Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 138 of 227

“Me yasa muka tsaya a nan?”

Ta tambaya a cikin wani yanayi mai kama da shagwaba da bata ma san tana yi ba. a juyo a hankali ya kalleta.

“Kuka na ga kina yi, shiyasa na tsaya har ki gama kukan, idan kuma bakin zon zuwa ne sai na maida ke, ni ban shirya tarbar wani karin bakincikin akan wanda nake ciki ba, bana son kukan kowa akaina a yanzu”

“Ba saboda kai nake kuka ba”

“Saboda wa?”

Ta yi shiru, sai ya kai hannu ya riko fuskarta ya juyo da ita yadda zata fuskance shi da kyau.

“Waira saboda na katse miki sarka ne? Ko saboda na yi magana da Maleek”

“Duka ne, ina son abun da Sulem ya ba ni, kuma ni bana son kana fada da Ya Maleek bana so ko kadan”

“Amman kina kallo a gaban idonki, shi ya fara fada min maganar banza, and ni bani da wani kuduri na lalataki ko rayuwarki, Allah ya sani ba ni da wani mummunar manufa akanki”

“Minene mummunar manufa?”

Ya kawar da kai.

“Manta kawai”

Sai kuma ya juyo ya kalleta.

“Zoben ki kuma zan siya miki wani bana son an sake ganinki da duk wani abun da ya shafi wani, bana son wata mu'amala tsakaninki da kowa, ba saboda Ummi kawai na dawo gidan nan ba, har saboda ke, so please don disappointed me”

Ita dai kallonsa kawai take ba dan ta fahimci mnufar zancensa ba.

“Amman Sulem shi ba a gidan yake ba, sau biyu kawai ya taba zuwa, kuma ya ba ni kyauta ne”

“Miye alakarki da shi?”

Ta yi shiru tana murza yatsun hannunta, so take ta tuna alakar dake tsakaninsa da ita.

“Shi ne wanda yake min sauki lokacin da ka barni a daji nan, shi yana so na baya min kamar yadda sauran mutanen suke min ba, kuma yana lalabani yana ba ni abubuwa kuma yana min magana mai dadi”

Ya sauke numfashi tare da kai hannu ya kunna motar.

“Ba dan'uwanki ba ne, baki da alaka da shi, Waira baki da alaka da kowa a yanzu sai ni”

“Kai ma ba dan'uwana ba ne!”

A wani irin dum maganar ta fado masa a kune ta fara rawa a kirjinsa. Ya dan karkato kamar zai kalleta sai kuma ya fasa ya cigaba da tukin motar.

“Ni ina son Sulem, Sulem ba ya min fada”

“Miye abun fada a cikin magana ta? Gaskiya na fada ai, waye silar zuwanki garin nan ba ni ba?”

“Amman ai a daji ka bar ni, baka taimaka min ba lokacin da maciji ya cije ni”

“That's was my mistakes, amman na taimake ki mana, na dauko ki saka ki a motar Nimra”

“Baka yi ba, Sulem ne yayi?”

“To a ina kika ga Sulem din?”

“Ni ban sani ba, amman shi na gani a gidan Hospital kuma shi ne yake min da sauki ba kamar saura ba”

“Shi fa likita ne kawai, amman ba shi yaje daji ya dauko ki ba, ke dai kawai kin farka kin ganki a asibiti ne, ya taimake ki ne saboda an ba shi kudi ba free yayi miki ba?”

“Ba a bashi kudi ba”

“Waya fada miki?”

“Na gani ai, babu wanda ya bashi kudi, kuma da iyayensa suka masa fada sai ya dauke ni ya kai ji wani gurin muka kwana a can, be bar ni ni kadai ba, kuma da masu bakin kaya police aka ce su kawo ni a nan be min fada ba, ni ina son shi”

Ya daki sitiyarin motar da karfi

“Haba Waira ina da fushi sosai, karki saka raina ya bace mana, don't make me angry, kar na fadi wata maganar da zata saka ranki ya bace har Maleek ya yi kwatance da haka”

“Toh ka daina min fada, gashi ka daki mota next ni zaka daka kamar Ya Maleek”

Ya amsa da sauri.

“God forbid ni ba zan taba dukanki ba, ba wannan ranar fada kuma na daina, zan siya miki sarka mai tsada sosai ki saka a wuyanki ba zobe ba, ba a saka zobe a wuya”

“Ni Sulem ya saka min ina so”

“Wannan Sulem din dan'iska ne”

Sai ta ji kamar ta fashe da kuka saboda ya zagi Sulem, ita duk mutanen da take kauna bata son a taɓa su.

‘Idan mutum yana kyautata miki shikenan ya zama masoyinki? Zan rufe idonki da kyautata har sai kin manta kowa a rayuwarki’

Ya saka a ransa sannan ya kalleta yana murmushin ya ce

“Yi hakuri, Sulem mutumen kirki ne, yanzu idan mun koma saka miki zobenki a wuya shikenan?”

Ta daga masa kai.

“Okay Smile”

Ta yi murmushin kadan, hakan kuma sai ya saukar masa da farinciki duk wani bacin rai da yake ya ji kamar an yaye masa shi
[7/17, 6:23 PM] My S Line: 56

Daddy yayi murmushi bayan ya gama sauraren hukuncin da Ameer ya yanke na zama a gidan Ummi for some days.

“Ka yi tunani mai kyau, kuma a yanzu na yarda ina ɗa mai hankali da sanin ya kamata, Allah ya maka albarka”

“Ameen”

Ya amsa sannan ya aje jaridar dake hannunsa ya mike tsaye.

“Idan dai akwai wani taimako da kake bukata zaka iya fada min”

Ya juyo ya kalli Daddy.

“Okay thank you Daddy”

“Your Welcome”

Daddy ya amsa masa da murmushi sannan ya  daga masa hannu. Ameer ma murmushin yayi ya juya  ya fice daga dakin. Falon Mummy ya shigo ga mamakin Waira ya samu zaune a kasa ta baje gashinta Fiyya na mata kitso kamar ba ita ba, Teema zai dariyarsu take, domin Waira son kitson take a gasken gasken, Fiyya kuma yawan gashin Waira ne ke burgeta yadda ya sha gyara ya sauko har gadon bayanta.

“Fiyya me kike”

“Kitso nake mata”

Murmushi yayi domin ya san shirme kawai za a tabka, Fiyya bata iya komai ba kawai dai tana son taba gashin ne. Ya zauna a kujerar dake fuskarta Waira ya kura mata ido ko kyabtawa babu, shi dai kam kallonta yana masa kyau matuka, ba ma kamar a yanzu da take ta far'ah kamar wani kitson arziki za'ayi mata.

“Is she your new girlfriend”

Ya dan juyo ya kalli Teema sai kuma ya juya ya kalli Waira da bata ma san ana yi ba, sai murmushi take tana taba gafen gashin da Fiyya take murdawa da sunan kitso, a rayuwarta ba a taba yi mata kitso ba, bata ma san wani abu kitso ba sai a kan su Ummi, abun ya burgeta amman bata taba sha'awar gwadawa a kanta ba, Ummi kuma bata damu da tace ayi mata ba, lura da yawan gashinta ba kowa zai iya mata kitso ba, kuma ba lallai ne ta yarda ba, domin zai iya mata zafi saboda abu ne da ba'a taba yi ba. Hakan ya saka ta maida hankali gurin gyara mata gashin kawai ba tare da kitsawa ba.

“Me ya saka ki tunanin budurwa ta ce”

Ya fada bayan ya dauke idonsa daga kallon da baya gundirarshi.

“Baka taba zuwa da wata mace a gidan nan ba, baka taba gabatar mana da wata ba, amman wannan kana shigowa sai ka cewa Mummy ga Waira suka gaisa, baka jira wani ya bata abinci ko abin sha ba, da kanka ka dauko mata lemu, ka nuna mata gurin da zata zauna, har kana fadar ta saki jikinta nan din ma gidansu ne”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.