Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 87 of 227

“Bismillah....”

Ta masu ishara da hanyar part din Abiey.

“Na dauka wata alaka ce mai karfi a tsakaninku”

Suna tafiya ta fadi haka sai ya kalli yanayinta ta da ya canja ta kasa sake fuska har lokacin. Murmushi yayi ya juya ya kalli kofar part din Ummi inda Waira ta shiga ya sake juyo suka cigaba da tafiyar.

“Wata kila kina nufin alakar jini, amman a gurina alakar da zaciya zata samu samu kwanciyar hankali idan ta san wanda take tausayi yana cikin koshin lafiya ita ma wata alaka ce mai karfi, da kin san yadda na damu da aka dauko yarinyar aka ce za a zo da ita Abuja, da kin taiyani murnar ganinta da na yi a gidanku, ko ba komai na san zata samu kwanciyar hankali da tsoro a nan”

“Haka ne ina taya ka murna Congratulations Sulem”

Ta fada tana dariyar yake, a badini bakar naganar ce ta yi masa, sai dai shi kuma be fahimta ba domin be fashinci komai ba. Iyakar kokarin da ta yi na danne abun da take ji a zuciyarta ne ta kula da shi yadda ya kamata sai dai duk wani dauki da murnar da take na zuwansa ya ragu a ranta.

Kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki haka Waira ta shigo falon da kofarsa take bude tun a fitar da ta yi da gudu bata tsaya rufe kofar ba, maida kofar ta yi ta rufe sai ta tsaya jikin kofar tana taba hannunta ganin fuskar Maleek a hade.

“Ba ki da hankali? Ta yi bako ya zo gurinta kije kina ruining abun da ta shirya, ji yadda kika fita da gudu kafafuwa tsil tsil kamar tsuntsuwa, ku a garinku ba ku da tarbiyar girmama bako ne? Haka ake tarbon bako?”

Yana mata fada tana turo baki daman tuni hawaye ya cika idonta domin bata so rabuwa da Sulem dinta ba, gashi kuma yanzu ya tsare ta da fada. Takawa ta fara yi ta bi ta gabansa zata sai ya daka mata tsawa.

“Ba magana nake miki ba shi ne zaki wuce”

Zabura ta yi ta hawayen dake makalle a idonta ya sauko saman kyakkyawan kumatunta, hakan kuma ba karamin kyau ya kara mata ba, dana da kwarjinin da har kuka kyau yake mata idan tana yi.

“Sulem ne ai”

“Ba Sulem ba sule, ina kika sanshi?”

Ta kai hannu ta rika sarkar wuyanta ta soma magana muryarta na karkarwa irin wanda kuka ke daf da subucewa.

“Ya bani wannan ya saka min”

“Miya faru?”

Mahmood dake saukowa stairs ya tambaya ganin hawaye na sauko mata wasu na bin wasu.

“Wallahi yarinyar nan bata da hankali yau na gani, wanda zai auri Namra ne ya zo sai kawai ta tafi ta rumgumeshi baka ga yadda Namra ta bata rai ba, idan ba hauka ba ina aka taba haka”

“Toh ai Sulem dina ne”

Ta fada tana kuka. Mahmood ta sauko gaba daya ta tsaya inda take.

“Wane Sulem”

“Sulem”

Ta nuna masa sarkar wuyanta.

“Oh na gane kai ta san shi fa, idan bata san shi ba ai ba zata je haka nan ta rumgume shi ba, ka gane Sulem din da take yawan magana, aiko ni ma zan so ganinsa ko dan na ji inda suka san juna tun da bata fada mana ba, waya sani ma ko ďan'uwanta ne”

“You miss the point ko yaya ne be kamatadaga ganin mutum an gayyato shi kije ki rumgume shi ba, wannan ai rashin tarbiya ne da sanin ciwon kai, she's so annoying sai ta rika yin abu kamar wata yar jaririya”

Mahmood ya zauna.

“Maybe daukin ganinsa take kuma ita ai ba musulma ba ce wata kila al'adarsu haka ake tarbon mutum”

Tsaki yayi ya nufi hanyar fita daga falon, Mahmood ya bishi da kallo baki saki, sai a yanzu shi ma yake mamakin sbun da Maleek yayi kamar ba shi ba, da can babu ruwansa da duk wani abun da ya shafi Waira, wata kila saboda kanennsa ba su taba rumgumar wani a gaban idonsa balle ace ya tsawata musu ita kuma ya ga ta yi dole yayi mata fada. Maleek be duba yiyuwar akwai alaka tsakaninsu ba, shi dai abun da idonsa ya gane masa ne be masa dadi ba, domin be ga dalilin rumgume mijin da kanwarsa zata aura Da Waira ta yi ba, yanayin yadda ya ga fuskar yar'uwarsa ta sauya baya tarin farincikin data wuce ta gabansa ta fita da shi ya sosa masa rai, wata kila yana taya yar'uwarsa kishi ne, ko kuma yana ganin rashin dacewar hakan da gaske. Bayan fitar Maleek Mahmood ya kalli Waira yayi murmushi

“Karki damu, haka yake takurawa kowa a gidan nan kin san halinsa ai ko?”

Ta daga kai.

“Ina son na tafi gurin Sulem”

“Yanzu ki bar shi ya huta tukuna, idan ya huta zamu tafi gaba daya har Ummi mu gaisa da shi sai ki sake ganinsa, yanzu zauna ki ba ni labarin i da kika san shi”

Ta zauna a kasa sai dai ta kasa labarta komai, sai tabin sarkar wuyanta take idan ta dago ta kalleshi sai ta yi murmushi kamar ba ita ce hawaye ya gama yi mata zuba ba.

“Toh shiga ki fadawa Ummi kin ga Sulem tun da ba zaki ba ni labari ba”

Ta mike tsaye da sauri daman abun da take nema kenan, da gudu ta hau stairs din kamar zata zame ta fado ta tura kofar dakin Ummi ta shiga sai ta samu bata cikin dakin, fitowa ta yi ta nufi dakin Nimra ta tura idan bata samu Ummi ba ai zata iya labarta Nimra sai dai tararda da ita da ta yi tana kuka ya saka jikinta yayi sanyi sai ta juyo ta fito ba tare da tace mata komai ba. Dakinta ta nufa tana shiga ta sami Ummi da Dr Zainab a dakin zaune Ummi tana hawaye.  Take kwarin guiwar data shigo da shi ya mutu sai ta tsaya jikin kofar tana kallon Ummi.

“Waira kin san shi ne?”

Ummi ta tambaya cikin karfin hali domin bata manta dazun data fita daga dakinta tana fadin Sulem ba. Wannan ne karo na farko da Waira bata damu da tambayar ko son jin dalilin Ummi na kuka ba, ta karasa cikin zumudi ta fara fada mata abun da zata iya tunawa a game da Shuraim. Sannan ta nufi gurin data aje tsofin kayanta na fata na ainahin garinsu ta bude ta dauko takardar da yayi mata rubutu a jiki ta nunawa Ummi.

“Ya ba ni wannan da babaken mutane za su kawo ni Habuja”

Ummi ta karbi takardar ta bude.

‘Ban san iya inda tafiya zata dauki be, ban san iya inda kaddara zata tsaya da ke ba, ban san yaushe Allah zai sake gadamu ba, a duk inda zaki karance ina fatar guri ne mai aminci da natsuwa. Ya kai wanda zai ci karo da wannan sakon ka ji tsoron Allah karka cutar da ita, fruits ne abun da ta fi ci, kuma ta tsoro da rashin sabo da mutane da wuri, Allah ya tsare ki

Dr Shuraim...’

Ya rubuta daga karshe, Ummi ta mikawa Dr Zainab takardar ita ma ta karanta sannan Waira ta karba ta nade a hannunta ta tashi tsaye ta fito dakin, so take ta je ta nunawa Sulem bata jefar da takardar da ya bata ba, tana nufo Stairs ta fara saukowa dai ga Maleek ya fara haurowa sai ta juya da sauri ta koma. Mahmood dake zaune yana hangen abun da ke faruwa ya saka dariya yanayin yadda ta juya ta koma din da sauri ya nuna tsoron Maleek take. Bata shiga dakinta da Ummi take ciki ba sai ta shige bedroom din Ummi da babu kowa a ciki a zatonta Maleek zai yi magana da Ummi ne ko kuma dakinsa zai tafi. Tsayawa ta yi a dakin tana sauraren idan ya wuce sai ta fito, shi kuma hango Ummi da yayi a dakin Waira kasancewar kofar a bude take, sai yayi reverse ya dawo baya. Kamin ya tura kofar dakin Ummi sai Waira ta bude masa a zatonta ya wuce ita kuma ta fito, ita da shi duk suna rike da kofar ne, ita zata bude ta fita shi kuma zai tura ya shiga. Sakin kofar ta yi ta matsa baya shi kuma ya samu damar shigowa ya rufe kofar. Ba saboda ita ya shigo ba amman hakan be yana shi yi mata ishara data zauna da ido ba. Ta nufi gefen gadon Ummi ta zauna a kasa tana kallonsa da idanuwanta da ya fi tsana a yanzu domin haushi take ba shi, ta boye takardar hannunta a bayanta ta matse gadonta ta natsu sosai irin natsuwar nan ta tsoro. Yau wardrobe din Ummi ya nufa ya bude ya fara dubawa a hankali domin ita kadai ce be bincika na a kwana uku da ya kwashe yana bincikar ďakin a duk lokacin da ya samu sa'a Ummi bata ciki, yadda yake bin komai a sannu yana maida shi mazauninsa a yadda ya taba shi sai ka rantse da Allah criminal ne da ya kware a sata. Ita dai Waira kallonsa kawai take kamin ta mike tsaye ta nufi inda zomonta ya leko ta dauke abunta ta rike. A hankali ya rufe wardrobe din sannan ya juyo ya kalleta tana shafa zomon tana kallonsa. Ya bude dayan side din ya fara dubawa daga samna gaba daya akwati ne da Ummi ta saka a gurin. Hankali kwance ya bude akwatin yana saka yadda zai fadawa Ummi cewar Waira ce ta ce ya duba mata tufafinta a gurin, tufafi ne sabin da ba a dinka ba a ciki lace da atamfa kasan kayan kuma wata karamar jaka ce irin ta saka takaradu, sai da ya cire kayan sannan ya dauko jakar dake lake da karamin makulli, aje jakar yayi ya maida akwatin da ya rufe sannan ya rufe wardrobe din yana ta mamakin me ke ciki fatansa dai ace abun da yake nema ne, domin ya duba gun da Ummi ke aje takardunta be samu komai a gurin ba. Sai da ya gama ya dauki jakar ya nufi kofa sai kuma ya juyo ya kalli Waira.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.