Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Wani Gari Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 66 of 227
“Yaya dai Jabir ko dai taku ta zo daya?”
“Da wa? Ai ba zaki yarda ba”
“Saboda me? Indai ruwan zai maka wanka ai sai dai mu nama maka na dauraya”
“Hmmm -Nhmmm Nimra kenan ke zaki yarda ki barwa wata ni?”
Ta saka dariya domin ta san halinsa da barkwanci musamman idan baya son abu yanzu ne zai juye ya mayar akan wani.
“Ni na mashinshini na kai ne baka da kowa, shiyasa nake maka kamu ka samu wannan yarinyar ta taimaka maka”
Ya girgiza kai yana cije baki.
“Ko waye mashinshinin nan na ki ki fada masa you're taken kuma ina da kishi bana son wani na rabar iyalina”
Dariya ta saka gudun kar Maleek dake zaune can gefe ya gwatsaleta ya saka ta juya ta koma falon tana gyara dankalin kanta. Shi kuma ya sake juyowa ya fuskanci Waira.
“Fada min ina iyayenki suke?”
“Waira zata fada, amman ba wayo ka yi ba”
Fada masa take zata fada masa, amman ba dan yayi mata wayo ba, shi kuma sam be gane salon karin halshen nata ba, shiyasa be yi kokarin cewa komai ba har ta cinye biscuits din dake kan plate din gaba daya ta kalleshi idonta na cika da hawaye ta ce.
“Waira bata da yaya, bata da Baba, bata da Mama amman tana da Eid”
“Waye Eid?”
“Dan'uwanta ne, yana sonta, Eid yana mata komai amman yanzu be neme ta ba, Waira ba zata koma garinsu ba, idan ta koma Sarki zai kasheta”
Mamaki ya kama Jabir.
“Saboda me? Me kika aikata? Wani kika kashe”
Sai ta girgiza kai hawaye na sauko mata.
“Bata kashe kowa ba, amman Sarki yace idan Waira ta gudu ba zata iya dawowa ba, kuma wani ya mutu saboda ita, za a kasheta”
“Miyasa kika gudu? Baki da yan'uwa a can? Ke baiwa ce ko kuma me?”
Ta girgiza kai hawaye na sauko mata kamar ba gobe.
“Waira bata san kowa ba, ita kadai take zaune tana da....”
So take tace bera da zakara kuma ba zata iya fadar hakan da hausa ba, ta suna sunan da aka fada mata na zaka da bera.
“Waira tana da Hens, Waira tana da Rat, Waira Waira zata mutu kusa Sarki ba zai kyale ba, zai kasheta”
Ta girgiza hancinta na zubar da majina kamar yadda idonta ke zubar da ruwan hawaye.
“Waira bata son ta mutu, Waira tana son ta ga Eid Waira bata son ta koma, ba zata gane hanya ba”
Da gaske take fada domin tana yawan tuna mutanen garin da rayuwar da take a garin amman ko kadan ta kasa tuna sunan garin ma balle kuma ta san hanyar da zata bi ta tafi, ita dai ta san ta rayu a wata duniyar kamin ta samu kanta a nan, kusan kullum sai ta kwanta da tunanin Eid da berayen da suke rage mata kewa. Ta kalli Jabir tana kuka sosai.
“Waira bata son ta mutu, Waira tana son Eid, Eid ba zai zo ba, Sulem ba zai zo ba... Waira tana Son Sulem....”
Ya matso kusa da ita ta jingina kanta jikinsa yana jin tausayinta na kama shi. Har suka ci suka sude Maleek be dago ya kalleta ba tun bayan kallon da yayi mata da farko, sai dai kunnuwansa suna sauraren komai take fada and one by one ya fahimci ko wace kalma dake fita bakinta.
“Waira bata son makaranta, suna mata dariya idan ta yi magana, Waira bata da kawa a makaranta”
Kusan duk wani abu dake cinta a rai sai da ta fadawa Jabir, the way da yan makaranta suke tsokanarta yana mata ciwo sosai, idan aka tambayeta ta kasa bada amsa ko kuma ta yi bayani ba a yadda suke yi ba, suna mata dariya ita kuma tana jin zafin haka, idan an tashi cin abinci bata da abokin zama ta ci abinci, she's not that child da za a ce tana tsoron mutane domin ba small girl ba ce, but yanayin rayuwarta ya saka tana shakkar kusantar mutane, ga yanayin mu'amalarta da shigarta ya ya banbanta da na sauran yan makaranta domin bata son taka talkami har yanzu, tana isa makaranta sai take cirewa ta rike a hannu, ta inda Allah ta taimake ta rashin rufe kai ba ita kadai ce bata yi ba, domin akwai yara da yawa a makaranta da basa rufe kansu wasu ma ristoci ne wasu kuma musulmai ne da suka ari rayuwar turawa suka yafa.
Ko baya ga wannan ma ita dai gani take an cilasta mata na cewa dole sai ta koyi rubutu da karatu, abun da bata iya ba tun farko, sai dai hakan ya taimaki rayuwarta domin tana jin yaren hausa da English a yanzu, sai idan an yi mata mai sarkakiya ne kawai ba zata gane ba. Rike hannunta ďaya a ciki ďayan.
“Waira tana son Ummi.. Tana son Nimra.. Waira tana Son Mahmood... ”
Ya nuna kansa.
“Waira tana son Jabir?”
Ta dago ta kalleshi idonta har sun sauya kala saboda kuka. Sai ta girgiza masa kai alamar aa.
“To Waira tana son Maleek?”
Nan ma ta girgiza kai.
“Waira tana Son Namra? Da Abiey?”
Ta girgiza kai a karo na uku cewar bata son su.
“Mun shiga uku har da Mai Gidan gaba daya? To shi mi yayi?”
Bata son Abiey da ďansa Maleek saboda basa sakar mata fuska yadda Ummi da Nimra suke, kuma basa janta a jiki yadda ya kamata, Jabir kuma yau ta fara ganinshi taya zata san halinshi har tace tana son shi. Maleek ya mike tsaye ba tare da ya dauke plate din da ya ci abinci ba ya fice daga gurin ya koma cikin falo. Ita kuma sai ta saka gefen rigarta ta share fuskarta, Jabir ya yamutsa fuska alamar kazanta.
“Noooo bari na dauko miki tissue”
Ya tashi shi ma ya bi sahun dan'uwansa Maleek, sai ita ma ta tashi ta nufi hanyar Garden tana tunani kala kala, a cikin abubuwan da take tunanin babu mao mata ciwo kamar rashi ganin Eid tana son ta sake saka shi a idonta kamin ta mutu, domin ta san mutuwarta zata iya zuwa mata a ko wane lokaci, Sarki be taba alkawari ya saba ba, kuma ba zai fasa akanta ba.
Abun ka da gwani, daga shiga dauko tissue Jabir ya shantake da bawa Ummi labarin abun da Waira ta fada masa, da kuma fahimtar manufarta da yayi. Tausayinta da kaunarta sai ta karu a zuciyar Ummi.
“Shiyasa bata da sakewa yarinyar nan kullum tana zaune kusa da ni, komai ake hira ba zata saka baki ba, shekararta ďaya a gidan nan amman taki ta sake jiki da kowa, wata kila shiyasa ta ki ta fada mana inda garinsu yake saboda bata son a maida ta garin, Allah kadai ya san abun da ta yi going through”
“Tace bata son Abiey da Maleek amman tana son da Nimra da Mahmood”
Ummi ta yi murmushi tare da mikewa tsaye tare da mika hannu ta karbi tissue dake hannun Jabir.
“Ba ni tissue”
Jabir ya mika mata ta zara ta share hawayenta daman abu kadan yana saka ta kuka a yanzu saboda zuciyarta a raunace take. Jabir har ya mike tsaye zai bita sai mahaifiyarshi sai dakatar da shi.
“Yanzu kuma ai sai ka ba ta damar magana da ita tun da ka yi mai yuyuwar, sanadinka ta fadi abun da ta boye kar kaje yanzu zata ce ka tona mata asiri wata kila yardar da kai ta yi shiyasa ta fada maka”
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.