Complete Hausa Novels

Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 61 of 227

“Are you okay ko kina jin wani ciwon ne?”

“Aa bana jin komai lafiyata kalau”

Ya sauke ajiyar zuciya domin ciwonta ne abun da ya fi damunsa a yanzu.

“Ummi har yanzu baki fada min yaushe ciwon nan ya sake ki ba, kuma me likitoci suka ce akai?”

Ta dubeshi.

“Ba nace wannan sirrinmu ba ne?”

“Ban fadawa kowa ba”

“Amman ka so ka yi maganar a gaban Namra ai, bana son kowa ya sani”

“Na ji, amman kina zuwa asibiti?”

“Na dade ban tafi ba, shakara biyu kenan da na gane cutar tana tare da ni”

“Amman Ummi kina shan magani? Kin san illar wannan cutar kuwa? Har kike cewa baki son kowa ya sani? Kin san abun da take janyowa”

“Likita ya min bayani, kuma yanzu zan duka da shan magani. Ina Waira?”

“Sun bata gado hoton ma daker ta yarda aka yi mata sai ihu take yarinyar bata da hankali”

Ummi ta mike tsaye tana tunanin mafarkin da ta yi wanda yayi kamanceceniya da abun da Waira ta yi a lokacin da ta so shiga dakin Maleek, suna tafiya Ummi ta juyo ta kalleshi.

“Kar dai ace aljana ta auri dan'uwanka Mahmood”

Mahmood ya girgiza kai.

“Haba Ummi wane irin aljana kuma? Yadda Maleek ya tsani mata har wata aljana ta samu damar aurensa?”

“Maybe ita ta saka mishi tsanar matan ai, wani mafarki na yi da ya ba ni tsoro...”

Jerawa suka yi suna tafiya tana labarta masa yadda ta yi mafarkin.

“Mafarki ba gaskiya ba ne, kawai dai dan kin saka abun a ranki ne ya saka kike yi mafarki, Ummi damuwata yanzu ciwonki ne yaushe zaki ga likitan? Kuma wane likitan ne yake dubaki, ba a wasa da ciwon nan”

“Sai na gama da matsalar Waira”

“And Ummi miye reason dinki na boye wannan sirrin ciwo ne fa”

“Bana son na tashi hankalin Babanku, kuma bana son hankalin Nimra da Namra ya tashi har da kai, dan dai Maleek na san ko ya rasa ni ba zai yi bakinciki ba”

Ta karasa a lokacin da Mahmood ya kai hannu ya tura kofar dakin da Waira take ciki.

“Maleek yana sonki Ummi, kawai dai wannan ciwon ne na kyamar mata ya saka shi nesantarki amman abun na masa ciwo, ya fada min haka kuma yace baya iya ayyana rayuwarsa idan babu ke, addu'a kawai ya kamata mu yi masa komai zai wuce”

“Kuma dole mu tashi masa tsaye, domin mafarkin nan da na yi jikina na bani kamar gaskiya ne in ba haka ba miyasa na ga Waira a mafarki har tana fadar wai kasheta za'ayi ban san ko suwa za su kashe ta ba”

Ummi ta zauna bakin gadon tana kallon fuskar Waira dake bachi.

“Akwai abun da yarinyar nan ta gani dazun tun da har gashi ta nuna”

Mahmood yayi shiru saboda baya son musawa Ummi. Ba shi kadai ba Abiey ma da ta labarta masa mafarkin a waya ta fada masa abun da ya faru be yarda ba.

“Mafarki ba gaskiya ba ne, kowa da yadda Allah yake halittarsa ku mata komai sai ku rika cewa aljannu ne, mun bincika abun nan a likitance an fada mana cewar halittace da Allah yake halittarsa kowa da irinsa”

Ta sauke ajiyar zuciya daman ta san ba lallai ne ya yarda ba.

“Hiayatee ki kwantar da hankalinki dan Allah komai zai wuce”

“Haka zamu saka masa ido ba tare da komai ba? Kullum sai dai ka ce min komai zai wuce when?”

Ta fashe masa da kuka kasancewar dakin babu kowa sai ita kadai da Waira dake bachi har lokacin, Mahmood tuni ya fice daga asibitin zuwa gurin aikinsa.

“Bari ki dawo sai mu zauna mu yi maganar abun da ya kamata, zamu saka ayi addu'a kuma muma zamu dage da yi har da sadaka idan ta kama har gurin dakin Allah sai aje ayi masa addu'a shikenan?”

“Eh amman da kullum baka yarda da zancena sai ka rika cewa komai zai wuce”

Daga can cikin wayar yayi dariyar manya, wadanda ke nishadi da matansu ya san halin sahibarsa tun kurciya na dawainiya da ita har zuwa yanzu da girma ya kama.

“Haba Madam yanzu ai na zubar da makaman yaki na ce za'ayi duk abun da kike so, kina asibitin har yanzu?”

“Eh ina son na tafi gida yanzu sai Hanne ta zo ta zauna da ita”

“Ya jikin nata? Likita ya fadi wani abu?”

“Sun duba komai a game da jinin idonta ba su ba mu sakamakon ba har yanzu, amman cizon dake hannunta sun ce da sauri tana da kyau jini, kuma likitan da ya duba da farko ya iya aiki shiyasa abun ya zo da sauki, sai dai yace duk da haka za su bata gado ta zauna har sai ta samu sauki gaba daya”

“Toh Allah ya biyaki, ita kuma ya bayyana mana iyayenta kuma ya shirya mana na mu yayan, ya nuna mana aurensu da yayansu a tare”

“Ameen... Abiey Ameen... Allah ya amsa....”

Ta amsa tana jin wani iri a zuciyarta, gani take kamar ba zata ga lokacin ba.

“Amman dan Allah ki saka ido akan yaran nan, bana son a samu wata matsala kuma ke ma ki kula min da kanki yawam tunani da damuwa ki ciresu kin fi kowa sanin yadda nake son farincikinki”

“Allah ya ba ni iko”

“Ameen, to sai na dawo?”

“A dawo lafiya Habibi”

“Allah ya sa”

Ya aje wayar, ita ma ta sauke wayar idonta na cika da kwalla, number Maleek ta lalubo ta danna kira ta saka hands-free. Ringing ďaya ya daga kamar yana jiran kiranta.

“Hello Ummi...”

Ya fada muryarsa har rawa take, sai da ta rumtse ido ta bude sanin uwa bata fushi da ďanta ta amsa masa.

“Na'am”

“I'm sorry ki yi hakuri da abun da ya faru bana nufin bata miki rai, ban san mi ya zo kaina ba kawai na samu kaina da bacin rai ne marar misaltuwa”

“Ba komai kana gida?”

“Aa na fita”

Ta yi shiru tana saurarensa sannan ta ce.

“Maleek ina son na tambaye ka, akwai mafarkin da kake ko kana ganin wani abun?”

Ta san it's not the right place ta yi masa tambayar, sai dai bata da zabin da ya wuce haka saboda baya zama da ita idan kuma ya dawo gida ba zai amsa mata tambayar ba.

“Ban fahimta ba”

“Baka mafarkin komai?”

“Ina mafarki kamar yadda kowa yake idan ya kwanta”

“Okay idan ka dawo za ku yi magana da Abiey”

“Okay amman kin hakura Ummi?”

“Ya zan yi Maleek uwa ai bata fushi da ƴaƴana na yi hakuri tun kana karami har ka girma, mi zai haka na ki hakuri akan abun da ka yi min? Ni dai ina son ka dage da azkar na safe da yamma, kuma idan zaka kwanta ma ka yi addu'a sannan ka roki Allah ya yaye maka wannan abun saboda yana damuna, bana son na mutu ban ga ka warke daga wannan damuwar ba Maleek, ciwon zai min yawa, idan zaka kwanta ka rika alwala kuma ka yi addu'a, sannan ka tsare karatun Qur'ane fiye da yadda kake yi, sannan ka rika daurewa ko da baka so kana zauna cikin kanenka da ni dan Allah duk abun da kake ji ka daure ka yaye abun a ranka idan ka ji abun ya taso maka ka nemi tsarin Allah”

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.