farka da farinciki da nishadin zuciya, ba na wanda ya samu biyan bukata ba, sai irin na wanda ya kusanci Sallah a lokacin da kowa yake bachi, Sallah kuma ta kusantar da shi ga Allah. Kusan wannan a bayyane yake duk wanda yake Sallah dare yana farkawa da farinciki da nishadi ko da bashi ko naira, fa kuma kusanci da yake karawa mutum ga Allah bayan hasken fuska da haiba da Allah ke sakawa bawa a fuskar duk wanda zai kalli mai Sallah dare.
Be tsaya jiran Daddy ko Mommy su fito ba, balle wani breakfast da ba damunsa yayi ba, zuciyarta bata bukatar arba da kowa sai abar kaunarsa Waira, dan haka ya shiga bathroom yayi wanka ya shirya cikin tufafin da suka fi yi masa kyau wato kananan kaya ya sanya turare mai kamshi, daman shi da turare 5&6 ne basa rabuwa da juna. Ya sauko da kuzarinsa ya fita harabar gidan, ko da be da abun fada mata shi dai yana bukatar ganinta, even if zaginshi zata yi ta fada masa magana marar dadi yana son jin duk abun da zai fito bakinta. Har ga Allah ya san yana son Waira irin son na mai fitar da mutun daga hankalinsa, mai saka namiji susucewa ya zama kamar wani soko, ba ita ce mace ta farko da ya fara gani ba, ya je gurare da yawa a duniya, tun yana da kurciyarsa har karatunsa zuwa yanzu da yake zaune a guri daya tare da familynsa amman be ga mace da ta dauke masa hankali ta birkita tunaninsa lokaci daya ba irin Waira. Yana tukin yana tuna duk wani moment na su na farinciki a baya, farkon fara haduwa da ita the way da take nuna farinciki idan suna tare, yadda take dagewa ta nuna ta san shi kuma tana son zama a kusa da shi, yadda yake iya tirsasa ta yi abun da bata so kamar cin abinci da bata saba ci ba, saka mata kaunar addinin musulunci da lurar da ida yadda addinin yake da kyau da gata, duk wannan ta tsaya ta saurareshi kuma ta fahimta ta gamsu, sai soyayyarsa ce kawai ta kasa samun muhallin a zuciyarta. It's because of abun da yayi ma Nimra or saboda abubuwan shaidanci da yayi ta aikatawa abaya ne. Har ya isa gidan aka bude masa gate ya faka motar be samu amsar tambayarsa. A ta inda zai ga windows din Waira ya faka yana hw spend time yana kallon gurin ji yake kanar zata leko tace masa Ameer darling good morning. Ya sauke ajiyar zuciya ya fi a kirga sannan ya bude ya fito daga cikin motar praying for her ya fara arba a idan idan ya shiga falon, sai dai hakan be saka hakonsa ya cin ma ruwa ba, domin ya shiga falon ya tararda Ummi da Maleek Mahmood Namra har ma da Abiey suna karyawa Waira bata tare da su, kamar wanda aka sarewa jiki haka ya shiga falon kallo daya zaka masa ka san ba su yake son gani ba, domin yawo yake da idonsa a inda ya san tana yawan zama ko zai ganta. Har yayi rabin falon sai kuma ya juya zai fita.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.