Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 40 of 227
“Fita fita fita”
Dan sanda ya fita waje, sannan ta yi shiru ta kara kankameshi, tana wani numfashi kamar zata shide, jikinta rawa yake ta ko'ina tana daga kai sama kamar ta ga abun tsoro. Dr Shuraim be yarda yayi motsi ba har sai da ta samu natsuwa sannan ya dagota jikinsa ya kama hannunta mai ciwo a hankali ya duba, sai ta yi saurin fisge hannun ta boye bayanta, sai dai bata yarda ta sake rigarsa da dayan hannunta da yake lafiya ba, gaba daya a firgice take wata rayuwa take gani da bata mafarkin yi ba, ga wasu mutane da bata san inda suka fito ba, komai ganinsa take kamar mafarki. Tausayinta sai ya kama shi sosai domin yadda hawaye ke mata zuba abun tausayi ne sosai ga wanda ya san zafin hawaye. Zaunawa yayi saman gadon sai ta zauna daf da shi kamar zata shige a jikinsa ta saki rigarsa ta kama hannunsa ta rike, shi kadai ne mutumen da take jin zata iya aminta dashi, ko ba komai shi ya bata irin abun da take iya ci kuma yayi kokarin fahimtarta har ta sake jiki da shi.
“Dr Tafiya za'ayi da ita”
Dayan police din da ya iso ya fada yana leko gurin.
“Yanzu?”
“Eh daga can office aka ce mu taho da ita za a wuce da ita Abuja ne?”
“Gurin me? Yarinyar da bata da lafiya?”
“Sun ce za a kula da ita a ne a can za su sama mata wani Asibitin, kamin a gano inda yan'uwanta suke, baban yarinyar da aka tsince ta a motar ne zai rika kamin a gano danginta”
Shiru yayi be ce komai ba, domin shi ma ya san yadda kasar take cikin domin yana cikinta, baya son ya shiga hurumin sa ba nashi ba, ba dan haka ba zai tambaya ya ji ko an hukunta wanda aka kama motar tata. But a yanzu ba shi ne babbar damuwarsa ba, damuwarsa ina za a kai wannan yarinyar? Da gaske rika ta din za'ayi ko kuma so ake a yi mata wani abu a rufe case din? Idan ma da gaske ne abu ne mai wahala ta yarda da bisu idan ta bisu kamin ta saba abu ne mai wahala domin ya lura da yanayinta tana da wuyar sabo. A take ya ji tausayinta ya cika masa zuciya sai dai babu yadda zai yi ya hana faruwar hakan domin ba huruminsa ba ne.
“Okay zamu shiryar takardar transfer, wace asibitin za a kaita a Abuja?”
“Ba mu da masaniya akan wannan”
“Ya kamata ku sani, saboda kar a cutar da yarinyar nan, ina ganin huruminku ne”
“Eh zamu sani ai dole, for now dai ba mu sani ba saboda case din a hannun manyan mu yake, su za su kula da komai”
Daga haka be sake cewa komai ba, har aka dauko masa tarkadun da komai suka miko masa yayi rubutu a kai sannan ya mikawa police din file dinta ya mike tsaye, tana ganin haka sai ta mike tsaye, a karon farko ta lura da fankar dake lake a sama tana bada iska, tun da take a rayuwarta bata taba sanin wani abu makamancin wannan ba sai yau, kallon fankar take sosai tana mamakin minene a gurin. Bata ankaro ba ta ji an taba hannunta dubawar da zata yi sai ta yi arba da masu bakaken kayan nan na jiya suna kokarin bata da mutumen da take jin kamar ta dade tare da shi. Wani irin kara ta saka tana fisgar hannunta tana son ta kubuce daga rikon da suka yi mata amman ina karfi ba daya ba, ko a babba balle ita da take matashiya, da karfin tsiya suka rabata da Dr da zuciyarsa ke masa ba dadi shi ma jin yake kamar ya dade tare da ita, musamman da be san inda za a kaita ba, Allah kadai ya san abun da za'ayi mata wata kila cutar da ita za ayi be sani ba. Fashewa ta yi da wani irin kuka ta fara fisge fisge police din ya dauke ta sama sai ta miko hannu tana son riko Dr Shuraim daya fito waje ward din yana kallonta zuciyarsa na masa ba dadi, hannu kawai take miko masa alamar ya rikota tana girgiza kai tana kuka sosai kamin ta kai bakinta ta gantsawa Police din cizo ba shiri ya sake ta sai ta rugo a guje ta gurin Dr Shuraim ta rumgumeshi da karfi tana kuka, dayan police din ne ya zo zai rikata sai Dr ya dakatar da shi.
“Kyaleta”
Hannu ta kai ta bugu Dr Shuraim da mugun karfi da kafa bakinta a kirjinsa ta cijeshi tana dukan kirjin nasa, so take ta ce miyasa zai bari a tafi da ita amman bata da bakin fadin haka domin bata jin yaren da suke fahimta kamar yadda su ma basa iya fahimtar yarenta. Sai dai kwarewa irin ta masu basira da hikima sai ya fahimcin haushinsa take ji, hannu ya saka yana rarrashinta.
“Yi hakuri ya isa”
Shiru ta yi kamar ba ita ce ta bude baki tana ihu ba, sai ta yi tsit ta kwantar da kanta a jikinsa kamar mage ta rufe ido gam, mutane suka yi cincirodo sai kallon ikon Allah suke, daga ma'aikan Asibitin har wandan ake jinya da masu jinyar, wadanda ba sun da zamanta ba a gurin ba ma sai da suka sani, har yan wani Ward din sai da suka zo kallonta.
“Dr ka samu mata”
Wani likitan ya fada yana zolayarsa, Dr yayi murmushi be ce komai ba, ya kalli police din ya ce
“Bari na dauko kayana sai mu tafi da ita a can”
“Hakan zai fi kam, domin abu ne mai wahala ta yardar ta bisu”
Shi ne abun da kowa ke fada, Dr ya daga kansa ya samu daker da cire hannunsa daga rikon da ta yi masa, sai ta kara kankanme jikinsa. Tana jin ya fara tafiya sai ta taka ita ma amman bata yarda ta bude idon ba, takawa take tana jin kamar tana taka ruwa saboda sanyin tile din bata taba tafiya a kansa ba, daker ya samu ya fita daga gurin, Office dinsa kam sai wani ne yaje ya dauko masa kayansa ya kawo masa, tana ta jin hayaniya mutane yayi yawa ta san sun fito guri mai mutane da yawa, a hankali ta bude idon ta kalli yadda gurin yake wasu na kallonsu wasu kuma na da hada hadarsu, dagowa ta yi ta kalleshi sai yayi mata murmushi sai ta sake rufe idon, sai da ya isa gurin motarsa ya bude sannan ta sake bude idon sokoko ta yi tana kallon motar at first bata ji tsoro ba sai mamaki tana kallon motocin da ba daya ba, ta kai hannu zata taba wani motar dake kusa da ta Dr yayi ma motarsa key karar da ta yi ya saka ta zabura ta dauke hannunta da sauri tana tasa motar a firgice, take hankalinta ya tashi ganin haka ya saka Dr ya ce.
“Mota zamu shiga”
Sunan mota ta fara rikewa, domin shi ta taba ji a bakin Eid.
‘Outarrr’
Ta maimaita sunan a ranta tana tuna yadda yake fada mata cewar wasu mutanen na dabam a wata duniyar suna hawanta su yi tafiya, bata taba sanin haka motar take ba sai yau, Dr ya kai hannu ya bude motar yayi mata alama da ta shiga da hannu, a take ta lake masa kafada alamar bata zata hau, he never thought da gaske take har sai da yayi unkurin sakata da karfi sai ta sake shi ta ruga zata fita daga gurin sai kuma ta rasa gurin waye zata tafi mutanen dake gurin sun mata wani iri da bata saba da su ba, ga gurin ababen hawan sun yi yawa ba mota kadai ba har da babur. Gudu take tana neman gurin boya ta rasa gurin wa zata tafi mutane sai kallonta ake kuka take sosai tana waige waige ta gudu nan ta dawo nan haka take har ta samu gurin wata fulawa ta boya ta nade guri daya kamar macijiya ga hannunta sai zafi yake mata zuciyarta na bugawa da mugun karfi kamar zata fado.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.