Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 190 of 227

“Duk wata azabtarwa da wahala da na jurewa sha a gurinku, tsawon lokacin da Waira ta dauka bata kusa, na jure ne saboda ina sonta ban taba fadawa kowa wannan maganar ba amman zan fade ta a cikin fadar nan, na san kowa ya lura da hakan, na raine ta tun tana karama har ta fara wayo, rana daya kuma sai wani ya dauke min ita?”

Wani daga cikin manyan masarauta da suke gurin ya mike tsaye ya isa gurin da Eid yake tsaye ya dafa shi.

“Kwantar da hankalinka Jarumi na, akwai mata da yawa a cikin garinmu da suke sonka, akwai matan da suka fi Waira kyau da komai ciki da wajen masarautar nan, ka rufe idonka daga ganin Waira ka bude idonka a garesu cikin kankanen lokaci za a gama da su, karka yarda zuciya ta deba ka gujewa umarnin masarautar nan, domin wannan matashin ba zai yarda ya barka maka Waira ba, ko da kuwa ka yarda ka koma cikin kalar tsafinsa ne, idan kuma muka hana masa ita zai iya gwada jayayya da mu”

“Toh a bar mu mu kara mana, sai a gane waye jarumi”

Ya fada da kakkausar murya yana tabe baki kamar zai yagashi.

“Ba mu taba gwada yaki ba, kuma ba zamu gwada saboda wata korariya a garinmu ba, ban yi tunanin karfin tsafi zai yi tasiri a gareshi ba, ko da ya ce ba zai aureta ba, ba samu yarda ta aura daga garemu ba wannan shine magana ta karshe”

Eid da duk sauran mutanen da suke fadar suka risnar da kai domin nuna biyayya ga Umarnin Sarkin da ba a musawa. Eid ya dago yana kallon Maleek fuska kamar an aiko masa da mutuwa, zuciya kamar bakin maciji dake cike da dafi, ya fice daga fadar yana hararar Maleek yana huci kamar zai fitar da hayaki. Duk wani abun da ake fada Maleek be ji ba, domin da yarensu suke maganar, Waira kuma jinta da ganinta tunaninta mamakinta zuciyarta da ruhinta gaba daya sun tafi gurin mutumen da take kira da yayanta wato Ya Maleek. Furucinsa na cewa yana son aurenta da jarumtar da ya nuna akanta sadaukarwa neman kareta sassauta ra'ayinsa da nema mata farinciki da yanci wani abu da ya kai ta rubuta a dutsen da ba goge zane da alkalamin zinari. Hawaye take irin hawayen da ba zata iya fadar na minene ba a yanzu, na farincikin abun da Maleek yayi mata ne ko kuma na samun yancinta ko kuma na komawa da zata yi gurin matar da ta zame mata uwa? Ko kuma dai na fasa kasheta da aka yi ne? Wata kila kuma na tsafin da suka ce sun yi ta aikawa Maleek ne be same shi ba.

“Nuwaira...”

Kamar wadda aka jefowa numfashi daga sama haka ta zabura ta dawo hayyacinta, sai ta lumshe ido tana jin ba a taba kiran sunanta da dadi kamar yadda Maleek ya kirata a yau ba. Rufe idon da ta yi sai ya saka shi tunanin ko bata ra'ayi ne musamman ma da yayi arba da hawayen dake zuba a idonta gashi tun da ya furta maganar take kallonsa ta kasa cewa komai kuma ta kasa dauke idonta daga gareshi.

“Ko baki so ne? Karki damu, na yi hakan ne saboda na sama miki hanyar fita daga garin nan, idan sun amince sun ba ni aurenki da zarar mun fita ba aurenki zan yi ba, za a miki aure ne best on zabinki”

Rashin Eid a fadar da zai iya fassara musu abun da Maleek yake fada, ya saka Sarkin amfanin da nasa baiwar ta tsafi ya yi communicating da aljannunsa suka fassara masa abun da Maleek ya fada, hakan kuma ba karamin dadi yayi masa, domin ya fahimci Maleek ba gaske yake son Waira ba, hakan na nufin zai fara mata yi mata butulci da zarar sun bar garin kenan, kuma hakan ya nuna Waira bata son shi, a kokarin Sarki na bakanta musu ya kalli na hannun damansa ya ce.

“A fadawa Dardu ya tada busa ya hura wuta, mata su fara nika ganyen za a daura aurensu a yanzu”

Nuwaira ta bude ido da sauri ta kalli Sarki domin daga ita sai jama'ar garin suka iya jin abun da Sarki yake fada ban da Maleek. Sarki ya kalleta yana tana tauna hakora ya ce.

“Zamu aura miki shi, kuma zamu cire duk wani tsafi da kariya ta mu da take jikinki yanzu nan, kuma duk wani abun da zai faru ko ya biyo baya karki neme mu, babu mu babu ke da zuri'arki”

Kasa cewa komai ta yi sai har lokacin hawayen ba su daina sauko mata ba. [8/9, 8:09 PM] 🦋-🦋: 74

“Ki fada masa ya cire kansa daga lamarinki in ba haka ba zai yi nadama”

Maleek yake nunawa amman da Nuwaira yake magana da yaren garinsu.

“Ba zaka cutar da shi ba Eid kai dan'uwa ne a gurina, mai matukar son abun da nake kauna, mai son abun da nake so, mai gudun bacin raina da kukana? Meya same ka ka canja? Kalamanka da kamanin da nake gani a fuskarka ba su ne na Eid da na tafi na bari ba, wannan mutumen shi da iyayensa tarbe ni, sun saka hannu biyu sun rumgume ni, ba dan sun san daga inda na fito ba sai dan karamci da sanin ya kamata irin na su, sun nuna min kauna, a gurinsu na san abun da ake kira da tsabta da kauna da soyayya, a gurinsu na san me iyali yake nufi, a lokacin da zuwa gida ya kama ni, suka sako ni a mota suka rokoni har kofar garinmu akan me kake tunanin idan ka nuna masa tsaya zan ji dadi? A wane hali zan bari ka cutar da shi? Da wace Hujja zaka zabe ni ka bar shi?”

Eid ya dauke hannunsa yana kallon Nuwaira dake magana taba zubar da hawaye. Ta sauke kanta kasa ta kalli hannun Maleek dake rike da nata, sannan ta kalleshi.

“A nan garinmu ne Ya Maleek zan rayu cikin aminci da yardar Ubangijin Kaaba”

“Hakan ba zai gamsar da ni ba Nuwaira, sai na ga halin da zaki kasance kuma sai na yi magana da Sarkinku”

Cikin wata kalar murya mai kamar ta zaki Eid ya zabuwa Maleek har jijiyoyin dake jikinsa suna bayyana.

“Waye kai da zaka ce zaka ga sarki? Mutanen dake cikin fadar sarkin mu ba baka isa ka gani ba balle Sarkin da kansa, duk wani abun da ka yi ma Nuwaira kai da iyalinka mun gode zaka iya tafiya”

Eid ya hade hannun biyu yayi masa godiya har da sirinawa sannan ya nuna masa hanyar da suka fito.

“Ban taba tirjiya ko musayar yawu da kafewa akan abu daya ba sai yau, idan da tsafi kuke taka ni ina takama da wanda yake da ikon akan komai da kowa, and mark my words sai na yi magana da Sarkinku zan tafi sai na tabbatar Nuwaira tana cikin aminci, idan har zan iya barin wani abu ya same ni to zan iya barin Nuwaira ta cutu kenan”

Sai a lokacin yan rakisarsa suka saka baki domin sun lura a yanzu ya wuce gona da iri, su dai rakiya suka zo kuma sun kawo yarinyar a gidansu akan wace hujja zai nace dole sai ya shiga cikin garin.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.