Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 135 of 227
“Lemme drop her home”
Fadar sai sauke ta a gida, abun mamaki ne a gurin Mummy da kuma Mahaifinsa Daddy ya san da be son ganinta ba zai sauketa gida ba, ba ma zai zauna a falon ba, sai dai Daddy be san manufarsa ta yin haka ba, hakan ya saka shi mikewa tsaye tare da kai hannu ya dafa kafadarsa.
“Karka fada mata magana marar dadi please”
Cikin wata siga mai kamar rada ya fada masa haka, Ameer ya girgiza kai.
“Ba abun da kake tunani ba ne”
Yana bashi amsa ya wuce yayi gaba, Ummi ta dauki jakarta zuciyarta na raya mata maybe Ameer zai yi amfani da wannan damar ne ya fada mata karta sake zuwa gidan duba shi. Mummy ta rakota har gurin motar ta tuko kanta, hakan ya saka Ameer barin jikin motarsa ya iso gurinta ya mika mata hannunsa.
“Key”
Ta ciro key a jakarta ta mika masa, ya nufi motar ya bude mata backseat, ta ji kamar ya karramata yayi mata alfarma a cikin daruruwan mutane.
“Hajiya na gode sai anjima”
“Toh Allah ya kiyaye hanya, ni ma zan shigo wani lokacin In Shaa Allah”
“Allah ya nufa”
Ummi ta fada sannan ta nufi motar ta shiga, Ameer ya rufe motar ya zagaya ya shiga mazaunin direba yayi ma motar key. Yana tukin Ummi na hawaye ko da ace ba a cikin dadin rai Ameer zai tukata ya kaita gida ba, ita abun farinciki ne a gurinta.
“Karki sake zuwa duba ni, idan kina son ganina ki min waya zan zo”
Ya fada yana tukin a hankali.
“Ba lallai idan na ce ina son ganinka ka zo ba”
“Saboda me?”
“Saboda ban kyautata maka ba, a lokacin da kake bukatata, na san kana kallona da wannan abun a kullum”
Yayi shiru na tsawon lokaci kamin ya sake fadar.
“Me yasa to kika yi?”
Hannu ta saka ta share hawayen idonta.
“A lokacin ina tsoron rasa rayuwar mahaifinka ne, saboda likitoci sun tabbatar min, idan ba a yi masa aikin ba, zai iya mutuwa, mun siyar da gidan gadonmu da kayan dakin Yayata Maryam mun hada duk be wadatarwa na bi yan'uwana da abokan mahaifina, kowa be taimaka min ba, ina cikin wannan halin ne Dr Hamid ya kawo min mafitar cewar akwai wacce take son siyen ciki, idona a rufe na aminta aka siyar, sai bayan da aka yi aikin mahaifinka sai kuma rayuwa ta yi bankwana, babu yadda ban yi ba saboda na gudu da cikinka amman ban samu dama ba, saboda ina da talaka ba ni da ikon komai, a cikin yarjejeniyar da aka yi da Hajiya Jamila ance idan har na karya alkawari zan biya kudi mai yawa, kuma ba ni da su...”
Ta yi shiru saboda hawaye dake mata zuba suna son su ci karfinta su zame mata kuka.
“Su waye yan'uwa mahaifina? Ban san su ba”
“Idan kana son sani, zan fada maka su, zan tafi da kai har Kano ka gansu”
“Sun san abun da kika aikata?”
“aa ba su sani ba, duniya tana kallon ďan da na haifa da Deen a matsayin mataccen”
Hawaye sun saukowa Ameer, sai ya kara rage gudun motar ya faka gefen titi ya jinginar da kansa jikin kujera.
“I'm sorry, na san baka kaunata na san a gareka ban cika uwa ba, na san ba zan taba kima a idonka ba, amman please don't leave me, i want you here with me, na san ba abu ne mai sauki ba, kuma ban cancanci ko wace kalar alfarma a gareka ba”
“Idan kina bukatata a kusa da ke, you can make a room for me, sai na dawo gidanki na zauna, i need to know who you are, me kike so miye baki so, ya rayuwarki take. It tear me up when you turn me down, ina son na ji ɗumin uwa how it's? To get to know you”
Yana fada yana kuka kamar karamin yaro. Ta girgiza kai.
“I don't want to force you”
Bude motar yayi ya fita ya rufe ya dawo back ya bude ita dai binsa kawai take da ido har ya shigo.
“You didn't force me, ni nake neman wannan alfarmar, ni dai kawai ina bukatar uwa ne, ko da wata uwarce ba ke ba zata tsaya a gabana tace ita ta haife ni, zan karbeta you leave a empty place here in my heart, i want you to fix it, that's little boy you left is still inside me, and he need a mother, i want to make a motherhood memory now”
Kuka yake Ummi ma kukan take jikinta na rawa tana son ta taba shi ta kasa, wannan karon ba tsoro ne ya rufe ba kunya ce irin na uwar data kasa bawa ďanta kulawa har sai da ya bukata. Ya saka rigarsa ya share hawayensa sannan ya fita daga back seat din ya rufe mata motar, jinginawa yayi motar ya na dan lokaci kana ya bude ya shiga ya cigaba da tuki, a gabansa dazun wata ke tsoron rasa nata iyalin shi kuma kari ma ya samu dan haka ba zai iya barin wannan damar ta wuce ba, ko dan ciwon da Waira ta fada masa Ummi tana yi. Kalaman da ya furta mata a yanzu sun yi effecting dinta, ji take kamar wani dafi ya saukar mata a jiki, kalmominta sun tsare jikinsa she couldn't hold her tears har suka isa gidan. Ya faka motar harabar ya ciro tissue da ya gani ya mika mata.
“I'm sorry please stop crying, a yanzu bana son kowa ya zubar da hawaye a kaina, ni ma ban kyauta miki ba ni ne silar mutuwar yarki Nimra wacce kanwa ce a gurina”
“No Nono daya kuka sha, she and her sister they are my step-daughters, kuma ba kai ne sila ba kawai Allah ya kawo ne, karka haka a ranka, idan ma laifi ne ni ce mai laifi ni ce silar komai”
Ta karba ta share hawayenta sannan ta bude gefenta ta fita, shi ma fita yayi ya jingina da motar yana kallonta.
“Waira tana ciki?”
“Kana son ka ganta ne?”
“I always wanted to see her, zata raka ni na dauko wasu abubuwan ne a gida, kamin mu dawo make sure my room is clean”
Ummi ta kara dubansa da kyau.
“Da gaske kake Ameer?”
“I need you by my side, ya zan yi?”
Hannu ta saka ta dafe kirjinta idonta ya sake cika da hawaye.
“Thank you so much for this opportunity, na gode da ka zabi zama da ni, thank you for everything Ameer Allah ya maka albarka, Waira zata zo yanzu. Thank you”
Ta furta sannan ta nufi hanyar falon tana jin wani kukan da bata san na minene ba ya sakota gaba, farincikin Ameer zai zauna da ita ne? Ko kuma na kuskuren da ta aikata a baya ne? Ko kuma na rayuwar da take tunanin ba za'a bata aro ta dade tare da ďanta ba ne? Barin jikin motar yayi yana fara zagaya harabar gidan yana kallon yadda tsarin gidan yake. Ba laifi su ma sun zubar da dukiya a ginin gidan kamar yadda aka zubar a gina na su, domin komai yayi tsarin ginin kadan ya banbanta da na Daddynsa. Yana tsaye Waira ta nufo inda yake da gudu tana murna, doguwar rigar material ce sanye a jikinta sai bakin talkami da karamar safa da ta rufe kafafuwanta kanta babu dankwali gashin kanta ya kwanta da kyau kana gani ka san ya sha gyara, sai kamshi take zubawa irin na manyan larabawa.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.