Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 30 of 227
Be yi unkurin yi mata komai ba har sai da ta suma, sannan yaja tsaki wata zuciyar na raya masa ya koma ya duba halin da mahaifinsa yake ciki, ba mamaki gaskiya Nimra take fada masa ya san yadda mahaifinsa yake sonsa idan aka ce wani abu ya same mahaifinsa be kamata ya musa ba, domin korar da yayi masa zata iya taba shi. Idan har akwai abun da Ameer yake kauna a duniya to yana a bayan Mahaifinsa ne, sai dai gata da tarin arzikin da ake sakar masa ya saka baya iya tsayar da fushinsa ko da kuwa a gurin mahaifinsa ne. Wani tunanin ne ya zo masa a take ya juya ya nufi inda carpet dinsa da ya shimfida yake ya cire rigar jikinsa ya nade hannunsa sannan ya janyo carpet din har cikin ciyayin da Waira take kwance wani kumfa ya zubo ta gefen bakinta dake bude. Kafasar ya saka ya rika turara ganin ba zai samu abun da yake so ba a dole ya saka hannunsa daya nade ya daga ta ya dora yana ta wani kyankyami, a cikin carpet din ya hade ta kamar wata gawa yana ta tofar da yawu, cikinsa sai wani kuka yake saboda kazantar da yake ji numfashinsa jin yayi kamar ya canja. Fita yayi a gurin ya taka har gurin motarsa yana kara waige waige ko Allah zai saka ya samu wanda zai bawa ita ko kuma ya taimaka masa ya saka mata ita mota, domin shi dai be jin zai iya taba wannan uban dattin duniyar dake jikinta even though ya nadeta a carpet da yake da tabbacin idan ya isa gida sai ya wanke hannunsa ya fi a kirga. Ganin kamar zai bata lokaci ya guri ya saka shi juyawa ya koma a samu gafen rigar dake nade a dayan hannunsa ya nade dayan ya dauketa yana kawar da fuska, gurin motar Nimra ya nufa, a dole sai da ya aje ta sannan ya bude bayan motar ya saka.
“This one is for you Nimra ina fatar yarinyar ta mutu”
Har wani daga gira daya yake, ko kadan baya jin komai a jikinsa sai ketar da yake ta sakawa, jefar da rigar hannunsa yayi ya bude motar ya shiga be saka kafafuwansa ba sai da ya cire talkamin kafarsa ya shiga motar haka, daga shi sai wando jean jikinsa ba riga sai farar fatar jikinsa da kuma mazanta dake kara fitar da zatin fuskarsa. Kunna motar yayi at first sai ta tashi sai da ya yunkura zai yi reverse sai ta tsaya, ya sake kunna ta mutu ya sake kunna ta sake mutuwa har sau hudu, jimmm yayi yana tunanin yadda rayuwa zata kasance masa idan motar nan bata tashi ba, ba zai yi mamaki ba idan ta ki tashi domin ya ci uban motar, yadda ya rika buga motar da icen dake gurin sai da gabanta ya lankwashe, abun da be saba ba sai gashi yana addu'a da fatan Allah yasa ta tashi. And he got lucky motar ta tashi abun yayi hamdala ga Allah sai gashi yana fito ya juya kanta da karfi ya koma hanyar da shigo da motar yana gudu sosai kamar an biyo shi. Babu inda ya nufa sai hanyar da zata sada shi da Abuja, tunanin yadda zai yi idan police ko sojoji suka tare shi a hanya be zo masa ba sai yanzu.
EID POV.
Yana tsaye bakin kofar dakin da Waira take yana kallon cikin dakinta dake hargitse, he felt very bad domin shi ne silar guduwarta a garin, guduwar da bashi da tabbacin Sarki zai yafe mata ko kuma ya kasheta kamar yadda ya alkawaranta.
“Waira duk saboda kar ki yi kewa babu ranar da bana kasancewa tare da ke, miyasa zaki tsorata har haka? Akan me zaki karya dokar dake nufin rayuwarki?”
Ya kai hannu ya taba kofar dakin, kamin ya sulale kasa ya zauna a hankali, tun da ta tafi kullum a gurin yake zama, idan baya dakinta to yana a gurin da ta saba zama ta ci yayan itatuwa, ko kadan baya son yayi tsafi ya ga halin da take ciki domin zuciya zata iya debarsa ya bi bayanta bayan kuma Sarki ya kafa masa doka tun a ranar da ta gudu cewar kar ya bi bayanta. Ya daurewa zuciyarsa ya bi Umarni Sarki na iya yanzu da zuciyarsa zata iya dauka, kamin ya shawo kan Sarki ya sassauta hukuncin da zartarwa Waira tun gabanin ya san zata gudu. Wani irin azaba ya ji hannunsa na yi kamar an jefa shi a ruwan zafi, an cire na kara a wuta, da sauri ya saka dayan hannunsa ya rike dayan da yayi masa mugun nauyi dafin na shiga har wuce iya inda zugin yake. Iyakar juriya yayi amman sai da ya kai kwance yana dafe da hannu tsabar azabar da ya ji hannun na masa, yanayin yadda gurin ke masa zafi dafin na masa yawo ya gane cewar maciji ne ya cizi Waira, mikewa yayi tsaye rike da hannu ya daga kansa sama ya lumtse ido. Sai ga wahala masu zafi sun sauko masa, ba Hawaye ne na kukan zafin da yake ji ba na cizon maciji ba, hawayen tausayin Waira yake a wane hali take ciki? Ta ina maciji ya cijeta? Daman tun da ta gudu babu ranar da ba ya tunanin halin da take ciki da kuma abun da zata ci, ko a ina ta boya, duk be sani ba kuma bashi bukatar ya sani a yanzu.
“Waira”
Ya fada yana jin azabar tana karuwa, har yawun bakinsa sun soma canjawa, gumin azaba da wahala na karyo masa a goshi har ya rasa inda zai saka kanshi. Lokaci daya kuma sai ya ji azabar ta dauke masa.
©KhadeejaCandy
©®Copyright
2023
_©Khadeeja Candy_
1️⃣3️⃣
Wani sabon tunanin ne ya zo masa hakan ya saka shi canja shawara, gefen hanya ya rika bi har ya samu wani Karamin shagon siyar da kaya, wani almajiri ya samu ya aika shi kiran mai shagon kasancewar akwai glass sai an bude za a shiga, ba shigar ce matsala ba rashin talkami da kuma rigar jikinsa ce matsala domin baya son ayi masa kallon mahaukaci. Almajirin na isa sai gaai shagon ya fito ya biyo bayansa. Tun kan ya isa Ameer ke masa kallon kasa da sama.
“Riga nake so wacce ta fi ko wace tsada, sai talkami idan kuna da su”
Shi ne abun da ya fada ya mika masa Atm din hannunsa tare da fada masa code.
“Akwai amman ba mu da machine din cire kudin, sai dai makocina shi kuma sai ya cire carjin dinshi”
“Ba matsala”
Ya fada ba tare da ya kalleshi ba, domin mutane kazanta suke ba shi a yanzu, Waira ma dake bayan motar jin yake kamar tana saman jikinta ne, kazantar dake jikinta ta lake masa a zuciya ya kasa manta abun da ya gani. Yana ji yana gani ya bata minti talatin a gurin kamin mutumen dake shakar Ameer ya kawo masa rigar da talkamin, domin jikinsa na bashi ba Ameer ba mutumen kwarai ba ne ganin sabuwar mota da aka buge gabanta gashi babu riga a jikinsa kuma babu talkami hakan na nuna sato motar yayi ko kuma wani abun dabam. Kallo daya Ameer yayi ma rigar da talkamin ya san ba ajinsa ba ne, sai dai babu yadda zai yi dole ya saka a haka, sai da yayi tsaki sannan ya karba tare da ATM din, a gaban mutumen ya saka rigar sannan ya ja motar yayi gaba, tafiya mai nisa yayi sannan ya saka talkamin ya faka motar gafen titi ya fita zuwa gurin wani mai shagon POS ya mika masa ATM din.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.