Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 96 of 227
“Waira”
Ya kira sunanta da tattausan lafazi, ta juyo tana kallonsa sai ta fashe da kuka.
“Toh me na ce miki kuma na kuka?”
“Ka ce Waira”
Ta fada tana kuka hawaye na mata zuba kamar bata san zafinsu ba. Hannu ya mika ya ciro tissue a motar Abiey ya mika mata bata tare da ya ce komai ba, sai ta saka hannu ta karba ta share hawayen, sannan ta juya ta koma gurin da ake mata lessons dinta. Sai a sannan ya bude mota ya sauko ya shiga cikin gidan. A kujerarta ta zauna tana share hawayenta har lokacin. Dattijon dake mata darasin ya ce.
“Kin tafi ki gani ko Ummi ce?”
“Ta daga kai”
“Ummi tana can asibiti gurin Nimra”
“Me ya same ta?”
Ta tambaya cike da son sani, domin ita dai tun da Maleek yayi mata tsawa dazun saboda tafiyar su Shuraim sai ta boya a kitchen tana kuka duk abun da ya faru bata sani ba.
“Saboda rabata da aka yi da wanda take so”
“Amman miyasa Ummi ba zata bari ta aureshi ba”
“Baki san Ummi ta haife shi?”
“Na sani”
“Na gani ai”
“Ta ina?”
Sai ta yi shiru bata son ta fada masa yadda aka yi ta sani saboda kar ya mata fahimta dabam, domin ta lura nan ba kamar garinsu ba ne da suke girmama tsafi. Dariya yayi ya matso kusa da ita
“A addininsu idan mace da namiji suka sha Nono daya ba a aure, ko da kuwa uwar su daban daban”
“Amman miyasa addininsu yake da zafi? Kai ma ai addininsu kake yi”
Ta tambaya domin ita dai bata ga illar haka ba, saboda sun sha nono daya ace ba za ayi musu aure ba bayan ba uwa daya ta haife su ba. Ya daga mata kai yana murmushi.
“Addininmu daya mana, amman ina fatar ba zaki jefar da na ki addinin ba ki dauki na mu, kuma ki daina kuka har idonki ya kumbura haka”
Kallonsa take kamar mai tunani ko mai son gano wani abu. Ganin hakan ya saka shiikewa tsaye ya isa gurin blackboard din suke rubuta ya cigaba da yi mata darasi.
AMEER POV.
Sai da suka yi nisa sosai sannan ya rage gudun da yake ya kalli Humaira dake gafen motar tana kukan da babu hawaye.
“Sai ki fada min gudun me nake wai?”
“Toh ba kamani za su yi ba, yarinyar nan na ganta a fito da ita da alama ma mutuwa ta yi, ai na san ina tsayawa za su kamani kashina ya bushe, Ameer ka ci amanar yarinyar nan kuma nima ka ci amanata, yanzu sun rike fuskata ko a wani gurin suka gan ni za su gane ni”
“Amman ke kin raina wayon mutane saboda wannan kika saka na taka mota ina da gudu kamar mun yi sata? Fitar min a mota Malama”
“Wallahi ba zan fita ba sai ka kai ni gidanmu, kuma ba zan yafe maka halin da ka jefa ni ba, kai dai haduwa da kai masifa ne babu alheri sam”
“Kuma rabuwa da ni bala'i ba, ina wayar?”
“Tana can na saki mana har da takardar na bar su a can, ni ba ta raina nake ba, Kuma Wallahi yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali kila ma ta mutu, ni ba ruwana da alakarku amman yanzu ka dauke ni ka saka ni cikin masifa, gashi iyayena talakawa babu ruwansu ka ja min matsala”
“Me aka ce ya samu yarinyar?”
“Ni ina zan sani wai, kaddara ce kawai ta hada ni da kai, gashi ka zame min kaya, Allah kadai ya san iya abun da ka yi ma wannan yarinyar ita ba, bakin mugu”
Ya taka turki yayo slow down ya faka ya fita ya zafaya ya bude gambun motarta.
“Fita, ba zaki zauna min a mota kuma ki zage ni ba”
“Ba zan fita nan ba Wallahi ban san abun da zai sake samuna ba, Ameer ka sakawa kanka imani ta tausayi haba, sai ka rika treating mutane kamar su basa da zuciya da jini kamar kai”
Wannan karon hawaye ne ya zubo mata.
“Ina kallo kana rubutawa mata cewar fake love kake mata fa, haka ake yi kwanan baya a gabana ka saka iyayenta kuka kuma ka saka tana zuwa nan kana taba ta ashe ma kai ba da gaske kake sonta ba, ina ta mata hannunka mai sanda ta gane amman bata gane ba”
“Gaskiya na fada mata ai, miye laifina a haka?”
“Bayan ka gama cutar da ita, ni Wallahi da ace mahaifiyarka ce sai na maka dan banzan duka, kuma sai na kai kararka gurin police na nuna min wukar da ka yi”
“Ko yanzu ai zaki iya marar kunyar yarinya”
“Marar kunyar yara dai”
Ta rama tare da kai hannu ta jango gambun motar ta rufe ta bar shi nan tsaye. Shi har mamakin yadda ta iya rashin kunya kuma take iya tsayawa ta fada masa magana son ranta yake. Zagaya ya shiga side din direba yaja motar har suka isa inda yake kyautata zaton unguwarsu ce domin ya ganta a gurin sau biyu kuma ta jadada masa a lokacin da ta kai shi cikin gidansu. Ya faka be ce mata komai ba ita ma bata ce masa ba. Bude motar ta yi ta fita sai da ta yi nisa sannan ta juyo cikin daga murya ta ce.
“Allah ya isa, mugun kawai, bakin mugu”
Gudun kar ya biyota da mota ya saka ta cire talkamimta ta ranta a ana kare. Ta gishin gaban motar yake kallonta har ta shige kwanar sannan ya ja motar ya juya kanta yana fadin.
“Wannan ta fi tunanina, idonta a tsaye suke bata tsoron kowa”
Yaja motarsa ya fice daga unguwar, sai dai har ya isa gida tunanin halin da Nimra take ciki yake, babu abun da yayi masa dadi kamar rashin tarar da mahaifinsa a gidan da yayi saboda ya san zai masa maganar wukar da aka ce ya dauka dazun. Tunani kala kala ne a ransa na yadda zai yi ya san halin da Nimra take ciki, sai yayi kamar ya kira number data kira shi da ita sai ya ji ba zai iya ba domin ba san wayar a hannun waye take ba. Cam dabara ta fado masa ya kira abokinsa Abdull, Abdull na dauka ya gabatar masa da bukatar ta son sanin inda Nimra take.
“Ni ban ma san abun da ke faruwa ba ai”
“Na dauka ko Maleek din ne yake dubata ai”
“I don't think so kasan Maleek baya duba mata ai, ko da kuwa yan gidansu ne”
“Dan Allah bincika min lafiyarta da inda aka kwantar da ita yanzu please”
“Hope dai ba wani abun zaka yi ba”
“Wai Abdull kun mai da dan ta'addane ko minene?”
Abdull yayi dariya ya kashe wayar. Ameer ya jefar da wayar saman gadonsa ya cire rigarsa ya wandon ba tare da tunanin ko gudun kar wani ya shigo dakin nasa ba ya nufi bandakin haihuwar uwarshi ya shiga ya sakarwa kansa shower ya rufe ido ya bude hannayensa ruwan na tsasa shi. Sai da ya ji ya gamsu da hakan sannan yayi wanka ya fito ya dauki tawul a dress room ya daura. In less then 20min ya shirya cikin korean trouser da farar T-shirt ya saka snipers masu kyau da tsada sannan ya nufi wayarsa ya dauka ya duba sakon da Abdull ya turo masa na asibitin da aka kwantar da Nimra.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.