Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 139 of 227

Ya yi murmushi, sam be taba tunanin Teema ta lura da abun da be san ma yana yi ba.

“Kuma tana da kyau, da irin wayewar da nake tunanin idan mace bata yi ba, kamar ba zaka yarda ka kulata, kalli yadda ta shigo rigarta kadan ta wuce knees, bata rufe kai wata kila saboda yawan gashin kanta, ga ta fara har farinta ya fi naka kyau, idonta irin mai kyaun nan ne, bakinta da hancinta iya ita”

A karo na yi yayi murmushi yana kara bawa kansa abun da ya kusa zame masa dole, wato kallon Waira.

“Komai kin canka daidai, amman ba girlfriend dita ba ce, rashin saja mayafi kuma ya samo asali ne saboda addinita da al'adarta, ita din ba musulma ba ce”

Teema ta sauke wayar hannunta ya kara kallon Waira da mamaki.

“Ikon Allah kiristace?”

“Ban san wane kalar addini take ba tukuna, amman dai zan sani soon”

“Gaskiya da zan baka shawara ka dauka, zan ce karka bari wannan ta wuce ka, domin ta hada komai da duk wani namiji zai gani ya ji yana sonta, sai idan namijin nan wani kala ne mai neman wani abun dabam a jikin mace ba wannan ba, kuma zaku yi matukar dacewa da juna, yayanku za su yi kyau”

Yayi murmushi ya mike tsaye still yana kallon Waira kamar zai cinyeta.

“Waira na barki a nan naje na dawo?”

Ta fisge kanta ta mike tsaye da sauri tana girgiza masa kai alamar aa.

“Okay saka ribbon dinki mu tafi yanzu”

Ta dauki ribbon din ta saka sai gashin ya hade guri.

“Ba zaka barta har ka dawo anjima ba?”

“Ba nan zan kwana ba yau”

“Amman ai dare yayi already”

“Yeah gida zamu tafi”

“Idan kun ci abinci ko? ”

Mummy ta tari numfashinsa tana aje kulolin abinci dinning.

“Bata cin irin abun da muke ci, tea kawai take sha sai cake ko biscuits”

Waira ta daga masa kai tana murnushin jindadin be manta abun da ta fada masa tana ci ba.

“Akwai cake ai, zan dumama mata”

Mummy ta fada ita ma tana yi ma Waira kallon budurwar Ameer ne dan haka so take ta kyautata mata saboda shi. Fiyya ta ware hannayenta tana fadin.

“Mummy ina da cake dazun da Ya Ya aje ni gurin birthday Ikram ta raba mana cake da zamu dawo gida”

“Toh dauko mata ta ci bari na hada mata tea, zo nan ki zauna yata”

Mummy ta mika mata hannu, sai ta kalli Ameer har sai da yayi mata umarni da ta tafi sannan ta isa gurin Mummy, Mummy taja mata kujera ta zauna ta zauna.

“To kai Malam ka zo ka zauna, zata fi sakewa da jindadi”

Ba musu Ameer ya iso gurin ya ja kujera ya zauna.

“Mummy ba abun da kike tunani ba ne, not yet”

“Ni ka ji na ce wani abu? Ko kuma ka shiga zuciyata ka ga ina wani tunanin ne?”

Mummy ta fada da murmushi a fuskarta sannan ta juya ta shiga Kitchen. Ameer ya dauki plate ya zuba abinci ya saka spoon, ya dauki cup ta zuba lemu ya zuba ruwa. Ya fara cin abinci kenan Mummy ta fito da ruwan zafi a cup ta aje a gaban Waira.

“Teema tashi ki dauko mata kayan tea ta hada da kanta ban san wane kalar tea take so ba kar na mata ba daidai ba”

Fiyyata nufo gurin da zimmar zama Mummy ta yi mata alama da aa da ido, sai kawai ta zarce kitchen ta dauko plate ta zo dinning din ta zuba abincinta ta nufi hanyar dakin baki dake kasan benen, Teema ma tana gama jera mata kayan tea ta shige ita da Mummy aka bar Ameer daga shi sai Waira. Da kansa ya mike tsaye ya fara hada mata tea yana tambayarta me da me zai zuba, sai ta nuna masa idan ta shimshina ta ji kamshi be yi ba sai ta ce ya kara.

“Ba a shinshina abinci ba kyau”

“Saboda me?”

“Saboda zaki sakawa kanki cuta ne kawai, abun da za'a ci ba a shinshinawa, kuma ba a hurawa musulumci ya hana”

“Me yasa ake hana ku abubuwa da yawa? Haka Ummi take cewa ba a cin abinci da hagu”

“Yes duk wani abun da zai cutar da mutum addinin mu yana hana mu aikata shi, idan kuma kika ji ance ka aikata to a cikin aikatawar akwai lada da karin kariya ko lafiya da kuma natsuwa”

“Minene lada kuma”

Yayi murmushi ya koma mazauninsa ya zauna ya fara cin abincin.

“Lada wani abu ne da ba a gani a ido, amman ana iya fadarsa kuma wani abun kana ganin ribarsa tun a duniya, bari na baki misali da karatun da kike yi, idan kuka yi assignment ko test ba ana baku maki ba?”

Ta daga kai.

“Kina ganin makin?”

Ta girgiza kai.

“Amman da makin ake auna abun da kuka yi mai kyau ko? Kuma a soke inda kuka yi ba daidai ba, a gyara musu wani gurin ko kuma a nuna muku yadda ake yi right?”

Ta daga kai cike da gamsuwa.

“Toh haka yake ko a gurin Allah, yana saka mala'ikonsa su auna ayukan da mutum yake na lada, idan ya aikata alheri kuma yayi da yawa, sai Allah ya saka masa da aljanna, kuma tun a duniya Allah zai masa gata har zuwa kiyama”

Kalmar kiyama, da Lada da kuma aljanna a gurin Ameer ta fara jinsa, kuma kalmomin sun daure mata kai, bata san ma'anarsu ba.

“Minene Aljanna? Da Kiyama?”

Ya kai spoon din abinci a bakinsa, sannan ya sake debowa ya kai saitin bakin Waira, ta kalli abinci sai ta matsa da kanta baya.

“Ni ban taba ci ba”

“Toh ki gwada mana, akwai dadi sosai it's high time ace baki fara dandana abincin garinmu ba, ya kamata ki iya ci saboda zaki cigaba da zama da mu ne fa, ni idan na je garinku ba zan kyamace kalar na ku abincin ba, zan ci komai aka ba ni”

Ta yi dariya.

“Ba zaka iya zuwa garinmu ba ai”

“Zan iya, kuma zan je na miki wannan alkawarin, zan je tare da ke ko kuma ni kadai, zan roki su yafe miki kuma su barki ki zauna a tare da mu”

A take yanayin fuskarta ya sauya.

“Za su iya kasheka”

Yayi murmushi ya kara matsar da spoon din bakinta.

“Bude baki”

Ta bude kadan sai ya saka hannunsa ya bude mata bakin ya zuba mata abincin a hankali.

“Tauna”

Ta fara taunawa tana yamutsa fuska, domin duk abun da baka saba da shi ba, zaka ji shi babu dadi kamin ka saba.

“Zan iya yin amai”

“No ba zaki yi ba”

Taunawa take tana jin zakin abincin har cikin kanta yana sarrafa kwakwalwarta.

“Bari mu koma gurin tambayar da kika min, kin ce minene kiyama da aljanna ko? Kiyama wani guri ne da Allah yake tara dukannin bayinsa musulmai da kafirar, bayan sun mutu sai ya sake tayar da su, su yi tsayuwa na jiran sakamakon abun da suka aikata kamin ganin makoma, kusan zan iya c miki guri ne na interview idan aka ga aikinka na kwarai ne za a baka sakamakon abun da ka aikata, idan kuma ka yi mummuna nan ma za a baka sakamakonka, sannan a tura yan wuta cikin wuta, yan Aljanna kuma cikin aljanna, kuma akwai wadanda sai an konasu a wuta sannan za a saka su a Aljanna. Aljanna ma wani guri ne da ya ninka duniya dadi da kyau da farinciki, akwai gulbin zuma da na giya da na madara, duk wani abun da kike so akwai a Aljanna, talaka a aljanna shi ne wanda yake da gida kamar girman duniyar nan”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.