Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 182 of 227

Ta amsa masa.

“Littafin da Ameer ya ce a baki, akwai addu'o'in safe da maraice a ciki, idan kina yi tsafinsu ba zai yi tasiri akanki ba, kuma ba Ameer ya ce kar mu barki ki tafi ke kadai zamu shiga cikin garin mu bawa Sarkin hakuri sannan mu fito”

Tana kokarin bude baki ta fada ma Maleek abu ne da ba zai taba yiyuwa ba, Eid ya nufo inda suke yana mata magana da yarensu yana nuna Maleek har wani cika yake kamar zaki, Maleek ya tsorata da ganin Eid not because of be yi addu'a ba no sai dai tsoro wani abu ne da Allah yake sakawa a zuciyar bayinsa, and yayi arba da abun da be saba gani ba, wato ganin mutane a cikin shigar da ba irin tasa ba, ga kuma wanda ya nufo inda suke yana magana da yaren da ba zai iya jin komai ba.

“Ki fada masa shi ko tawagar da suke tare da ita, ba zai taba shiga cikin garinmu ba, rikon da suka yi miki mun gode za su iya komawa daga nan, addini da al'adar da suka ara miki kika zo mana da ita, ki ba abar su su koma da ita, tufafi da duk wani abub da kika san ba na garin nan ba ne karki shiga da shi”

“Zan fada mata, daman tun can na fada masa ba za su iya shiga cikin garin ba, amman addini da tufafi wani abu ne na dabam da ya shafi rayuwata babu ruwanka da wannan”

Ta bashi amsa da yaren. Ya kara takowa ya kai hannu ya taba fuskarta yana mata magana a hankali da yarensu.

“Ikke tek tek far der tik Waira”
_aki watsar da komai waira_

“Ban da addinin nan, karka takura sai a aje Eid ba zan iya ba, na gamsu da wani abun da baka taba ji ba da na tabbatar da a yanzu kai ma ka aje wannan addinin ka dauki wanda na zo da shi”

Ya kama hannayenta ya rike.

“Baki san iya lokacin da ya dauke ni ina bauta ina azabtuwa saboda neman Sarki ya yafe miki ba Waira, ba na kisan da ake zargin kin yi ba na guduwar da kika yi, wannan kisan ni na aikata kuma na fadawa Sarki haka, amman dauko wani addini ki shigo da shi wannan abu ne da ni kaina ba zan yarda da shi ba balle kuma sarki da jama'ar gari, bayan kuma kin sa abun da yake jiranki, shiyasa na yi ta nanata miki cewar karki jefar da addininki karki dauki addinin wasu”

“Ta yaya yaushe”

Ya kai hannunsa ya bugi goshinta da karfi har sai da Police din suka matso da zimmar rike su Maleek kuma ya kai hannu da sauri ya buge hannunta. Sai ga jini yana fita ta hancinta kamar rufe ido a bude haka ta tuna a wacan ranar da Ummi ta fada mata Malaminta yana son ganinta duk wani abun da ya faru a ranar a take a gurin ta tuna shi. Eid ya fisge hanunsa ya yarfar yana watsawa Maleek wani mugun kallo ya kalli Police din dake cikin uniform da kuma masu sanye da kayan gida, shi dai wanda yayi jagorancin zuwa garin yana can labe gurin mota yaki ma fitowa dan kar a ganshi.

“Kar wanda ya taba ni a cikinku, rakiya kuka yi kun kawo ta mun gode zaku iya tafiyarku”

Da mugun mamaki suke kallonsa jin yayi musu magana da hausa, bayan kuma tun zuwansu gurin da yare yake magana da Nuwaira.

“Ina malamin da yake koya min karatu Eid?”

“Ni nake koya miki karatu ba shi ba, tun a ranar da aka daukeshi yake na fanshe shi, zomon da kika baro a can ni ne na baki ba shi ba, shiyasa ban taba bari kin taba ni ba, domin na san zaki iya ganewa, babu wani Malami Waira sai ni na yi siffar wannan mutumen ne saboda na samu shiga, ina bibiyarki da duk wani hali da kike ciki zan iya yin komai shiyasa na kashe tun ranar farko da aka kawo shi na yi siffarsa, a duk tsawon lokacin babu kalar azabar da ba gani ba Waira saboda ke”

Ya juya mata bayansa ta yi arba da tambunan dake bayan farar fatarsa, sai ta dauke ido hawaye na sauko mata ta kalli Maleek da yaren hausa ta ce.

“Ya Maleek za ku iya tafiya ni kun kawo ni gida na gode”

“Me yake fada? Ba zamu tafi mu barki a nan ba, gashi tun yanzu ya fara tsorata ya fitar miki da jini a hanci, dole mu shiga ciki mu yi magana da Sarkin”

“Zancen shiga cikin garin ba zai taba tabbatuwa ba, saboda haka mu yi hakuri mu yi bankwana a nan”

“Idan ba za su yarda mu shiga duka ba, to ni zan shiga, ba zan barki ki tafi ke kadai ba, Ameer ma ya roki na yi masa haka ni kaina hankali ba zai kwanta ba sai na tabbatar kina cikin koshin lafiya”

“Babu abun da zai same ta, a can inda ta tafi wani abun be same ta ba balle a garinsu? Ina tare da ita babu wani damuwa zaku iya tafiya, shiga a cikin garin nan kamar kiran mutuwa ne idan kuma kin shirya sai ku shiga mu gani”

Eid ya fada musu da yaren da za su fi fahimta, wato yaren Hausa. Police din suka fara kallon juna, Maleek ya mika hannunsa for the first time ya rike hannun Nuwaira.

“Idan ka ga na saki hannunta, to na yi magana da Sarkinku ne kuma na tabbatar zata rayu cikin aminci ne”

Eid ya nuna Maleek da tsaya kamar zai tsokane masa ido.
[8/9, 8:10 PM] My S Line: 74

“Ki fada masa ya cire kansa daga lamarinki in ba haka ba zai yi nadama”

Maleek yake nunawa amman da Nuwaira yake magana da yaren garinsu.

“Ba zaka cutar da shi ba Eid kai dan'uwa ne a gurina, mai matukar son abun da nake kauna, mai son abun da nake so, mai gudun bacin raina da kukana? Meya same ka ka canja? Kalamanka da kamanin da nake gani a fuskarka ba su ne na Eid da na tafi na bari ba, wannan mutumen shi da iyayensa tarbe ni, sun saka hannu biyu sun rumgume ni, ba dan sun san daga inda na fito ba sai dan karamci da sanin ya kamata irin na su, sun nuna min kauna, a gurinsu na san abun da ake kira da tsabta da kauna da soyayya, a gurinsu na san me iyali yake nufi, a lokacin da zuwa gida ya kama ni, suka sako ni a mota suka rokoni har kofar garinmu akan me kake tunanin idan ka nuna masa tsaya zan ji dadi? A wane hali zan bari ka cutar da shi? Da wace Hujja zaka zabe ni ka bar shi?”

Eid ya dauke hannunsa yana kallon Nuwaira dake magana taba zubar da hawaye. Ta sauke kanta kasa ta kalli hannun Maleek dake rike da nata, sannan ta kalleshi.

“A nan garinmu ne Ya Maleek zan rayu cikin aminci da yardar Ubangijin Kaaba”

“Hakan ba zai gamsar da ni ba Nuwaira, sai na ga halin da zaki kasance kuma sai na yi magana da Sarkinku”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.