Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 49 of 227
“Are you okay?”
“I hope so”
Ya amsa yana kallon harabar gidan, Maleek ya cigaba da danna wayarsa.
“Tunani nake yadda rayuwa zata zama idan babu Ummi”
Mahmood ya fada ba tare da ya kalli inda Maleek yake zaune ba. Cak Maleek ya tsayar da taba wayar ya dago kalli Mahmood.
“Baka da hankali? How could you say that? Kasan abun da ake nufi da babu Mahmood? Rasa ta fa kenan mutuwa, ta ya zaka fadin irin wannan maganar?”
Mahmoud yayi murmushi yana kallon Maleek, da ya mike tsaye rai a bace.
“Wannan ranar ba zata zo ba Mahmood idan kuma ta zo to ba zata same ni da rayuwa ba, ban taba mafarkin rana zata zo da zan saka kafata a cikin gidan nan ace Ummi bata nan ba, ban san me ya zo kanka ba ya kamata ka yake shi ka nemi tsarin shaidan daga wannan mummunan tunani naka i hate nonsense”
Ta zazzaga masa magana sannan ya saka kafarsa sai fice daga gurin sai kuma ya juyo ya kalleshi.
“Ko wani abu kanji Mahmood?”
“No ban ji wani abu ba, kawai zuwan yarinyar nan ne ya ba ni tausayi ta rabu da iyayenta, ya saka ni tunanin mu idan muka rasa Ummi ya zamu ji irin yadda muka saba da ita?”
“Ku da kuka saba da ita kenan, ya kake tunanin ni da ka kasa kebewa da ita ko da tsawon awa daya ne? Balle har na raba jikinta na rumgume ta a matsayin uwata? Baka tunanin ina jin zafin haka Mahmood? Mi yasa zaka min irin wannan maganar? Why?”
Ya karshe maganar muryarsa na karkarwa irin na wanda rauni da bakinciki ya dade a zuciyarsa.
“Bana nufin bata maka rai...”
Fuuu ya fice daga gurin be tsaya sauraren abun da Mahmood zai fada ba, baya jin komawa ya cikin gidan hakan ya saka shi nufar Katon Garden din dake gidan, Garden da aka kawata da itatuwa da fulawoyi ta ko'ina ta bangare daya kuma an yi Swimming Pool, an jera kujeru a kusa da gurin, ta dayan gefen dama kuma kebantattun tsuntsaye ne da aka yi musu muhalli na dabam, sai barewar dake ta kiwonta a gurin wani decoration na busashen itace. A hankali yake takawa har ya isa gurin da tsuntsayen suke ya bude yar wayar da aka kewasu da ita ya shiga cikin garden din, guri ya samu a gurin kujerun nan da ake na siminti ya zauna yana kallon yadda wasu suke tashi wasu na sauka. Wayarsa dake hannunsa ya bude Gallary ya shiga can wani gurin ajiyar sirrin ya kamo hoton mahaifiyarsa inda take zaune tare da Abiey aka yi musu hoto Tan murmushi har koranta sun bayyana. Yatsansa yakai ya shafa saitin inda take a jikin hoto yana jin wani launi marar dadi na masa yawo a zuciya. Shi ne kadai abun da yake iya, ya kalli hotonta ko ya shafa amman a fili ba zai iya zama yayi shawara ko hira da ita ba, ba zai iya kai hannu ya taba taba jikinta a matsayinta na mahaifinyarsa ba, ba zai iya kebewa daga ita sai shi na tsawon awa daya ba, tun da yayi wayo ya mallaki hankalin kansa be san wata rana da haka ta taba faruwa a tsakaninsu ba, sai dai duk da haka Ummi bata taba juya masa baya ba, bata taba jin ta tsana shi ba, tana kokarin ganin ta ja shi a jikin sai ta ga hakan ya gagara sannan ya saka masa ido ta daina kokarin kebewa da shi a cilas ko taba shi, sai ma taimaka masa da take na yadda zai rayu ba tare da yan'uwansa sun shiga rayuwarsa sun bata masa rai kamar yadda baya bukata ba.
Shi dai ya san ba tsanar mahaifiyarsa yayi ba, domin bata yi masa abun da zai saka ya tsane ta ba, idan ma ta yi masa dole ya so ta saboda ita din uwa ce, balle kuma bata yi ba, sai dai ya tsabarsa da mata ne ya saka ita din yake kaurace mata saboda ita ma tana daya daga cikin jinsin matan. To miyasa ya tsani matan? Why? Shi kasan ba zai iya fada ba, be yi soyayya ba balle yace yaudararsa akai yi, be zauna da matar uba ba balle yace ta cucheshi. Sai da aka kira Sallah magariba sannan fito daga gurin, a harabar gidan ya hadu da Ummi ta nufo Garden tana kallonsa.
“Mahmood yace min kana Garden tun dazu gashi Magariba ta yi baka san iya abin da zai sauko ba”
Cike da kulawa irin ta uwa take masa magana, lafiyarsa ce abar damuwarta a yanzu. Ya dan dauke kai daga barin kallonta ya kalli kasa.
“Ina taba waya ne ban ankaro lokaci yayi ba sai da na ji kira, bari na je na yi alwala”
Ya amsata yana tafiya sai ta juyo ta biyo bayansa domin inda sabo ta saba da halinsa. Yana gaba tana bayansa har suka shiga falon kai tsaye ya nufi Upstairs ita ma stairs din ta nufa domin gabatar da nata alwalan, daf da zai wuce dakin da Waira take ciki ya shiga nasa dakin sai gata ta fito da gudu daga dakin da yake bude kicibis suka yi da Maleek bata tsaya komai ba ta rumgume shi ta rike da mugun karfi.....
Duk wani abu mai rai da motsi a cikin jikinsa sai da ya tsaya cak, ciki har da bugun zuciyarsa da numfashinsa.
Ummi ta rufe baki daga bayansa da take tsaye domin ta ga abun da ya faru, Nimra da ta biyo bayanta da gudu ma ta tsaya cak ta zaro ido. Shisshikar kuka kawai Waira take tana kara rike shi ba dan ta san waye shi ba ita dai gurin boya da cuto kawai take nema. Ganin ya rumtse ido ya ya cige baki ya saka Ummi ta nufo inda yake da sauri ta banbare hannun Waira har da mai ciwon taja ta baya, a lokacin ne wani abu mai kamar ba suma ya ziyarce shi sai ya ji wani uban jiri da rawar jiki na neman kamashi ya bude ido zuciyarsa har gargada take numfashinsa na sarkewa. Waira sai kuche kushen ta subuce a hannun Ummi take ta sake rikeshi ganin take kamar maza sun fi mata yi mata kirki da kyautata. Tasss ya wanke mata fuska da mugun mari har sai da ta ji wata kara a kunnenta ganinta yayi batan wucin gadi, kwatankwacin tsayin da yayi a dazun da ta rumgume shi irinsa ta yi jini ya cika bakinta idonta ya cika da hawaye ya sauko mata...
AMEER POV.
10:24pm O'clock
Abincin ya masa dadi fiye da na kullum har cikin kwakwalwa kansa yake jin yadda abincin yake kai masa. Ba karyar Step Mother dinsa ta iya girki musamman na yau da ya zama na dabam.
“Da alama dai yau gaba daya zaka cinye jalof”
Ameer ya tsayar da cin abincin da yake yayi murmushi tare da daukar cup din ruwa ya sha.
“Sis don't fake it ke ma fa kin ji dadin abincin nan”
Sister ta yi murmushi tana cigaba da cin abincin. Wayar dake kam teburin ya dauka ya shiga Instagram dinsa ya the first thing da ya fara dubawa shi ne account din Nimra, sai kuma yayi sa'a ta amsa masa bukatarsa ta son following dinta.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.